Tuesday, 24 July 2007
Hira da Kamaruddeen Imam
Agajin Harkar Rubutu: Ya Kamata Gwamnati Ta Shigo Ciki - K'amaruddeen Imam
Daga Ibrahim Sheme
Kamaruddeen Imam yana daga cikin ’ya’yan kakan marubutan Hausa, wato marigayi Alhaji Dakta Abubakar Imam, marubucin littattafai kamar su ‘Ruwan Bagaja, Magana Jari Ce,’ Tafiya Mabud'in Ilmi,’ Tarihin Annabi Da Na Halifofi, Tambaya Goma Amsa Goma, da sauran su. Shi ma Alhaji K'amaruddeen marubuci ne, kuma mawallafi, kuma shi kad'ai ne daga cikin ’ya’yan Imam da ya gaji mahaifin sa a fannin adabi.
Kamar Baba Imam, shi ma Alhaji K'amaruddeen ya kwanta dama. Ya rasu a ranar Juma’a, 12 ga Mayu 2006 a gidan Imam da ke Tudun Wada, Zariya, a Jihar Kaduna, bayan ya yi fama da rashin lafiya na tsawon shekara biyar. Shekarun sa 56 a duniya.
Ya rasu ya bar mahaifiyar sa da matar sa da ’ya’ya shida da kuma jikanyar sa. Allah ya jik'an sa, amin summa amin.
Abin ikon Allah, na samu damar yin hira da K'amaruddeen a Zariya tun yana da rai, wato a ranar 29 ga Agusta 2004. Mun tattauna a kaset lokacin da na halarci wani taro da iyalan Imam suka kira don k'addamar da kwamitin Gidauniyar Tunawa da Alhaji Abubakar Imam (Abubakar Imam Foundation) tare da gina gidan yana a intanet. Ni memba ne a kwamitin. Mun yi tarurruka da dama don d'abbaka wannan muhimmin nufi, wanda a k'arshe an kafa cibiyar tattara bayanai kan Imam a wani gini da ke duban K'ofar Babban Dodo a birnin Zariya, sa’annan an gina gidan yanar (www.abubakarimam.com).
Malam K'amaruddeen mutumin kirki ne, mai sauk'in kai, mai sanyin murya, mai fara’a – kamar dai dukkan ’ya’yan Imam da na gani. Lokacin da na buk'ace shi da mu tattauna, nan da nan ya amince, muka zauna muka tattauna kan sha’awar sa ta rubuce-rubuce, da matsalolin sha’anin wallafa a Nijeriya da kuma halin da ake ciki.
Na so in wallafa hirar a jaridar Leadership lokacin ina editan ta, amma sai abubuwa suka rincab'e; haka lokacin da na ke babban editan jaridar Public Agenda, na so buga hirar, amma nan ma abubuwa suka giggitta. Sai a yanzu ne Allah ya ba ni damar wallafa wannan tattaunawar da marubucin.
Wannan hira tana da muhimmanci, domin kuwa ita ce ta farko da Malam K'amaruddeen ya yi da wani d'an jarida a kan rubuce-rubucen sa, kuma ita ce ta k'arshe.
Bismillan ku:
SHEME: Zan so ka fad'i sunan ka da kuma dangantakar da ke tsakanin ka da marigayi Alhaji Abubakar Imam.
KAMARUDDEEN: To ni suna na K'amaruddeen Abubakar Imam, kuma ni d'an Alhaji Abubakar Imam ne.
SHEME: Yanzu aikin me ka ke yi?
KAMARUDDEEN: Yanzu ni marubuci ne kuma ina buga littattafai, kuma ana ba ni gyaran rubutu kamar na 'manuscript'.
SHEME: To ko za ka gaya mana yawan littattafan da ka rubuta da kuma sunan su?
KAMARUDDEEN: Na rubuta littattafai da dama. Akwai "Tsaka Mai Wuya," "Hannun Ka Mai Sanda," sannan kuma na rubuta "Halaye Nagari a Cikin Musulunci," "Sir Usman Nagogo" – amma da Turanci ne ni da (D'ahiru) Coommassie muka rubuta shi – da kuma "To Use Knowledge."
SHEME: Kamar daga wane lokaci ne ka fara rubuce-rubucen nan?
KAMARUDDEEN: Na fara wannan rubuce-rubuce tun lokacin da marigayi Baba Imam yake da rai, har ma ya sa ni a kan wasu hanyoyi inda ya ke ce mani, “In za ka rubuta tarihin mutum, to rubuta abin kirkin da ya yi na alheri ga jama’a, maimakon ka yi yabon shi.”
SHEME: Yanzu kenan kai kad'ai ne cikin ’ya’yan marigayi ka gaji baban ka ta wajen rubuce-rubuce?
KAMARUDDEEN: I to, haka ne, don har yanzu ni kad'ai ke yin irin wad'annan ayyuka na rubuce-rubuce.
SHEME: A da, ka d'an rubuta littattafai na k'irk'ira, amma kuma daga baya sai ka bari. Ko me ya kawo haka?
KAMARUDDEEN: To dalilin dai shi ne saboda rashin kud'i, kuma in ka rubuta ka kai ma wasu su taimake ka sai su ce ba su da kud'i, ko kuma su ce kai ka kawo rabi, in ka kawo ma in ba a yi sa’a ba sai ka ga kud'in ka ma ya mak'ale.
SHEME: To ban da matsalar rashin kud'i, ko za ka iya fad'in wata matsala da ke iya shafar aikin wallafa, musamman a nan Arewa?
KAMARUDDEEN: Akwai matsaloli mana. Misali irin yadda mutane ke rubuta littattafai barkatai ba tare da an tsara shi yadda ya kamata ba, musamman masu soyayya. Ba wanda bai iya soyayya ba, to amma ya kamata in za ka rubuta ka tabbatar da ka rubuta abin da yake mai kyau kuma mai inganci.
SHEME: Menene maganin abin?
KAMARUDDEEN: Maganin abin shi ne gwamnati ta shigo ciki, ta zo ta rik'a sayen littattafan. Ya kamata kuma a rik'a sayar ma makarantun sakandare. Ta haka za a samu tarbiyya a makarantu, ba wai mutum ya je ya kalli fim ya zo ya maida shi littafi ba, ko kuma irin yadda ake cusa ma matasa ra’ayin soyayya ba; misali, duk wanda ya karanta Magana Jari Ce ya san lallai wannan Bahaushe ne ke magana, kuma ba batsa, sannan ga tarbiyya a ciki.
SHEME: To Alhaji, ga shi Allah ya had'a mu a nan Zariya don tunawa da shi marigayi da k'addamar da kwamitin tunawa da shi. Ko za ka gaya mana abin da ya sa ku ke son a kafa wannan kwamiti?
KAMARUDDEEN: To, akwai wani d'an jarida wanda ake kira Ibrahim Sheme, yana yawan rubutu a kan Dakta Abubakar Imam. A gaskiya ya nuna mana k'auna, ya nuna yana son marigayi Dakta Abubakar Imam. To kwanan nan sai ya yi wani rubutu wanda ya zama mana kamar tuni ko k'aluballe, don kuwa har wani shagub'e ya yi mana inda ya nuna mana cewa ’ya’yan marigayin kamar ma sun manta da shi. To jin haka sai mu ma muka harzuk'a muka fara shirin kafa wannan kwamiti don tunawa da marigayi Dakta Alhaji Abubakar Imam.
SHEME: Ya ka ke ganin wannan abin zai amfani mutane a nan gaba?
KAMARUDDEEN: In aka kafa wannan Foundation, to kowa da kowa zai zo ya zauna ya duba duk abin da ya ke buk'ata na Dakta Alhaji Abubakar Imam, kuma wannan ya had'a kowa da kowa. Misali, akwai wata mata, mutuniyar Jamus ce, take bincike a kan Dakta Abubakar Imam, yanzu haka har ma ta yi nisa ta kai wata matsaya babba. Ka ga yanzu in ta zo sai kawai mu nuna mata wannan wurin don kuwa da man an tab'a yi mata bayanin ana wannan aiki.
SHEME: To a k'arshe, ko za ka iya ba ni d'an tarihin rayuwar ka?
KAMARUDDEEN: To ni shekaru na 54 da haihuwa, kuma a nan Zariya aka haife ni. Bayan na gama karance-karance na na sakandire da jami’a, na yi aiki da jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo, lokacin Edita Baban Zarah.
SHEME: Ai ina zaton kai a Katsina ka ke.
KAMARUDDEEN: Asali na shi ne Katsina, kuma muna da yawa, misali su Shamsuddeeni Imam, Nuruddeen Imam, su suke can Katsina; amma mu da aka haifa a nan Zariya - Najmuddeen Imam, K'amaruddeen Imam, Amadi Imam, Jalaladdeen Imam – nan Zariya muke.
SHEME: To Alhaji, na gode.
KAMARUDDEEN: Ni ma na gode. Allah ya saka maka da alheri, amin.
(BAYANI: Hoton Kamaruddeen da ke wannan shafin ya dade da dauka, watakila sama da shekara 20 kafin rasuwar marigayin, domin ya zama dattijo lokacin rasuwar sa)
Malam SHEME Allah ya saka maka da alkhari don wannan mahimmin tarihi. Amin. Shi kuma marigayi KAMARUDDEEN Allah ya jikan sa. Amin
ReplyDeleteFatan Alkhairi
ReplyDelete