Thursday, 11 October 2018

Ina Kudin Kaddamar Da Littafin Shata? Wasikar Aliyu Ibrahim Kankara Ga Marigayi

Wannan rubutun da ke kasa ba nawa ba ne, na Aliyu Ibrahim Kankara ne. Shi ya wallafa abin sa a turakar sa mai suna Taskar Mamman Shata a ranar Alhamis, 16 ga Satumba, 2010 (wato shekara takwas da su ka gabata). A ciki, ya yi bayani kan taron kaddamar da littafin mu na "Shata Ikon Allah!" a cikin shekarar 2006. A cikin 'yan kwanakin nan, Kankara ya wallafa zargin cewa wai ni, Ibrahim Sheme, ni ne na cinye kudin taron kaddamar da littafin Shata wanda aka yi a 2006.

Ban yi karambanin yin editin din wannan rubutun nasa ba, don haka duk yadda aka gan shi haka ya rubuta kuma ya gabatar da kayan sa. In da hali ma, ya kamata mai karatu ya ziyarci turakar ta Dr Kankara, ya gane wa idon sa. Adireshin shi ne:
http://taskarmammanshata.blogspot.com/2010/09/budaddiyar-wasika-zuwa-ga-dokta-mamman.html


BUDADDIYAR WASIKA: Zuwa Ga Dokta Mamman Shata 

 

 Daga Aliyu Ibrahim Kankara

 

Ranka shi dade Yallabai, Ban yi niyyar rubuta maka wannan ‘yar guntuwar takarda ba,ban kuma yi niyyar rubuta ta da wata manufa don birgewa ko don in matsa maka a inda kake kwance ba, a’a Allah shi baka nasara tun lokacin da muka zanta da kai ranar asabar 19/9/1998 akan wallafawa da kaddamar da littafinka tun a sannan ka ga irin kokarinmu da kishin mu na ganin mun tallata abubuwan da ka yi a rayuwar ka.Littafi dai bai kammala ba sai bayan da ka bar wannan sararin. Kai kanka ka yi kokarin ganin littafin ya fito da wuri sai dai kash,a sannan rashin lafiya ta addabeka,wanda qarshe Allah bai yi zaka ga kaddamar da littafin ba. To, an qaddamar da littafi ranar asabar 7/8/2006 amma kusan ba’a taru ba a yanda ya kamata. Cikin aminanka da basu da adadi ina iya kirga maka waxanda suka halarci wurin:daga Sa’in Katsina Amadu Na Funtuwa sai Ammani Inuwa Fage Kano, sai Umaru xan Duna na Gwandu(direba) sai Alhaji Hassan Hadi da marigayi Dan Tireda Ali Gombe sai Hakiman Funtuwa(sarkin Maska Mainasara Idris kenan) da Musawa sai Alhaji Adamu Yusuf BBC marigayi. Ni kaina na tafi da Hajiya Maimuna Mairo Munari daga Funtuwa. A wurin, naga wasu da ban iya tantancewa ko kunyi alaqa tare ko a’a ba, kamar su ritaya Kanar Bello Kaliyal(tsohon Gwamnan Bauchi) da Janar Garba Duba(ko da yake shi aiko shi akayi ba zuwan kanshi ba ne), na kuma ga Musa Gwadabe(tsohon ministan ma’adinai) da shugaban Jami’ar Bayero, farfesa Attahiru Jega. Shi ASD(Alhaji Sani Dauda) ba’a ma gayyace shi ba a rediyo yaji ana shirin ya tashi ya je ya kuma bada naira dubu 100 saboda kaunar ka.Sarkin Zazzau ma ya aika da naira dubu 250 duk sabili da son ka.A nan mutane da dama masu qaunar tsakani da Allah sun je wurin da ban ma yi tsammanin za su je ba. Amma duk ‘yan siyasar nan da sarakuna da manyan sojoji da masu hali da ka wake duk basu je ba,alhali mun taka har gidajensu mun kai masu katunan gayyata. Sannan an kaddamar da littafi amma duk alkawurran da masu kaddamarwa suka yi basu bamu kudaden ba. Ga dai jerin sunayen wadanda muka biyo bashi na littatafan da suka kwasa: 1.Alhaji Sama’ila Isa Funtuwa(shine ma babban mai kaddamarwa)= naira 2,000,000. 2.Janar Ibrahim Badamasi Babangida =naira 1,000,000. 3.Gwamnatin Jihar Gombe =naira 250,000 4.Alhaji Dahiru Barau Mangal= naira 250,000 5.Alhaji AY Gombe= naira 100,000. 6.Alhaji Muntari Dandutse(shugaban karamar Hukumar Funtuwa)=naira 150,000 7.Alhaji Maitama Sule Danmasanin Kano= naira 100,000 8.Alhaji Sahabi Liman Kaura ya bamu ceki na kudi mun je Banki ba kudin=naira 50,000 Dokta Aliyu Modibbo shi ya biya kudi kaka buga littafin ya kuma buga katin gayyata ya kuma kama mana hayar wurin bukin, shi kuma ya jagoranci nemo masu kaddamarwa.Shima din ya taba kiran mu Abuja don mu amso kudin karshe bamu samu dammar ganin sa ba.Munje ga Alhaji Sama’ila Isa sai yace mu je mu samu Modibbo.Muka sake komawa Modibbo ba halin mu ganshi,don alokacin ministan Ciniki ne bashi ganuwa.Muka gaji da gararanba cikin Abuja kamar shegu marasa galihu muka dawo gida.Saima asarar kudi har dubu 14 da nayi.Na shiga mota na neme sun a rasa.Kaga garin nemo qiba na rame a Abuja. A waje daya ga wasu ‘ya’yan ka mazan suna ta azalzalarmu cewa mu basu kudi,sun dauka ko dai munyi sakacin qin amso masu kudin ko kuma mun amsa mun kashe. Yau shekara uku kenan ba wata magana ba alamar kudin za su fito, mu kuma wallafe-wallafen da muke yi da hirarrakin da mu keyi a rediyo na bayyanawa duniya wanene Shata bamu fasa ba, ba za kuma mu fasa ba. Ka duba kaga irin yanda ka sadaukar da rayuwar ka ka taimaka wa jama’a:ka yi hanya an ba wasu sarautu,ka yi hanya an ba wasu mukamai a gwamnati,arzikin wasu yak are ka taimaka masu,wasu sun rasa muqaman su ka taimakesu an mayar masu,wasu kuma ka basu kudi da abinci saboda tausaya masu.Amma yau gashi saboda an ga ba ka a duniya kowa ya watsar da hidimarka da abinda ya shafe ka. Yanzu an yi maka adalci kenan? Alhali kai da kana raye na tare da kai har tausayink a suke,don in ka xauko kudi da dukiya kana badawa kamar ba zaka bar ma iyalanka komi ba. Jama’a da dama sunce kyautar ka irin ta mutanen da ce:kyautar da in mutum yazo maka da matsalar kudi to bazaka bashi rabin kuxin ba ka ce ya tafi ya nemi sauran a’a gaba daya zaka bashi. Shata, ka tuna fa a da can duk maroqanka kusan ka kaisu Makka. A cikin 1970 kawai, a Kano ka biya wa mutum ashirin Hajji gaba daya. Ka yi waqoqi sama da 8,000 da bama nan nahiyar ta Afirka ba kawai har ma Jami’o’in Amurka da Turai suna nazarin su suna amfana da su.Tun cikin shekarun 1940 da 1950 aka fara nazarin waqoqin ka a can. Domin a Jami’ar Kalifoniya da ke Los Angeles a Amurka kawai Turawa kusan shidda suka amshi digiri na Ukku ta hanyar nazarin waqoqin ka da rayuwarka.Amma daga karshe yallabai kaga sakayyar da akayi maka.

No comments:

Post a Comment