Wednesday, 29 August 2018

Littafin "Shata Ikon Allah!" ya fito!

Littafin "Shata Ikon Allah!"



Alhamdu lillah! Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!

Bayan na shafe shekara 12 ina aiki kan sake rubuta shahararren littafin nan na tarihin Alhaji (Dr) Mamman Shata Katsina, da zurfafa bincike a kan rayuwar sa, a yau dai Allah (SWT), mai kowa mai komai, ya yi ikon sa, littafi ya shigo hannu na. An kammala dab'in sa da shirya shi a bisa sabon fasalin da ya dauka. Allah na gode maka!

Wannan littafi, wanda Shata da kan shi ne ya ba ni izinin rubuta shi, ya bambanta da wanda na jagoranci rubutawa a baya, wato wanda ya fito a shekarar 2006. Ko makaho ya shafa, zai ji bambancin. Ya inganta ta fuskar kyautata bincike da nazari, ya inganta ta fuskar yawan shafuka, ya inganta ta fuskar kyan dab'i, ya inganta ta wajen yawan shafuka.

Shafi 921 ne. Akwai shafi 32 masu dauke da hotuna masu kala, wadanda aka buga kan takarda mai santsi.

A cikin littafin, akwai hotuna guda 580. A cikin su, akwai hotuna masu kala har 98.

Babu littafin da na taba shan wuyar rubutawa kamar wannan. Na yi yawo a garuruwa da kauyuka. Na kashe kudi ban san adadin su ba. Na rika zama a tebur, a gaban komfuta, daga safe zuwa karfe 2 na dare, na tsawon watanni, na hana kai na more rayuwa yadda ya kamata, kafin wannan aiki ya kammala. Sannan na sha fama da masu cewa don Allah yaushe wannan littafi zai fito? Masoyan kenan. Na sha fama da masu zunden cewa na rike littafi, na hana shi fitowa. To, Allah ya yi - wai aure da mara kwabo - a yau ga kwafen littafin ya shigo hannu na.

To yaushe zai shiga kasuwa? Ai har ma ya shiga, domin kuwa ko a gobe za mu iya sayar da shi ga duk mai so.

Addu'a ta ita ce Allah ya sa a ce gara da aka yi. Allah ya sa albarka.
Allah ya jikan Alhaji Muhammadu Shata, amin.


Ibrahim Sheme

No comments:

Post a Comment