Thursday, 31 January 2008

MACE MUTUM!


A yau Alhamis (ko in ce jiya, tunda karfe 1 ta haura) na shiga kasuwar Wuse, Abuja, inda na samu sayen littafin Mace Mutum na Rahma A. Majid. N820 na saye shi. Littafin ya dan yi kwana biyu da fitowa ban gan shi ba, ga shi kuwa wai ni ma d'an gida ne (tunda "kanen" marubuciyar ne!). Hasali ma dai na aika wa da wasu littafin, ciki har da Amina Abdulmalik (mai 'Ruwan Raina'), wadda ta na Katsina yanzu, na sa Danjuma Katsina ya kai mata kwafe har gida, kuma ta karanta har ta gama cikin kankanin lokaci!

Na aje littafin a kan teburi na a ofis. Duk wanda ya shigo sai ya dauka, ya yi mamakin girman sa, har wasu na cewa, "Wannan tarihin waye?" Ba su ga hoton Yar'Adua ko Babangida a bangon ba! Sai na ke ce musu, "Ai novel ne."

"Novel? Da ma ana yin novel da Hausa haka?"

Mutane sun saba da ganin littafi mai shafi 40 zuwa 70 na Hausa. Shi Mace Mutum, shafi 520 ne. Wane yaro!?

Kai, lallai Rahma ta ciri tuta! Mace mai kamar maza, kwari ne babu! Matar soja kin fi karfin yaro!

Allah ya sa sauran marubuta za su dauki hannu, su yi koyi da ita. Ni da ma na shafe shekaru ina yekuwar cewa ya kamata marubutan mu su rika yin rubutu mai inganci, kuma su rika yin littafi mai kauri-kauri. Su yi kokarin ficewa daga kangin 'Adabin Kasuwar Kano.' To, Rahma dai ta fara. Allah ya k'ara mata basira, da kwarin gwiwa.

Gobe (ko kuwa dai a yau!) zan fara karanta shi insha Allahu.

Kuma na kudiri aniyar saya wa marubuciya Sa'adatu Baba Ahmad Fagge kwafe daya in kai mata a gidan su a nan Abuja (domin fa ta na gari yau mako biyu, kuma na ziyarce ta sau biyu, gobe ma zan koma). Zan ba ta mamaki da kyautar littafin, domin ita ma har yanzu labarin sa kawai ta ke ji. Za mu yi tseren gama shi kenan.

Sallaman ku!

7 comments:

  1. Tabdi jam, a gaishe Sheme, kai ma ai namiji mai karfin mazaje dubune. Irin wannan kokari da kakeyi, sai dai muce Allah ya saka da Alkhairi.

    Wannan littafin, a gaskiya ina bukatarsa, sai dai gashi ni ina Maiduguri na nema ban samu ba, da so samu ne da munyi magana a waya sai na aika ma da kudi ka aiko min ta wannan adireshin

    Mustapha Ali
    P. O. Box 5058,
    Baga Road,
    Maiduguri - Borno State.
    email: busuguma@yahoo.com
    08059060331

    Ni member ne kanoonline.com ina amfani da suna Dan-Borno.

    Sai naji daga gareka

    ReplyDelete
  2. Na karanta wannan blog din kuma nima ina da sha'awar in karanta wannan littafin. Sai dai gashi ba a Nigeria nake da zama ba. A yanzu ina garin Leeds a England.
    Da Allah da akwai hanya nima da zan iya aiko da kudi a aiko mun da littafin? Ba ma shi kadai ba. Ina da sha'awar in samu wasu hausa novels din dan in karanta. Kamar na marubuta irin su Bilkisu Ahmad Funtuwa, Sa'adatu Baba Ahmad Fagge, Balaraba Ramat Yakubu, Fauziya D Sulaiman, da sauran su.
    Email address dina is: kdambatta85@gmail.com
    Na gode.

    ReplyDelete
  3. Mallam Ibrahim gaskiya ni ma ina da bukatar in karanta wannan littafi na Hajiya Rahama. Dan Allah ko ka san inda zan same shi a Kaduna? Har da ma littafin 'Yartsna wanda na dade ina jin labarinsa.

    ReplyDelete
  4. Mallam Ibrahim, barka da kokari

    bashahmad29@yahoo.com

    ReplyDelete
  5. Mimi kwa kweli kama ramani na picha ya juu ni kwa sababu inajenga hisia creepy. Hata hivyo, nadhani ni sanaa, na ni sehemu ya utamaduni. Ni kama buy viagra kwetu.

    ReplyDelete
  6. Mimi kwa kweli kama ramani na picha ya juu ni kwa sababu inajenga hisia creepy. Hata hivyo, nadhani ni sanaa, na ni sehemu ya utamaduni. Ni kama buy viagra kwetu.

    ReplyDelete