Tuesday, 14 October 2008
Dan Arewa A Washington
A ranar Laraba da ta wuce Allah ya kawo ni kasar Amurka a karo na farko. Na je wurare da dama (irin su White House da VOA), kuma na hadu da mutane daban-daban, musamman 'yan Nijeriya da ke Sashen Hausa na Muryar Amurka. Na hadu da su Malam Oumaten Attah da abokin sa Mal. Adamu Muhammad, wadanda 'yan Nijar ne. Ina jin ba zan iya ba da dukkan labarin balaguro na din ba sai na zauna na natsu, musamman bayan na koma Nijeriya.
Abin da kawai zan fada shi ne: mun zo taron shekara shkara na Bankin Duniya da IMF ne a birnin Washington, DC.
Zan tsakuro abubuwan da zan iya tsakurowa don sakawa a wannan taskar tawa har zuwa lokacin da Allah zai nufe ni da yin cikakken bayani.
Ga hoto na nan a gaban fadar Shugaban Kasar Amurka, wato White House, wadda na ziyarta shekaranjiya.
No comments:
Post a Comment