Thursday, 9 July 2009
ALA: Korafin Marubuta Mata
A yau din nan marubuta biyu mata sun yi magana kan tsare Amiunu Ala da aka yi. Ta farkon su ita ce fitacciyar marubuciyar nan Rahma A. Majid (wadda hoton ta yake kan shafin nan) sai kuma Malama Maryam Ali Ali, wadda ita ce sakatariyar kudi ta Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA). Sun yi magana ne a Majalisar Marubuta ta Yahoogroups. Ga abin da su ke cewa:
RAHMA A. MAJID:
DON ALLAH KADA MU YARDA!!!
"Lokaci ya yi da zamu hada karfi da karfe ta kowane sashi na adabi mu yaki gwamnatin
zalunci da manufofin ta. Kullun sai sharhi muke kan abinda muka rigaya muka sani kan manufofin hukumar zaluncin amma mun kasa jajircewa mu yi aiki kai tsaye. An kafa hukumar tace-tace domin ta tato duk wanda zai yi amfani da ganga, majigi, ko alkalami ya tona asirin manufofin ta na murdiya. Na jima da aka sinsina min haka tun a lokacin da ba a kafa hukumar karara ba inda wasu masu daure da irin zanin ta suka yi ikirari a jaridar New Nigeira cewa sun ba ni tallafin karatu sanda nake jami'a da sunan littafi na bai dace da fiqihu ba(don tsananin jahilcin kasa bambance shara'a, adabi da fiqihu). Amma a wancan lokacin Rahma wadda take bakuwa bata sami wanda ya tayata hangen abinda zai faru a yau ba har sai da yayi nisa.
"To! Ko a yanzu in an mike ba a yi laifi ba. Kira daya da zan yi na neman hadin kan uudabaĆ¹ shine a yi wa Allah a yi wa adabi, kada a bar wannan fafitika ta zamo ta neman a saki Ala kawai. Don Allah ko da an wanke shi mu katange junan mu baki daya daga sabon cin fuska da dauki-dai-dai da wannan hukuma ke mana a sanadiyyar son girma, ko neman gindin zama ko rashin hadin kai, ko hassadar mu ta tsaga wa kadangare bango.
"Hakika a watan Nov. insha Allahu na shirya dawowa majalisa with full force, amma saukar da wannan sako ya yi a gadon bayan zuciya ta ya sa dole na karya doka ta."
MARYAM ALI ALI:
"Salam,
"A gaskiya yadda Ala ya bauta ma wannan gwamnatin da baiwar sa, abin ya zama abin
tsoro in har za a yi mai haka, to lallai kam, abin da razanarwa, kowa ma ya shafa
ma kansa da gemun sa ruwa."
Preach on sisters! Haba, enough is enough. I'm not a writer (yet!) but I'm a fan of Hausa literature and I think enough is enough of this nonsense that the Kano state "censorship board" is doing!
ReplyDeleteOur constitution allows freedom of speech! It's almost as if people are not allowed to have an opinion anymore....it's not fair! people are frustrated!