Wednesday, 29 August 2007

Musulmi ne abokin gabar Musulmi

A cikin wannan makon, labari ya bazu a Kano cewa wai an samu wani sabon bulufim kuma na wata 'yar fim din, wato bayan na Maryam Hiyana da ya bazu a gari. Wai wata wadda sunan ta ya fara da suna "M" ce ita ma ta yi majigin batsa.

To a gaskiya na yi cikakken bincike, na gano cewa sam, labarin ba gaskiya ba ne.

Abin da ya faru shi ne, wasu shakiyyai (ko wani shakiyyi) ne suka dauki wani bulufim na Amerika, suka saka a cikin wayar GSM, suka ba shi sunan ita wannan "M" din, suka kuma yad'a a garin Kano cewa wai ita ma ta yi bulufim. Inda za ka san cewa ana bin 'yan fim da sharri da gangan shi ne yadda su kan su Turawan da ke cikin wannan fim, ba ma bakar fata ba ne, a'a, jajaye ne suke yin lalatar, to amma don sharri sai aka ba fim din sunan "M" din.

Don haka don Allah mu daina saurin yad'a ji-ta-ji-ta. Sai ka ga mutum bai yi wani bincike ba, amma da jin cewa an yi kaza sai ya shiga yad'awa, wani har a intanet (watakila don kada a riga shi!). Don Allah mu daina yad'a ji-ta-ji-ta. Mu tuna, a yau Musulmi shi ne babban abokin gabar Musulmi; Musulmi ne ke daukar wuka ya dab`a wa cikin sa. Mun ga haka a al'amarin Hiyana.

No comments:

Post a Comment