Wednesday, 26 September 2007

Film Burning In Kano


Sakamakon fushin da jama'a suka yi da 'yan fim kan majigin batsa da lalata na Maryam Hiyana da Usman Bobo, kwanan nan aka yi wani gangami na kona finafinan Hausa a birnin Kano.

A ranar 11 ga Satumba 2007 aka yi gangamin, a wurin bikin cikar shekara uku da kafa Hukumar A Daidaita Sahu (Kano State Commssion for Social Reorientation) wadda Malam Bala A. Muhammad ya ke jagoranta. A zauren wasa na dandalin Sani Abacha da ke Kofar Mata(Indoor Stadium) aka yi taron.

Bayan kammala bikin na cikar shekaru uku da kafa hukumar ne sai Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da mataimakin gwamnan Kano tare da shugaban masu rinjiye na Majalisar Dokoki ta Jihar Kano da Alkalin Alkalan jiha (Grand Khadi) su ka jagoranci kona finafinan a wajen harabar wurin.

Manyan mutanen sun cinna wa finafinai fetur da ke cikin wani daro wuta da sandar da ke hannun su, tare da yin Allah-wadai da irin gurbata tarbiyya da cin mutuncin addini da aka ce finafinan su na yi.

2 comments:

  1. Ga abin mai irony: an kona finafinai a dandalin mai suna Sani Abacha... Wato, Sani Abacha d'in ya fi mutuncin 'yan fim?...

    ReplyDelete
  2. Bai kamata a kona finafinai kawai ba , ya kamata a karada tsumagewa , domin sun jefa al'umma cikin tsaka mai wuya.

    ReplyDelete