Tuesday, 8 March 2011

Ka zama aminin ’ya’yan ka!

Duk uba ya na so ya samu kintsattsen ]a, ballantana a ce mai haza}a ne. Ya na so ’ya’yan sa su kasance masu }o}ari a makaranta, masu girmama na gaba da su, masu ]a’a, masu tsare gaskiya, masu tsafta, masu tsoron Allah, masu sauraren ra’ayin da ba su yarda da shi ba, wayayyu, masu jin }ai ga marasa galihu da marasa lafiya ko marasa }arfi, da sauran su. Haka kuma ya na yi masu addu’ar samun nasara a rayuwa, ta hanyar arziki ko samun ci-gaba a wurin aikin su. To, in kuwa haka ne, ya za mu yi mu reni ’ya’yan da za su kasance nagari?

Kwanan nan, ni da wani aboki na mu ka shiga hira kan irin yaran da ake samu a wannan zamanin namu, kai har ma kan yadda mu ke mu’amala da junan mu a cikin al’umma. Na girgiza matu}a kan yadda na ga hul]a ta na }ara }azancewa a }asar mu a yau, musamman ma tsakanin iyaye da ’ya’yan su, maza da matan auren su, malamai da ]aliban su, shugabannin addini da mabiyan su, da kuma ’yan siyasa da nasu mabiyan. Kawai a dalilin }in amincewar da mu ka yi kan abin da ya kamata da wanda bai kamata ba a al’umma, sai ka ga wasu su na ta ya}ar juna. Duk an maye gurbin hanyoyin }warai na sasanci ko gyara koma]ar hul]a da wasu sakarkarun hanyoyin da ba za su ta~a haifa mana da ]a mai ido ba.

A shekarun baya, iyaye da sauran shugabannin al’umma su kan horas da ’ya’yan su ne ta hanyar matsi, su na gudun kada su kauce wa hanya su lalace ta hanyar bin wasu ababen rayuwar zamani. Su na gudun kada ’ya’ya su kangare, su zama marasa ]a’a. Ana yi wa ’ya’ya horo da bulala ko tsabga don kada su lalace.

A hirar da mu ka yi da abokin nan nawa, na fi nuna damuwa ne kan yadda mu ke tarbiyyantar da ’ya’yan mu, tare da kawo hujjoji. Irin tarbiyyar da aka yi mana mu na yara ita ce babban dalilin da ya sa mu ka zama abin da mu ka zama a yau. A wancan zamanin, ana horas da ]a ne ta hanyoyi da dama, wa]anda su ka ha]a da lalama da kuma hukunci mai tsanani. Shi aboki na, wanda mabiyin gargajiya ne in an zo maganar tarbiyyar ’ya’ya, ya yi amanna da cewa rashin matsanta wa ’ya’ya da iyaye ke yi a yau shi ne ya haifar da lalacewar ’ya’ya da yawa.

To amma abin tambaya shi ne: shin duk magidantan da ke da ]a’a da yakana a yau sai da su ka sha kashi daga hannun magabatan su kenan? Shin hanyar tarbiyya ta zamanin da ta fi ta yanzu kuwa? Babu shakka, akwai hikima mai }arfi a hanyoyin da iyayen mu da kakannin mu su ka bi a nasu zamanin, to amma fa tuni abubuwa su ka soma canzawa. Iyaye da malaman makaranta na wannan zamanin sun fara tunanin ko akwai alfanu a cikin duka ko zagin ’ya’ya don a koya masu abin da ya dace da wanda bai dace su yi ko su fa]i ba. Sun fara yarda da cewa zai iya yiwuwa a koyar da ’ya’ya tarbiyya mai kyau ba tare da an ri}a zane su a kai a kai ba. Sirrin abin shi ne kai uba ko uwa ka tabbar da cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin ka da ]a ko ’yar ka; ka koyar ta hanyar nagartattar halayya kai kan ka, kuma ka jawo iyalin ka a jika. Ya na da muhimmanci ga iyaye su ri}a magana a kai a kai da ’ya’yan su, su saurari abin da su ke cewa. Rashin }ulla zumunci da ’ya’yan mu ya na gina katangar }arfe a zukata, wadda ita kuma ta kan haifar da abubuwan ~acin rai. Idan ’ya’yan mu sun ~ata mana rai, mu fito mu fa]a masu, mu nuna masu kuskuren su, maimakon mu haukace mu dinga fitina. Mu tabbatar da cewa mu na aiki da a}idar }in yin gaba ko rashin ]asawa da ’ya’yan mu, wato abin da zan kira da “rashin yin gaba a tsakanin mu.” A ta}aice, iyaye, malaman makaranta har ma da ma’aurata za su iya tirjewa ba tare da sun tsauwala ba a kan a}idar su ta rayuwa.

Zan rufe wannan ma}alar da wani labari da wani mutum mai suna Mista Arun Gandhi, wanda jika ne ga babban ]an kishin }asar nan na }asar Indiya, wato marigayi Mahatma Gandhi, ya ta~a bayarwa a wurin wani taro da aka yi a Jami’ar Puerto Rico a ran 9 ga Yuni, 2010. Shi Arun, wanda shi ne shugaban cibiyar fidda sa~ani ta M.K. Gandhi, wato M.K. Gandhi Institute for Non-violence, ya yi wannan bayanin ne a wani jawabi da ya gabatar a matsayin misalin zaman lumana a cikin iyali. Ga abin da ya ke cewa:

“Ina ]an shekara 16 da haihuwa kuma ina zaune tare da iyaye na a cibiyar da kaka na ya kafa a wani wuri da ke mil 18 a bayan garin Durban, a }asar Afrika ta Kudu, a cikin gonakin rake. Mu na zaune a gidan gona, inda ba mu da ma}wabta, don haka sai ya kasance ni da ’yan’uwana mata guda biyu mu kan so mu samu damar shiga cikin gari ziyarar abokai ko kuma mu shiga silima.

“Ran nan sai mahaifi na ya bu}ace ni da in tu}a mota in kai shi gari don halartar wani taro na kwana ]aya. Murna ta kama ni. Da yake zan shiga gari, sai mahaifiya ta ta ba ni jerin sunayen wasu kayan lambu da ta ke so in sawo mata, kuma da yake zan wuni a cikin garin, shi ma baba na sai ya ba ni wasu ayyukan da ya ke so in yi masa, ciki har da yi wa motar sabis. Da na aje baba na a wurin taron da safe, sai ya ce mani, ‘Mu ha]u a nan da }arfe 5:00 na yamma, sannan mu wuce zuwa gida.’

“Da sauri, na gama ayyuka na, sai na zarce kai-tsaye zuwa wani gidan silima da ke kusa. Na tsunduma cikin kallon wani fim ]in Amurka na jarumi John Wayne, ban ankara ba har }arfe 5:30 ta yi sannan na tuna. Kafin in je garejin gayan mota in ]auko mota in tafi inda baba na ke jira na, har }arfe 6:00 ta yi. Cikin damuwa, ya tambaye ni, ‘Me ya sa ka makara?’

“Ina jin kunyar in fa]a masa gaskiyar cewa na tsaya kallon fim ]in John Wayne ne, sai na ce, ‘Ba su gama aikin motar da wuri ba, shi ya sa na tsaya,’ ashe ban sani ba har ya buga waya garejin, ya gano komai. Da ya gane cewa }arya na ke, sai ya ce: ‘A gaskiya akwai wani abu wanda ba daidai ba a yadda na tarbiyyantar da kai wanda ya sa ba ka da }arfin halin fa]a mani gaskiya. Saboda haka, don in fahimci ko ina ne na yi kuskure game da kai, zan taka a }asa mil 18 zuwa gida in yi tunanin abin.’ Saboda haka dai, a cikin shigar sa ta kwat da wando da takalma sau ciki, sai ya fara takawa zuwa gida da dare a kan hanya marasa kwalta, kuma a duhu. Ba zan iya tafiya in bar shi ba, don haka sai da mu ka shafe awa biyar da rabi ina bin sa a baya da mota, ina kallon mahaifi na ya na shan ba}ar wahala kawai saboda shirmen }aryar da na shara. Tun a lokacin na sha alwashin cewa ba zan }ara yin }arya ba.

“A ko yaushe, na kan yi tunani kan wannan abin, kuma ina tunanin cewa in da ya hukunta ni ta yadda mu ke hukunta ’ya’yan mu a yau, to da ban koyi darasi ba ko }iris. Ban tsammanin zan iya. Da kawai zan sha wuyar hukuncin da ya yi mani, amma zan ci gaba da aikata kuskuren da na yi. To amma wannan abin guda ]aya da ya yi na nuna rashin fushi ya yi matu}ar tasiri a rayuwa ta, ta yadda ina ganin kamar jiya jiyan nan abin ya faru. Wannan shi ne }arfin }in yin fushi.”

No comments:

Post a Comment