Abin mamaki ba ya karewa. A yau da rana an zabe ni a matsayin Sakatare-Janar na Kungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kaduna (Kaduna State Film Producers Association). Jiya Abdullahi Maikano Usman ya aiko mani da 'text message' ya sanar da ni cewa za a yi zaben a Ma'aikatar Al'adun Gargajiya ta Jihar Kaduna a nan garin Kaduna, kuma ya ce ya kamata in je. Da ma ni memba ne a kungiyar (saboda finafinai na, wato 'Gagarabadau', 'Daren Farko,' 'Kash!' da kuma 'Artabu').
Da zuwa na, sai aka bukaci masu takarar zama Sakatare su janye. Ana ganin cewa babu wanda ya cancanci wannan mukami a wurin, sai ni! Ni kuma ga ni da tsoron a ba ni mukami a kungiyar, domin na san matsalolin harkar fim na Hausa sarai, musamman ma a Kaduna. Mutane da yawa su ka taru su ka ce lallai ne sai in fito takara. Hasali ma dai an rufe karbar 'yan takara tun tuni (kwanaki masu yawa) amma aka canza dokar saboda ni. To, ganin cewa mutane sun nuna mani goyon baya, sai na amince. Na ci zaben babu hamayya. Mutum 15 su ka zabe ni daga cikin mutum 15 da su ka jefa kuri'ar! Ba a yi wani 'PDP' ba a wurin.
Shugaban kungiyar a yanzu shi ne Yusuf Mohammed (mai 'Al-Yusuffas Film Production').
Na gode Allah da ya ba ni wannan dama ta yi wa masu shirya fim aiki a Jihar Kaduna. To amma akwai jan aiki a gaban mu. Harkar fim ta durkushe. Mutane masu kallon fim sun dawo daga rakiyar 'yan fim, su na ganin cewa duk finafinan shirme ake yi yanzu. Su kan su 'yan fim din, ba su damu da samo mafita ba; sai gaba su ke yi a tsakanin su.
Na dade ina kallon kai na a matsayin marubuci kuma dan jarida kawai, amma ba d'an fim ba duk da yake na shirya finafinai. To yanzu ni dan fim ne kenan? Bari za mu gani!
Ina so in ga cewa na kawo shawara ga 'yan kwamitin mu na shugabanni a kafa Hukumar Tace Finafinai a Jihar Kaduna (Kaduna State Film Censorship Board), irin ta Kano da Sakkwato. Za mu hada gwiwa da Gwamnatin Jihar Kaduna a karkashin sabon Gwamna, wato Alhaji Namadi Sambo, don ganin an kafa hukumar. Wannan zai taimaka wajen bunkasa harkar a nan jihar. Ba sai mutum ya je Kano ya yi kwana da kwanaki ba domin a tace masa fim. Ina ganin cewa idan har mu ka cimma wannan burin, to ai mun yi aiki ma.
Haka kuma ya dace mu tinkari batun yanayin finafinan, wato jigon su, da kyan aiki, da tsarin su, da sauran su dai. Akwai kuma batun dabi'ar 'yan fim, wadda mutanen gari ke kuka da ita, musamman idan an buga munanan labarai game da su a mujallun industiri. Shi ma kalubale ne babba.
A gani na, shugabannin da aka zaba masu kishin harkar ne, kuma 'ya'yan kungiyar su na girmama su. Idan mu ka yi amfani da wannan damar ta samun shugabanci, mu ka kama wasu daga cikin manyan matsalolin mu ka magance su, to alhamdu lillahi, kwalliya ta biya kudin sabulu.
Allah ya ba mu sa'a, amin.
No comments:
Post a Comment