Sunday, 12 August 2007

Hiyana - Tsiraici a fagen shirin fim

Wata zazzafar muhawara ta barke a kasar Hausa tun daga makon jiya. Wani guntun hoton bidiyo na minti takwas mai nuna tsiraicin wasu matasa biyu ya bayyana a makon da ya wuce. Mutanen biyu dai mace da namiji ne, kuma macen ba wata ba ce illa wata 'yar fim mai suna Maryam Usman, jarumar shirin 'Hiyana'. Ana yi mata lakabi da 'Maryam Hiyana'.

Kasancewar ta 'yar fim ya sa mutane da dama su na cewa lallai yanzu ta tabbata cewa 'yan fim 'yan iska ne. Na kalli "video clip" din da ido na, kuma na kad'u matuka da na gan shi, musamman da yake dukkan su Musulmi ne. An nuno yarinyar tsirara a ciki. Wani saurayin ta wai shi Bobo, wanda ke sana'ar canjin kudi a Legas, ya dauke ta hotunan bidiyo din da kyamarar wayar sa ta selula har na tsawon sama da minti takwas. An nuno ta kwance a kan gado, haihuwar uwar ta, daga nan kuma shi ma ta dauke shi da kyamarar - shi ma zigidir, alkalamin sa a mike; daga nan kuma shu'umin ya hau kan yarinyar, ya yi lalata da ita a lokacin da yake ci gaba da daukar hotunan bidiyo din. Har sai da ya kawo (a gafarce ni!), kuma ya yi wasa da maniyyin sa a kan cinyar ta.

A cikin "clip" din, Bobo da yarinyar su na magana, kuma ana ji radau.

Yanzu mutane cewa su ke yi wai an yi "bulu fim." To amma a gani na, za a iya cewa an yi "fim" ba a yi "fim" ba. Abin da ya sa na ce haka shi ne, wadannan matasa biyu ba su dauki wannan iskanci da nufin shirya fim ba. Shi fim, ai ya na da matakai da dalilai na shirya shi, da ma'aikata da sauran su, kuma a karshe manufar sa a kai kasuwa a sayar. Har ma sai an yi tallar sa a kafafen watsa labarai kafin a kai shi kasuwa. Su kuwa wannan yarinya da wannan mutum sun yi wannan abu ne domin shi mutumin ya rika kallo bayan sun rabu.

A lura, sun dauki wannan abu ne a cikin 2006, amma sai yanzu ya fito duniya ta sani. Can a kwanan baya Yakubu Lere, mawallafin mujallar Gidauniya, ya buga labari mai nuna cewa wata yarinya ta yi "bulu fim," har abin ya harzuka 'yan fim, su ka dakatar da sayar da mujallar a shagunan sayar da finafinai a Kano.

Akwai bayani na daban kan yadda wannan bidiyon tsiraicin ya fita daga hannun su har ya shiga hannun jama'a, amma wannan wani labarin ne na daban.

Babu shakka abin da suka aikata abin Allah-wadai ne, musamman a daidai lokacin da mutuncin 'yan fim ya ke tangal-tangal din zubewa. Don haka babu dalilin kare su a nan. Sun yi ba daidai ba. Wannan shi ne bidiyo na farko mai nuna tsiraicin Hausawa da ya shiga hannun jama'a miliyoyi (kuma ba a san inda abin zai tsaya ba!).

Ba a yi "blue film" ba domin wannan ba fim ba ne, "clip" ne kawai aka yi domin "private viewing". Ita kan ta yarinyar, da farko ba ta san ja'irin daukar ta ya ke yi da kyamarar wayar sa ba har sai da ya gaya mata, kuma ta bayyana mamaki tare da cewa ya daina. Amma da yake ya ba ta ta dauke shi (kuma tsautsayi ba ya da rana!), sai ta kyale shi har ya yi lalata da ita ya na dauka.

A sakamakon wannan abu, mutuncin 'yan fim ya kara zubewa. A ranar Juma'a da ta wuce, malamai sun yi hudubobi a kan wannan al'amari, kuma sun yi tsinuwa. Haka kuma an ci gaba da yin Allah-wadai da al'amarin a wurare da dama. Kafafen yad'a labarai su na ta babatu a kai.

Yarinya dai ta gudu ta boye (an ce wani saurayin ta da ya ce shi ya ji ya gani zai aure ta, shi ne ya boye ta - wai ma za su yi aure kafin azumi).

Duk wani dan fim ya kad'u. Shugabannin 'yan fim hankalin su ya tashi matuka. A yau din nan sun ba da sanarwar dakatar da shahararrun 'yan wasa sama da goma (maza da mata) wadanda ake zargi da aikata munanan ayyuka iri-iri, ciki har da zina da shaye-shaye. Sun yi haka ne don ganin sun tsaftace harkar daga bata-gari da ke shigowa su na yin abin da su ka ga dama, kuma don gudun fushin Gwamnatin Jihar Kano, wadda ake ganin za ta iya daukar tsauraran matakai kan harkar fim din baki dayan ta.

Amma jama'a mu yi tunani: ba fa 'yan fim kadai ba ne 'yan iska. Mutumin da ya yi ummulhaba'isin wannan aika-aika, BA DAN FIM BA NE, kuma BAHAUSHE ne, magidanci, mai sana'a, miloniya, dan kasuwa. DON HAKA, al'umar Hausawa (Musulmi) baki dayan ta ce ta ke bukatar gyara. Kuma dukkan mu kowa ya dubi kan sa, ya gyara rayuwar sa, domin babu shakka a cikin masu yin kumfar baki kan wannan abu akwai masu aikata zububban da su ka fi wannan da ake babatu a kan sa.

Allah ya shirye mu baki daya, amin.

21 comments:

  1. TO JAMA AR MUSULMI KO INCE HAUSAWA WANNAN WANNAN KADDARORI NE DA KE IYA FARUWA GA KOWA NE MUSULMI DOMIN HAKA BA ABIN DA ZAMU STINE MUSU BANE SAI DAI MUYI ROKON ALLAH YA SHIRYE SU MUKUMA YA STARE MU DAGA GARBA ABUBAKAR JAHAR KEBBI

    ReplyDelete
  2. TO JAMAAR MUSULMI IDAN MUNDUBI MUMA MU DUBI ABUBUWAN DA MUKE YI SABODA HAKA KADDARA CE YAKAMATA KAWAI MU ROKI ALLAH YA SHIRYASU.KO KADAN KADA NUYI MASU MUGUNYAR ADDUA.YAKAN IYA FARUWA GAREKA.ALLAH YA SHIRYEMU AMIN

    ReplyDelete
  3. thatsridiculous very disappointing saboda haka we should take this as a lesson Allah sha shiryemu

    ReplyDelete
  4. assalamu alaikum,kungiyar musulmai ta arewacin nigeria shin Hiyana da Bobo sune kadai mazinata na farko a kasannan ko kuwa shin saboda su sanannune.saboda ALLAH ina manyan masu kudi a arewa masu gina manyan hotel inda kowa yasan me ake aikatawa a wanan wurare shin ina maraban jos,tafa,kwanan dan gora,zimbabwe,oke koto a legas da sauran makamantansu, shin wani mataki kungiyar musulunci suka dauka,ina yan luwadi,dan ALLAH rokona anan duk wani abu da za a yanke ayi saboda ALLAH.

    ReplyDelete
  5. assalamu alaikum,kungiyar musulmai ta arewacin nigeria shin Hiyana da Bobo sune kadai mazinata na farko a kasannan ko kuwa shin saboda su sanannune.saboda ALLAH ina manyan masu kudi a arewa masu gina manyan hotel inda kowa yasan me ake aikatawa a wanan wurare shin ina maraban jos,tafa,kwanan dan gora,zimbabwe,oke koto a legas da sauran makamantansu, shin wani mataki kungiyar musulunci suka dauka,ina yan luwadi,dan ALLAH rokona anan duk wani abu da za a yanke ayi saboda ALLAH.Ibraheem Jos.

    ReplyDelete
  6. alal hakika a baya anyi ta kokarin nuna musu hanya amma basu ji ba a koda yaushe suna ta kokarin gyara sana'arsu da yimata kwaskwarima to amma a sani ko hakkin kannenmu mata da kuka dauka kuke sasu dinki mai fidda al'aurarsu sai allah ya saka mana da sannu wanda yafi wannan ma zai fito. DAGA DANJUMA YAHAYA AZARE JIHAR BAUCHI.

    ReplyDelete
  7. A Hakikanin gaskiya abinda ya faru ga maryam hiyana ba abin farin cikineba kamar yadda wasu suka dauka kaddara ce kuma tana kan kowa mukanmu mudubi irin namu ayukka damuke aikatawa Allah kasa mugane amin
    Daga Sanusi fari jahar sokoto
    GSM 08069661227 Gidadawa area.

    ReplyDelete
  8. HAUSA FIM: TARBIYAR TSIRARA
    HAUSA FIM: TARBIYAR TSIRARA
    AUWAL MUHAMMAD ABDULKADIR
    aazarema@yahoo.com
    6/8/1428h-19/8/07m
    BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
    Sanannen abune cewa kasashe masu kaffa-kaffa da
    addinin su da al'adunsu na kwarai suna kokarin maida
    finafinai da wasan kwaikwayo wata kafa ta tattauna matsalar
    alumma da tarbiya da bada tunani na gari, sabanin halinda
    muke a kasar hausa na karkatar da wannan dama zuwa
    gwada kwarewa wajen nuna rashin kunya da da koyawa
    manyan gobe munanan dabi'u daga baya kuma sai ace ana
    kokarin gyara tarbiya to lallai bamu ba tarbiya har duniya ta
    tashi indai yan daba da mata masu cin gashin kansu da
    wadanda aka kasa tarbiyarsu suka gudu suka bar tarbiya su
    -ne masu tarbiya kai abun dariya da takaici duk da haka
    shuwagabanni da wadanda abun ya shafa basu yi yunkurin
    hanawa ko kokarin garkatar da akalar fina-finan izuwa koyar
    da tarbiyar gaskiya ba . to yanzu abun yakai ga dole kowa ya
    ciza yatsa , akwai matukar da takaici ace yar fim ta fito tsirara
    har na tsawon dakikai takwas kan gado sannan wani yazo ya
    haukanta yayi tsiyar da zaiyi da ita, sannan yayi wani irin
    nau'i na wasa da maniyinsa kan cinyarta , kai ! wallahi ,
    na'uzu billahi minashshaidanirrajim! wani irin dabbanci kenan?
    kuma abun mamaki harda cewa '' a gafarcemu'' amma
    wannan yarinya taci sunanta ''HIYANA'' don kuwa ta ha'inci
    duk musulmin duniya, ta kuma tona asirin musulmin najeriya.
    Duk wani mai zurfin tunani yasan hakan zata faru tunda
    kokari suke su kwaikwayi [nigerian film] su kuwa wannan ba
    bako bane gunsu, ga wani abunda na taba karantawa jaridar
    gaskiya tafi kwabo
    ''GTK: To, a matsayinki na wadda take fitowa a fina-finan
    Hausa da na Turanci, yaya za ki kwatanta bambancin da ke
    tsakanin fina-finanmu na Arewa da kuma na Kudanci?
    HAUWA MAINA: Ai dai wannan ne ko kuma aka tambaya, za
    ku iya fadin bambancin (dariya).
    GTK: Amma da yake ke kina cikin harkar ne, ina ganin ke ya
    fi cancanta ki yi mana bayani.
    HAUWA MAINA: To shi kenan, a gaskiya, �yan Kudu sun yi
    mana fintinkau in dai za a yi maganar gaskiya ce. Amma
    Alhamdulillahi mu ma mun fara shiga sahunsu, saboda idan
    aka yi la�akari da irin na�urorin da suke amfani da su, to,
    yanzu mu ma mun fara samun irin wa]dannan na�urorin. Haka
    kuma �yan wasanmu na Hausa su ma yanzu sun zaburo, suna
    kuma kokari sosai. Saboda haka nan ba da jimawa ba za mu
    rika hada kafada da kafada da su.''
    hakika abun daya ban mamaki cikin wannan al'amari babu
    kamar wasu masu kokarin wanketa da cewa ai ba fim din
    tsiraici bane, saboda wannan wani abu ne tsakaninta da
    saurayinta bai da alaka da fim, to amma ai ita jaruma ce a
    wannan harka ta tarbiya, wa ya sani ko ta sadaukar da kanta
    ne wajen gyara al'adun banza har ta fara yada tarbiya kyauta
    ana yada ta a blue tooth cikin kayan mutunci , domin ayi koyi
    da ita, sannan an sakar muku haka ne , shin wannan baya
    gwada cewa wata ran za'a yi hakan a tsare da furodusa da
    dukkan shikashikai da sharuddan fim.
    sannan wasu kuma sun bige da cewa taci mutuncin hausa-
    fulani ina ruwan wannan matsala da hausa fulani , wasu na
    cewa daman ba hausawa bane masu yi , hakika wannan
    karya ce mai girma da neman wanke kai na banza da wofi ,
    to kai in ma haka ne , waya basu izinin shigowa kano, jama'a
    kar mu rudi kammu, hausa fulani dai a duniya zamu bar shi
    ba wani abu mai anfani gun Allah sai musulunci.
    IYAYE : sune kashin bayan tarbiyar 'ya'ya kuma sune
    matakin da idan yaro ya rasa ko sukai sakaci dashi rayuwarsa
    zata shiga wani yanayi wanda bara aji dadin karshenta ba,
    wani yana cewa '' uwa makaranta ce idan ka shirya ta kamar
    ka shirya al'umma ne'' kuma kamar yadda kowa ya sani
    wadannan masu cin abinci da lalata tarbiyar manyan gobe
    galibinsu in bamu ce duka ba sun fuskanci matsala da iyaye
    kamar auren dole ko rashin mai riko mai kyau ko rashin tsawa
    da kwaba don haka dole iyaye su dau hakurin daukan kaso
    mai girma na laifi saboda kaso mai girman ba suke dashi
    wajen jibintan yayansu da kuma damar tarbiya.
    YAN WASA: saboda sune masu fuskantar da wannan
    matsala zuwa ga alumma kai tsaye don haka duk da barrantar
    da kan- su da wasu uzurori da suke bayarwa wanda zai yi
    wuya su kansu su yarda da su a cikin zukatansu balle
    al'umma gaba daya.
    Su dai kokarin su dole sai sun kwaikwayi turawa alhali kuwa
    kowa yana kokarin bada gudumawane daidai al'ummarsa,
    idan bature da baturiya sukai wani rashin kunya a wasan
    kwaikwayo to saiku duba cewa to shin kowa a cikin jama'arku
    ba rike ya ke da addini ba ? ba tare yake da mafadi ba? Shin
    burgewa a garemu shine mu fita daga shingen iyaye da
    sunan yanci? Wadannan banbance-banbance na addini da
    al'ada idan ba'a duba su ba to zamu jima cikin wannan rami,
    mu fito mun yi kura duk wanda ya kallemu ba zai iya
    maimaitawa ba.
    SHUGABANNI: wato duk Wanda yake da damar fada aji
    amma bai hango matsalar da zata iya jawowa masu
    zuwa ba, ko ya hango baiyi kokarin kawo sauyi ba .
    Daga karshe ina kara rokon wanda abun ya shafa da suyi
    hattara wajen daidaita wannan wasa inda zaiyi daidai da
    addinin jama'arsu da al'adunsu na kwarai , in ba haka ba muyi batan bakatantan bamu ga namu bamu ga nasu .
    Allah ya raba mu da sharrin shaidan

    ReplyDelete
  9. Assalamu Alaikum
    Shin shi wanda ya bayyana wannan mummunar abin, me ya samu? ko me zai samu tunda ya bayyana.
    Allah kadai yasan abinda shi wanda ya bayyana abin yake aikatawa
    domin irin wannan sabon Allah ai ba'a yin shi a fili,su dai ne nasu ya bayyana.saboda haka sai a taimaka masu da addu'a.
    Allah shi yafe masu ya yafe ma dukkan musulmi.
    Muhammad Abubakar kaura

    ReplyDelete
  10. Assalamu Alaikum 'yan uwa musulmi..
    dan ALLAH mu rinka tawakkali ga ALLAH mana, dan wannan abu ya faru ai badan tanuna ita tafi kowa iskanchi ta yishiba, ita kanta batayi tunanin abun zaizo ya fito har duniya tasaniba amma mu daukeshi kaddara domin idan ana tsine mata kusanifa zata dada lalachewane, to don ALLAH ina rokon jama'ar musulmi murunka taimakamata da addu'a domin hanunka baya rubewa ka yanke ka zubar don tazama dole agunmu tunda musulmache gata da farin jini, ke mache 'yar uwata dan ALLAH dan ANNABI ki taimaka mana da addu'a kema kuma ki dauka kamar 'yar uwarki akayiwa dominkuwa CHIWON 'YA MACHE NA 'YA MACHENE.ma'assalam 'yar uwarku a muslunchi I LOVE YOU MARYAM HIYANA.

    ReplyDelete
  11. I really appreciate this article especially the lessons we can learn from the clip. I think basically as you said it this is not just a mere act between an actress and her so called boy friend or partner, I think this is an issue that affects all the muslim society in general and the hausa community particularly. If we tank a glance in the past through the"evolution" of hausa film industry,I think we can objectively find the source of such obscenity. An actor is just some who as his name says act but there is a producer and all the staff that make a movie out. So from time to time people admire what these people are doing including their dresses and other dances as well you can see the most popular are those who dress "well" ie showing their bodies or those who dance like american. As I said it earlier we should know who we are, being a muslim is a total submission to all rules and regulations of Qur'an. So please don't speculate on the issue of Hiyana and Bobo, we are all accountable of their act. I hope this will be a starting point for Hausa muslims to come back to the truth and leave the culture of other to live our own culture that was shown by our prophet.

    ReplyDelete
  12. Allah ya kiyaye gaba, ya kuma shiryemu baki daya

    ReplyDelete
  13. Haba Sheme? Ka na ta cewa wai wasu na aikata laifi ai. Ba a kariya da irin wannan magana.

    Ku ne ke daure gindin rashin gaskiya saboda kai ma ka na samun wani abu na kudin sayar da shiriritar mujalla da sauransu.

    'Yan fim din na fa dukkan al'amarinsu da gyara a ciki. Ba su da asasi mai kyau kwata-kwata. Haduwa da maza da mata [yara danyu] dole ya haifar da bala'i. Da ma jin Kannywood ka san an bar hanyar - an yi koyi da Turawa tun daga "identity". A ganin mutane da yawa holewa ce kawai harkar; kuma ma ka lura sosai ka fi ni sanin su, shin wanda bai fahimci al'ummarsa ba yaushe ma zai ce zai koyar da ita wani abu.

    Ka ce wai ba za a iya hana fim ba - to wannan wani al'amari ne dabam. Don kuna ganin kila kuna da goyon baya a wurin masu fada-a-ji ko?!

    Wallahi, na damu kwarai da na ga "clip" din. Abin tausayi ce Maryam irin walakancin da ya yi mata. Kai karanta bayanin ma a jaridu sai da na dage. Saboda farkon ganin fim dinta, sai da na ce wannan yarinyar bai dace ta shiga shiririta ba ko kodan - a "screen" sai da zuciyata ta ce Maryam na da kunya. Amma kash, wani sai da ya zago ya cuce ta.

    Abin da ya faru kuwa farko cewa na yi am ba ta wani abu ne ta sha! Allah shi ne masani. Amma yawanci 'yan matanmu ba su da wayo a wurin mazaje shaidanu ko idan su na sonsu [they are too weak!]. Amma maganin bari kar a fara, in ji bahaushe - bayyanar da kai yadda za ka ga lambar wayarsu a hannun maza kala-kala har su iya kiransu da yin appointment shi ne asasin faruwar irin wannan aika-aika. Akwai ranar da wani na ji yana fada ai ya kawo wata 'yar fim wani otel ko za mu ganta. Wallahi, duk wanda ya ce yarinya ta bar gidansu, ta kama haya wai da sunan tana yin fim a Kano ko ma a ina ne bai daura gaskiya ba. Kuma batun wai nan gaba sai an shaide ta da hali na gari shi ma shirme ne - idan ta zo da hali na garin aka lalata ta fa? Ka ga ai an sanya ta cikin mummunar hanya.

    You know akwai abubuwa da yawa. In na ga 'yan matan fim na kan ce wai ina iyayensu ne su ke? Idan yaran wasu jinsi sun zama "so cheap to become objects of amusement" bai kamata yaranmu su zama haka ba. Al'ummarmu har yanzu da saura.

    Na yarda cewa abin da ya faru ya tono abubuwa - 'yan fim da ke kare kansu bisa irin fahimtar da aka yi masu [ka ga har su Kasimu Yero, Dan Wanzam, Tumbuleke, etc su ka daina drama ba a kawo laifinsu ba sosai]. Amma Kannywood fa? A bar ma ta "theme" dinsu kashi 99 wai soyayya da aure! Na kalli wani fim, kawai sai na ga gwamna a kan kujera three-seater yana waka! Lighting zero! Haduwa da mata too bad - a ina su ke canja kayansu a otel da gidaje? Yin bacci fa? Wai ma har da "Gala Night" - Turai kawai! Ga san kudi, cikin 'yan shekaru kadan ka ji wani ya ce wai bai san adadin yawan fim da ya yi ba - saboda ba quality! Akwai masu shirya fim masu ma'ana ko a nan Afirka, wasu shekaru su ke yi a na shiri yadda zai yi gasa a cikin fina-finan duniya ko na Afirka. Ka duba taron fim da aka yi a Ougadougu cikin shekarar nan [da fatan na kawo suna garin daidai]. Shin za ka hada su da irin yadda a mako guda wasu ke yin fim a Nijeriya [Aljazeera, cikin shirin "The Fabolous Film Show" na watannin baya, wani darektan fim a Nijeriya cewa ya yi su na shiri a mako daya, a na "reharsal a na "shooting".

    Daga karshe, ni a ganina, ya kamata ne mutune su rika kokarin rage matsalar al'umma ba karawa ba. An yi mana dariya kwananan saboda bala'in da ya kunnu kai na "clip" din; wani website da na duba cewa ya yi yanzu "Islamists" su ka fara daukar hanya. Wa ye ya jawo wannan cin fuskar, fisabilillahi, Sheme sai ka ba ni amsa!

    Allah ka rufa mana a asirinmu duniya da lahira, ka kuma shiryar da mu tafarki, ba na son zuciya ba, amin.

    ReplyDelete
  14. babu shakka wannan musibacew kuma baasan muslmi bahaushe da irin wannan tabargazaba babu abinda zaisa ayi shiru ayi lalwam kamar bawani abinda yafaru
    amma babban abind ayakamta ayi shine ayi maganin gaba kuma atilastawa wannan dan ta adda maci amaba ya aure wannan mata{khiyana}
    kuma yakamta yan nigeria su koma su zauna tsanake su duba yanayin gudanar da shirin finafinannan
    domin sau dayawa basu gwada al adu na mallam bahaushe yadda suke
    allah ya rufa mana asiri gaba dayanmu

    ReplyDelete
  15. KAWAI MUI ADDUA ALLA SHIRYEMU BAKI DAYA AMEEN

    ReplyDelete
  16. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  17. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  18. Nidai babu Abinda zance saidai nema mata yafiya a gurin ubangiji, Allah ya yafemata, kuma Allah ya kawar da tunanin mutane daga kan wannan video, Allah shine Mai rahama Mai Jin kai ba mutum, kuma akwai mutanan dasuke aikata munanan laifuka Wanda sukafi wannan Kuma su tufa sudaina kuma Allah ya karbi tufansu, itama itama idan ta roki Allah zai yafemata shi kadai ne me Rahama Mai Jin kai, Allah ya yafemana kurakuranmu baki daya.

    ReplyDelete
  19. So yanzu ina clib din yake?
    Send the Link pls to msmuhd2020@gmail.com

    ReplyDelete