Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!
Fitattun 'yan fim guda biyu, Husaina Ibrahim Gombe (Tsigai) da Shu'aibu Mohammed (Danwanzan), sun rasu a ranar Lahadi, 8 ga Afrilu, a wani mummunan hatsarin mota. Su na dawowa ne daga Legas, inda aka gayyace su su ka yi wasan gala, sun shigo mota Toyota Hiace mai zuwa Kano. Sun kusa Kaduna (kilomita 22) sai direban ya yi zaton kila akwai 'yan fashi da makami a can gaban su, su na tare mutane masu shiga Kaduna a daidai lokacin. Wajen karfe 4:30 na asuba ne. Sai direban ya yi u-turn ya koma daya hannun hanyar (mai zuwa Abuja daga Kaduna). Ai kuwa ba a dade ba su ka yi taho-mu-gama da wata tirela wadda ta dauko shanu daga Maiduguri za ta kai Anacha.
Mutane 16 ne a bas din. A cikin su, 11 su ka mutu - mata 4, maza 6, da karamin yaro 1. Mutum 5 sun tsira. Direban bas din, wani Bakano, ya rasu. Amma direban tirelar bai samu ko kwarzane ba. Hasali ma dai a jiya lokacin da mu ka tuntubi 'yan sanda, ya na can cikin garin Kaduna ya na yawon sa abin sa.
An rufe Tsigai a Kaduna (a makabartar da aka rufe jaruma Balaraba Mohammed a Maris 2003). Shi kuma Danwanzan, an kai shi gida Kano aka rufe shi a can.
Tsigai ta na da 'ya'ya biyu (Anas da Nafisa), Danwanzan ya na da 'ya'ya 4. Maaifiyar Tsigai ta rasu, amma baban ta ya na nan da ran sa a Gombe. Iyayen Danwanzan duk su na nan da ran su a Kano.
Tsigai da Danwanzan sun yi fice ne a bangaren wasannin kwaikwayo na ban-dariya, masu nuna rayuwar talakawa ko 'yan kauye. Tsigai ita ce matar Ibro (Rabilu Musa Danlasan) a wadannan wasannin. Hasali ma dai ita ce ta saka shi cikin wasan dirama, har ya zo ya zama shugaban kungiyar su ta dirama (Hamdala Drama Group). A wasannin, Tsigai ta kan fito a matar Ibro mafad'aciya, wadda ba ta gode dukkan abin da mijin ta ya ba ta, amma kuma daga karshe sai ta zo ta yi da-na-sani.
Lokacin da labarin rasuwar tasu ya bulla shekaranjiya waccan, ina Kano. Al'amarin ya girgiza mutane matuka, musamman 'yan fim da kuma masoyan wasannin Ibro. Na garzayo Kaduna don sake shirya mujallar Fim, wadda har za ta fito a ranar da aka yi rasuwar. Nan da nan aka sake buga wata sabuwa, aka saka mamatan biyu a bangon mujallar.
Allah ya jikan Tsigai da Danwanzan, amin.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Allah ya jikansu. Allah ya sa su hutu. Allah ya ba mu hakuri.
ReplyDeleteAllahu Akbar;
ReplyDeleteDaga Allah muka fito kuma gareshi za mu koma
Allah[SWT]Ya jikan Danwanzan da Tsigai Ya kuma yafe kurakuransu Amin
Allah Ya kyautatamu bayan tasu Amin summa amin
Daga Yunusa Abdullahhi
Allahu Akbar Allah yajiqansu yayi masu Rahama
ReplyDelete