Thursday, 23 September 2010

Wai da sunan ’yancin addini!

A makon ba a ji irin ta ba. Wai so ya yi a yi gangamin }ona Al}ur'ani mai tsarki a ranar Asabar da ta gabata. Tun lokacin da faston ya bayyana wannan }udiri nasa a dandalin duniya na intanet (a shafin Facebook), da sunan “Ranar Babbaka Al}ur’ani ta Duniya”, aka shiga musayar miyau kan al’amarin a ko'ina a fa]in duniya. Shi dai wannan bidiri, wata }aramar majami'a ce mai suna Dove World Outreach Centre da ke garin Gainesville da ke jihar Florida ta }asar Amerika ce ta shirya shi, a }ar}ashin fasto mai suna Rabaran Terry Jones, a matsayin tunawa da kewayowar ranar harin }unar Ba}in Wake ]in nan da aka kai wa Amurka da jiragen sama a watan Satumba 2001. Kowa ya zuba ido ya ga abin da zai wakana, amma kwatsam, a ranar Alhamis ta makon jiya sai fasto Jones ya bayyana ]age taron.

Wannan ]agewa da ya yi ta sa Musulmi a fa]in duniya sun yi ajiyar zuci, sun yi murna, to amma kuma sun ji haushin kasawar da faston ya yi. Sun yi murna domin hakan ya sa an kauce wa faruwar wata fitina da ba a san inda za ta tsaya ba in ta tashi, sun kuma ji haushi saboda gangamin na Jones ashe soki-burutsu ne, kuma wata hanya ce ta neman suna. Duk da haka, Musulmi sun fahimci cewa soke gangamin ya }ara nusasshe mu da al}awarin da Allah (SWT) Ya yi a cikin littafin Sa mai tsarki cewa Shi mai karewa ne ga wannan Littafi a koyaushe.

Ba Musulmi ka]ai ba ne su ka yi murna da ]age gangamin }ona Al}ur'anin. Hatta Kiristoci da Yahudawa sun yi murna, domin kusan kowannen su ya yi tir da yun}urin da faston ]an shekara 58 ya yi. A gaskiya, babu wani Kiristan kirki da zai goyi bayan irin wannan aika-aikar. Dalili shi ne, duk da yake Musulmi da Kirista sun bambanta matu}a kan manyan ginshi}an addinan su, amma su na girmama junan su, musamman ma a wannan zamani da duniyar ta }an}ance, ta zama tamkar wani ]an }aramin }auye inda kowa ya san kowa, sannan jama’a mabambantan addinai su na rayuwa tare a cikin gari ]aya ko }asa ]aya. Jones dai ya yi }aurin sunan da ya so ya yi, to amma kama tun daga fadar Fafaroma zuwa fadar shugaban Amurka har zuwa kan jarumar finafinai Angelina Jolie babu wanda bai yi Allah-wadai da shi ba. Daga birnin Montreal na }asar Kanada har zuwa Nijeriya babu wanda bai yi kira a gare shi da kada ya kuskura ya tafka wannan shirmen nasa ba.

An yi zanga-zangar nuna rashin amincewa a }asashe da su ka ha]a da Afghanistan da Pakistan da Indonesiya. Fadar Fafaroma ta ce Kiristoci “ba su amince da wannan gagarumar ~arnar da ake shirin yi kan littafin da mabiya wani addini su ka amince da cewa mai tsarki ba ne.” Wani shugaban Kirista a Lahore, babban birnin Pakistan, wato Achibishop Lawrence John, ya bayyana }udirin Jones da cewa ya “sa~a wa girmamawar da mu ke yi wa dukkan addinai kuma bai yi daidai da a}ida da kuma karantarwar addinin mu ba.” Shugaban Kiristocin }asar Lebanon, Michel Suleiman, ya ce barazanar gangamin }ona littafi mai tsarkin “bayyanannen sa~ani ne ga karantarwar addinan nan uku da su ka samo tsatso daga jinin Annabi Ibrahim da kuma bu}atar daraja juna a tsakanin su.” Addinan dai su ne addinin Yahudanci (Judaism), da Kiristanci da kuma Musulunci.

A birnin Washington na Amurka, shugabannin addinai daban-daban sun yi babban taro a cibiyar ’yan jarida ta }asa inda su ka yi kira ga mabiyan addinai da su ha]u su yi bataliyar yin artabu da “fargaba da rashin ha}uri” da ake nuna wa Musulunci. Shi kuma tsohon babban limamin cocin Katolika na Washington, wato Kadinal Theodore McCarrick, kiran }iyayyar da ake yi wa Musulunci ya yi da sunan “babban lokaci da ke bu}atar babban martani.” Sannan a}alla shugabanni guda 24 na addinai daban-daban da ke kusa da cocin Jones a garin Gainesville sun shirya gudanar da ayyuka don nuna }in gangamin }ona Al}ur’anin. Wani fasto da ke majami’ar United Church ta garin Gainesville ]in, wato Larry Reimer, ya ce Jones “ba ya wakiltar kowa... Abin da ya ke yi babu girmamawa a ciki, sannan babu ruwan Allah a ciki, wanda Shi ne ya ce mu }aunaci junan mu.”

A nata ~angaren, gwamnatin Amurka ta ji tsoron cewa ’ya’yan }asar za su iya shiga wani mugun yanayi a }asashen waje. Shugaba Barack Obama ya bayyana }udirin Jones da cewa zai ba }ungiyar Al}a'ida damar samun }arin membobi. Jami'an gwamnatin sa ma sun yi nuni da hakan. Misali, Janar David Patreaus, wanda shi ne kwamandan sojojin Amurka da ke Afghanistan, ya bayyana wannan ba}ar aniya ta Jones da cewa ita ce “ainihin irin abin da }ungiyar Taliban ta ke amfani da ita kuma za ta jawo mana manyan matsaloli - ba ma a nan }asar ka]ai ba, har ma a sauran sassan duniya inda mu ke mu’amala da al’ummar Musulmi.” Takwaran sa da ke Ira}i ma, Janar Ray Odierno, ya yi garga]in cewa idan har aka ci gaba aka yi wannan gangamin na }ona Al}ur’ani, to babu shakka akwai raddin da zai biyo baya daga Musulmi. Ya ce: “Ina da damuwar cewa hakan zai jawo a kai wa sojojin mu hare-hare.” Ita kuma ministar harkokin waje ta Amurka, Hillary Clinton, ta yi tir da yun}urin ne, ta ce “babban abin kunya” ne.

Idan mun lura, daga kalaman da ke sama, za mu iya fahimtar cewa }udirin fasto Jones bai samu tagomashin sauran Kiristoci ba, don haka ba wai dukkan su ba ne su ka ha]e wa Musulunci kai su ka ce a yi hakan. Kawai wasu tsirarun masu tsattsauran ra’ayi ne su ka shirya abin; hasali ma dai, kwata-kwata mabiyan Jones mutum 50 ne a duk }asar. Na biyu, Jones ya yi amfani da irin damar da kafafen ya]a labarai na Amurka su ke ba ’yan taratsi irin sa ne wajen ya]a manufar sa. Su wa]annan kafafe, da ma haka su ke kambama }an}anin abu, su maida shi }ato; kowane irin shirme aka wurga masu da sunan abin labari ne, sai kawai su ]auka su bi duniya su na yayatawa. In da ba su yayata wannan shirmen na Jones ba, to da shikenan hankalin kowa ba zai tashi ba.
Na uku, shugabannin siyasa na }asashen Turawa sun }i goyon bayan Jones, ba wai kurum don ya sa~a wa karantarwar addinin su ba, har ma saboda yun}urin wannan ja’irin zai iya jefa ’yan }asar su da ke waje cikin ha]ari. Na hu]u, wannan lamarin ya }ara tabbatar mana da cewa tunanin nan da wasu masana ke yi na cewa wata rana za a kwafsa tsakanin }asashen Turawa da Musulunci, har yanzu bai kau ba. Ba shakka, }udirin Jones babbar alama ce da ke nuna cewa mabiya addini masu }iyayya da duk wani addini su na }ara zurfafa }iyayyar su a cikin yun}urin su na ganin bayan ]aya addinin. Idan kuwa haka ne, ashe akwai babban aiki a gaban masu }o}arin ganin an samu fahimtar juna da zaman lumana a tsakanin addinai mabambanta.

A gaskiya, a }asashen Turawa ne ka]ai, musamman ma a Amurka - inda duk abin da aka ce maka zai yiwu, to zai yiwu - ake samun wani wanda ake ganin babban mutum ne a }asar ya shirya irin wannan aika-aikar har a saurare shi. Amma abin tambaya shi ne, me ya sa hukumomin Amurka ba su yi }o}arin hana shirmen Jones ba maimakon su tsaya su na ba shi magana? Na san amsar da za a ba ni ita ce ai wannan coci na garin Gainesville ya na da dama, a }ar}ashin tsarin mulkin }asar, ya yi abin da ya ga dama bisa ’yancin yin addini. Lokacin da Jones ya ce ya soke gangamin }ona Al}ur’anin, ya yi }o}arin danganta yun}urin sa da wani yun}urin da wasu Musulmi su ke yi na gina masallaci a harabar wurin da aka kai hare-haren jiragen saman nan a cikin 2001. Wannan ba wani abu ba ne illa }o}arin yi wa Musulmi tarna}i na ba gaira ba dalili, domin kuwa ai gina masallaci a wurin ba wula}anta addinin Kirista ba ne. Ni a ra’ayi na, bai zama ma dole a gina masallaci a wurin ba; dalili: yin hakan zai }ara gur~ata dangantaka da ’yan }asar wa]anda ke kallon wurin a matsayin wata fuska ta tsantsar Amerikanci, kuma zai zafafa dangantaka a tsakanin addinai. Kamar yadda Obama ya fa]a, gina masallacin bai sa~a wa doka ba to amma ba lallai ba ne a ce ya dace - wato kamar yadda wani jami’in fadar White House mai suna David Axelrod ya ce lokacin da ya ke tarfa yawun bakin sa kan aniyar Jones, inda ya ce ta yiwu Jones “ya na da ’yancin yin hakan. Amma abin tambaya shi ne ko hakan ya dace.”

A yanzu dai akwai alamun cewa wannan hayaniya ta Jones ta wuce, to amma fa kada mu yi sake. Har yanzu akwai sauran rina a kaba domin kuwa akwai mutane masu ra'ayi irin nasa da yawa a Amurka, kai har ma a Nijeriya. Ya kamata }asashen Turawa su sake yin nazarin dokar su ta ba da cikakken ’yancin addini. Tsaron lafiyar jama’a ha}}i ne da ya rataya a wuyan gwamnati. Idan har abin da Jones ya yi }o}arin aikatawa barazana ce ga tsaron Amurka kamar yadda masu magana su ka fa]a, shin wannan bai zama kamar ya na karya dokar Amurka ba kenan? Shin ba akwai Musulmi masu yawa ba da ke tsare a }iri}irin tsibirin Gwantanamo kawai bisa zargin sun yi abin barazana ga bu}atun Amurka?
Kyakkyawar aniyar nan ta Obama ta rage rashin jituwar da ke tsakanin }asashen yammaci da addinin Musulunci ta na samun barazana daga mutane masu tsattsauran ra’ayi irin su Jones. Barin irin wa]annan mutanen su na ya]a }iyayyar su ya sa~a wa }udirorin da Obama ya ta~a zayyanawa a gagarumin jawabin da ya yi a jami’ar Al-Azhar ta Misira lokacin da ya hau mulki. Shi ’yancin yin addini, kamar kowane ’yanci, ya na fa da iyakoki; ’yanci ne da ya ba ka damar ka yi addinin ka, amma bai ba ka damar ka hana wani yin nasa addinin ba. {ona Al}ur’ani - wanda hakan ya nuna tsananin }iyayya ne - ya na nufi a hana Musulmi su gudanar da addinin su, ta hanyar wula}anta addinin su, da tsoratar da su da kuma muzanta su. Wasu ’yan tsirarun masu tsattsauran ra’ayi ba su da ’yancin yin duk wani abu da zai iya jawo ramuwar gayyar da za ta yi sanadiyyar salwantar rayukan wasu wa]anda ba su ji ba ba su gani ba.

Ya kamata kuma mu fahimci cewa in da wannan ta’asar ta yi nasara, to za ta iya bazuwa a wasu }asashen wa]anda ba ruwan su da haukan da aka kitsa a Gainsville. Ko yanzu ]in ma, maganganun sa~o da Jones ya ri}a furzaswa kan Musulunci ya ba}anta ran Musulmi da yawa, musamman ma da yake cikin Ramadan ya ri}a yin su, wato wata mafi tsarki a Musulunci. Shi fa Jones, wanda ba ya wakiltar Amurka ko addinin Kirista, bai damu ba idan wani ya mutu a sanadiyyar shirmen da ya tafka. Shi da kan sa ya nuna hakan lokacin da ya fa]a wa gidan talabijin na ABC cewa wai “abin ba}in ciki ne” idan ko da ran mutum ]aya ya salwanta a dalilin wannan abu, “to amma duk da haka, mu ba mu damu da cewa laifin mu ba ne.” Don Allah, Amurka kada ki bari mutane irin wa]annan su na aikata abin da su ka ga dama wai da sunan ’yancin yin addini.

No comments:

Post a Comment