Monday, 9 February 2009

Tsare Iyan-Tama: Sabon Zubin Zalunci

BUD'AD'D'IYAR WASIK'A ZUWA GA MALAM IBRAHIM SHEKARAU

Daga IBRAHIM SHEME


Mai Girma Gwamna,
NA rubuto maka wannan bud'ad'd'iyar wasik'a ne saboda na yi amanna da cewa za ta fi saurin isa gare ka maimakon in bi hanyar da ku ka tsara, saboda ina da magana mai buk'atar sauri. Idan na mik'a wasik'ar a ofishin ka, za ta iya d'aukar kwanaki da yawa ko ma watanni kafin ta isa gare ka, kuma kafin lokacin ba za ka iya samun bayani na hak'ik'a ta kafa mai zaman kan ta ba kan tantagaryar zaluncin da wasu jami’an ka su ke aikatawa da sunan ka. Na biyu, tun tuni ma ake ta zancen a majalisun hira a tsawon watanni da su ka gabata. Yanzu akwai alamun an jingine maganar ta hanyar wata shari’a wadda ko kad'an ba ta da kan-gado, inda wasu masu fushi da fushin wani su ka yi amfani da ak'idar ka ta aiki bisa doka da oda, da tausayin talakawa, da rashin yaudara da kuma tanadodin Musulunci. Bugu da k'ari, buga wannan wasik'ar a bainar jama’a zai ba wa duk wani mai sha’awar sanin abin da ake ciki damar samun k'arin haske kan d'aya daga cikin muhimman al’amuran da ke gudana a gwamnatin ka.

Ran ka ya dad'e, ina da cikakkar masaniya kan wannan lamari, ba kawai don ina biye da maganar a kotun majistare ta Kano inda aka kai ta ba, a’a har ma saboda ni d'an cikin gida ne a al’amuran sana’ar finafinan Hausa. Ba sai na nanata maka ba cewa Kano ce cibiyar finafinan Hausa a sama da shekara goma da aka yi ana yin sana’ar.

Na tabbatar da cewa ba za ka rasa masaniya ba kan shari’ar da ake tafkawa tsakanin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano (KSCB) da wani furodusan fim ba mai suna Alhaji Hamisu Lamid'o Iyan-Tama. Ran ka ya dad'e, Iyan-Tama d'an asalin Kano ne wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da harkar finafinan Hausa gaba, sannan kuma d'an wasa ne d'an sahun gaba. Hasali ma dai shi ne shugaban farko da aka zab'a na K'ungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFPAN). Kowa ya san cewa bai tab'a shirya fim ko kuma ya fito a fim d'in da za a yi Allah-wadai da shi ba, wato wanda ya sab'a wa kyawawan al’adun jama’ar Kano ko addinin Musulunci. Duk rol d'in da zai yi a fim, za ka taras na manyantaka ne; ya kan nace kan lallai a yi fim da ya dace da al’adun mu, sannan shi mutum ne mai bin doka. Finafinan sa sun ci manyan kyaututtukan girmamawa.

Ran ka ya dad'e, idan har ka samu damar karanta wannan wasik'ar a yau, to Iyan-Tama ya kwana biyu a gidan yarin Kano, domin a ran Talata wata kotun majistare ta yanke masa hukunci kan abin da ta kira laifuffuka guda biyu, bayan an shafe watanni ana yawo da hankali a kes d'in. A hukuncin da kotun ta zartas, Iyan-Tama zai shafe wata uku a tsare ba tare da zab'in biyan tara ba. Haka kuma zai biya mak'udan kud'i na tara ko kuma ya yi zaman kaso na tsawon shekara d'aya.

Yawancin mu da ke sa ido kan lamarin ba za mu damu ba ko kad'an da hukuncin in da a ce da gaske Hamisu ya aikata laifuffukan. Ni d'in nan na yarda da bin doka da oda, domin hakan shi ne ginshik'in d'orewar mulkin dimokirad'iyya. Ba wanda ya fi k'arfin doka. In an yi amfani da wannan tsarin ne dimokirad'iyya za ta iya d'orewa kuma k'asa za ta samu zaman lafiya. To amma gaskiyar magana ita ce, Hukumar Tace Finafinai ce ta k'irk'iri laifukan da aka ce Iyan-Tama ya aikata, sannan wani alk'ali mai goyon bayan hukumar, wanda kuma ya yi k'aurin suna wajen d'aure duk wani wanda aka gurfanar a gaban sa, ko da bai da laifi, shi ne ya yanke masa wannan d'anyen hukuncin. Wani abin ban-damuwa shi ne ana tafka wannan aika-aikar ne da sunan tanadojin nan masu tsarki na Shari’ar Musulunci. Daga fahimta ta da abubuwan da ke fitowa daga bakin ka da ganin wasu abubuwan da ka aikata, har yanzu ban amince ba da cewa kai d'in nan za ka goyi bayan zalunci ta kowace fuska ko kuma ka bar wani ya na saka siyasa cikin shari’ar Musulunci don ya ci mutuncin jama’a cikin son rai.

’Yallab'ai, bari in d'an fad'a maka abin da ya faru. Jami’an Hukumar Tace Finafinai sun kama Iyan-Tama a ofishin sa a Kano, su ka kai shi kotun tafi-da-gidan- ka wadda aka kafa don yi wa ’yan fim da marubuta shari’a (aka fad'ad'a zuwa duk wani nau’i na rubutu). Abin mamaki, babu wata kotu irin ta; babu kotun ’yan acab'a ko ta karuwai ko ta ’yan caca ko ta ’yan luwad'i, da sauran su. An tuhumi Iyan-Tama da "laifuffuka" guda biyu:

1. Sakin fim d'in sa na ‘Tsintsiya’ a Kano ba tare da Hukumar Tace Finafinai ta amince da shi ba kamar yadda doka ta tanada;

2. Gudanar da kamfanin shirya fim mai suna Iyan-Tama Multimedia, ba tare da yin rajista da gwamnati ba.

To amma duk wad'annan tuhumar, k'arya ne, kuma lauyan sa ya yi k'ok'arin nuna wa alk'ali Alhaji Mukhtar Ahmed hakan. An d'auki watanni kafin a yanke hukuncin, wanda ya yi matuk'ar girgiza yawancin mazaunan Kano da wajen ta.

Bari mu fara da tuhuma ta biyu. An yi wa kamfanin Iyan-Tama Multimedia rajista da gwamnati wato a Corporate Affairs Commission (CAC), wadda ke da alhakin yi wa dukkan kamfanoni rajista a Nijeriya. Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta ce wai Iyan-Tama bai sabunta rajistar sa ta shekara-shekara da ita ba. Wannan ma k'arya ce domin watanni kafin a kama shi, ya sayi fom d'in har an ba shi rasid'ai. To wanda ya yi wannan yunk'urin ai ya na kan hanyar yin rajistar ne kuma bai yi kama da wanda ke k'ok'arin karya dokar yin fim a Kano ba. Kuma ya na da amincewar gwamnatin tarayya.
Tuhuma ta farko ma ta fi ban-haushi. Ran ka ya dad'e, Iyan-Tama bai saki fim d'in ‘Tsintsiya’ a Kano ba. Hasali ma dai ya yi tallace-tallace da hirarraki a rediyo da jaridu kafin a k'addamar da fim d'in a Abuja, inda ya fito k'arara ya ce ba za a saki fim d'in a Jihar Kano ba.

A lokacin da Hukumar Tace Finafinai ta yanke shawarar "koya wa Iyan-Tama darasi," jami’an ta sun karya shagon saida finafinai na HRB da ke unguwar Tarauni a Kano, su ka samo faifan sidi na fim d'in, wanda wani d'an wasan fim ya b'oye cikin durowar teburi wanda ya ce a Kaduna ya sayo shi da nufin zai ba wa wata mai sha’awar finafinan sa. Ba wai an kasa sidi d'in don sayarwa ba. B'ullar sa a Kano bai da wata alak'a da Iyan-Tama. Idan ka karanta takardun kotu inda lauyoyi ke yi wa jami’an Hukumar Tace Finafinai su biyu tambayoyi a gaban alk'ali, za ka yarda d'ari bisa d'ari cewa ba a tabbatar da cewa Iyan-Tama ne ya kawo faifan sidi d'in wannan shagon ba.

A bayyane ya ke cewa shari’ar Iyan-Tama ramuwar gayya ce kurum. Wani b'angare ne na yunk'urin yak'i da wasu ’yan fim ko ta halin k'ak'a wanda Hukumar Tace Finafinai ta d'aura. A gajeren tunanin hukumar, ta hanyar yin haka ne za a iya share duk wani abu na sana’ar fim da harshen Hausa. Hukumar ta na amfani da bak'ar farfaganda, ta na ba da bayanan k'arya, tare da yin ragguwar fassarar Dokar Tace Finafinai ta 2001, sannan ta na amfani da sunan Musulunci ta hanyar da ba ta Musulunci ba wajen sauya alk'iblar hanyoyin nishad'i a Kano.

Mai Girma Gwamna, duk wannan ya sab'a wa furucin ka na tabbatar da adalci. Kuma hakan ya haifar da abubuwa marasa dad'i ga gwamnatin ka da kai kan ka, wad'anda zan fad'a maka su yanzu tare da duk girmamawa a gare ka.

Ya Girma Gwamna, yak'in da ake yi da sana’ar fim a Kano, ana yin sa ne da sunan Shari’ar Musulunci, to amma ko kad'an ba Musulunci ba ne. Wad'anda ke yin yak'in sun yi gangami ne su na furta kalaman Alk'ur’ani mai tsarki da Sunnar Manzo, to amma abubuwan da su ke aikatawa kai ka ce Hitla ne ya ce su aikata shi. Babu wani abu da su ka aikata kan ’yan fim da ya nuna cewa sun bi nasihohin Annabi Muhammadu (SAW). Kamar yadda na fad'a a sama, tsarin da su ke bi na halaka sana’ar fim ta na da illa matuk'a, ba wai kawai ga ’yan fim ba har ma ga gwamnatin Jihar Kano. Zan d'an bayyana wasu daga cikin illolin yanzu:

1. An jefa dubban matasa cikin rashin aikin yi bayan kuwa a da su ne su ke sama wa kan su hanyoyin abinci, wanda hakan ya shafe su tare da iyalan su. Ba a sama masu wasu hanyoyin na daban ba domin samun abinci. Mayak'an ka su kan ce, "Ina ruwan mu da su? Ai yawancin su ba ’yan Kano ba ne!" To amma hakan ya sab'a wa k'ok'arin gwamnatin ka na sama wa d'imbin matasan Kano da aikin yi.

2. Yak'in ya kawo koma-baya ga tattalin arzikin Kano wanda da ma ya na cikin garari. Da yake manyan kamfanonin Kano duk sun durk'ushe, kamata ya yi a gina harkar fim ta yadda za ta kasance mai dogaro da kan ta, kuma wadda ta dace da al’adun Kano da dokokin hukuma. Maimakon a yi hakan, sai aka koma ana kashe ta.

3. An haifar da fargaba da rashin sanin alk'iblar rayuwa a zukatan matasan, kuma da yawan su sun koma ’yan maula.

4. An haifar da k'in Shekarau a zukatan matasan. Hujja ita ce irin wak'ok'in b'atanci da ke ta bayyana daga situdiyoyin wak'ok'in finafinai a Kano, Zariya da Kaduna. Da fari, irin wad'annan wak'ok'in su na sukar Hukumar Tace Finafinai ne, to amma yanzu akalar su ta sauya har su na had'owa da gwamna da iyalin sa. Kai, wak'ar da ta fi yin fice a wannan fagen ma, an shirya ta ne a situdiyon da wani na hannun daman ka ya mallaka, to amma Hukumar Tace Finafinai ta kasa yin komai a kai saboda shi mai situdiyon ba ya tab'o a gare ta. Wannan tsanar da ake yi wa Shekarau ta na ta k'aruwa kuma za ta iya kasancewa bak'ar guguwa ga jam’iyyar ANPP a zab'en da za a yi a shekarar 2011 a Jihar Kano.

5. An fara yin shakku kan manufa da kuma alk'iblar yekuwar Shariar Musulunci, wadda miliyoyin jama’a su ka runguma. Duk shugaban da ke yin nasihar adalci da gyaran tarbiyya, bai kamata ya hana dubban matasa hanyoyin samun abincin su ba.

Ran ka ya dad'e, ina daga cikin masu goyon bayan shirin ka na gyaran zamantakewar jama’a ta yadda za su yi daidai da al’adu da tanadodin addinin da jama’ar mu ke bi. Shi ya sa na ke goyon bayan shirin gwamnatin ka na A Daidaita Sahu, wanda abokin mu Malam Bala Muhammad ke aiwatarwa cikin ban-sha’awa da kuma samun cikakkar nasara. To amma Hukumar Tace Finafinai ta na warware duk wata tufka da A Daidaita Sahu ta cimma nasarar yi. Gaba d'aya tsarin a baud'e ya ke, kuma ana aiwatar da shi a kan tafarkin mugunta da ramuwa da rashin jin k'ai. Ya kauce wa duk wani tsari na ya-kamata.

Mun yarda da cewa sana’ar finafinai ta shiga rud'u wanda ya kamata a gyara ta a cikin shekarun baya. Hakan ya k'ara bayyana ne bayan b'ullar majigin batsa na Hiyana. To amma akwai buk'atar a jawo shugabanni na sosai na industiri d'in don a samu nasara. Maimakon haka, sai Hukumar Tace Finafinai ta ture su gefe d'aya, ta jawo wasu ’yan koren ta, sannan ta na shirya tarurruka na yaudara da rainin wayo, har ma da shirya dina don magoya bayan ta su zo su ci abinci. Ba shakka, wannan tsarin na raba kan jama’a da farfaganda irin ta ’yan Nazi da hukumar ke yi ba abin da ya haifar sai bala’o’i, sannan an samu gazawa a wajen gyaran tarbiyyar industirin finafinan Hausa.

Har yanzu ana sayar da finafinai da fosta-fosta na batsa a Kano. Haka kuma, ’yan k'alilan d'in finafinan Hausa da magoya bayan Hukumar Tace Finafinan su ka shirya (tare da amincewar hukumar don a b'oye k'aryar cewa ba kashe sana’ar fim ake yi ba) ba su da wani bambanci da irin finafinan da hukumar ta ke ik'irarin cewa marasa inganci ne. Don Allah, finafinai masu inganci kuma "wad'anda sun dace da tarbiyya", guda nawa ne aka shirya a k'ark'ashin jagorancin Hukumar Tace Finafinan tun daga lokacin da majigin Hiyana ya fito?

Ran ka ya dad'e, za ka yarda da ni idan na ce maka ainihin dabarar shirin fim ba aba ce mai illa ba, don haka bai kamata a kashe ta ba. Za a iya shirya finafinai kan jigogin rayuwa iri-iri wad'anda su ka dace da al’adun mu. Kamata ya yi a yi wa ’yan fim jagora, ba wai a rik'a yi masu b'atanci ba ko kuma a yi masu korar kare daga gari.

Ran ka ya dad'e, Hamisu Iyan-Tama dai fursunan siyasa ne: ya yi adawa da kai lokacin zab'en 2007 ta hanyar fitowa takarar gwamna shi ma. Ai bai ma yi maka wata barazana ba. Kai aka k'ara zab'a. To amma saboda tsaurin idon da su ke ganin ya yi na yin takara da kai, jami’an ka su na hukunta shi. Sun ce wai shi mutum ne mai cika baki, mai surutu kuma wai ya na sukar gwamnatin ka. To mun ji, shin su d'in ba masu cika baki ba ne, su na yin abu sai ka ce sun fi kowa iko a duniya? Shin ba sa kallon duk wani wanda bai yarda da ra’ayin su ba a matsayin abokin gaba ko su kafirta shi, ko maras bin biyayya gare su, ko su ce ai ba d'an Kano ba ne ko kuma bai san ainihin abin da ake ciki ba? Shin wannan ba babbar d'agawa ba ce?

Kuma ma ko da a ce Iyan-Tama na da cika baki ko kuma abokin adawar ka ne na siyasa, shin hakan hujja ce ta hukunta shi da zaman gidan yari duk da yake bai karya doka ba? Shin ya yi maka illa a siyasance irin illar da masu surutan nan ke yi maka a gidan Rediyon Freedom? Shin a ina dimokirad'iyyar da ake ta magana ta ke? Shin ko Manzon Allah (SAW) ko wani daga cikin halifofin sa ko d'imbin tabi’an da su ka biyo bayan su za su bi irin wannan hanyar don hukunta abokin adawa?

Mai Girma Gwamna, ya kamata ka binciki wannan al’amari na Iyan-Tama, don Allah, musamman rawar da alk'alin da ya d'aure shi ya taka a shari’ar da sauran shari’un zalunci da ya yi wa masu sana’ar fim. Kuma don me za a ce kotu ta na yi wa wata hukumar gwamnati aiki? Don me alk'ali d'aya ne kad'ai zai rik'a yin duk wata shari’a da ta had'o da Hukumar Tace Finafinai bayan an ga sau da yawa ya nuna inda bakin sa ya karkata? Shin wannan mutum ne mai tsoron Allah ko kuwa d'an siyasa mai k'ullatar jama’a?

Ka yi amfani da k'arfin mulkin ka ka fitar da Iyan-Tama daga k'angin da aka saka shi a ciki ta hanyar janye k'arar da ku ke yi da shi a kotu. Na san ka na da zuciyar yin hakan domin ai ka tab'a yin irin haka a wasu al’amura da su ka had'o da kai, ciki kuwa har da wanda ya had'o da b'atancin da aka yi wa maid'akin ka. Kada ka bari wasu mutane ’yan d'oki wad'anda ka ba muk'amai su rik'a yak'ar abokan adawar ka ta hanyar zalunci domin kuwa Gobe K'iyama za ka amsa tambayoyin ka ne yayin da za su amsa nasu daban da naka.

’Yallab'ai, zan tsaya nan sai nan gaba za mu k'ara yin wannan magana da sauran maganganu a nan gaba. Ni ne mai biyayya a gare ka, kuma mai ba ka shawara tagari. Wassalam.

(Wannan fassara ce na sharhin Turanci da na yi kwanan baya. An wallafa wannan na Hausan a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'a da ta wuce)

1 comment: