Monday, 8 October 2018

Yadda Na Jagoranci Rubuta Littafin Tarihin Mamman Shata

A ranar Juma’a, 21 ga Satumba, 2018 jaridar Aminiya (ta kamfanin Media Trust Limited) da ke Abuja ta soma buga wata tattaunawa da ta yi da ni. Daga nan ta ci gaba da buga hirar a makwanni biyu masu zuwa, wato a ranakun 28 ga Satumba da 5 ga Oktoba. A rana ta farko, kanun labarin hirar (headline) shi ne “Ni Na Fara Aikin Rubuta Littafin Tarihin Shata – Ibrahim Sheme”, a mako na biyu kuma kanun labarin shi ne, “Abin Da Ya Sa Na Sake Rubuta Littafin Tarihin Shata Karo Na Biyu – Ibrahim Sheme”, sannan na ƙarshen shi ne “Ina Shirin Samar Da Gidauniyar Adana Ayyukan Shata Da Na Sauran Mawaƙa – Sheme”.

Wanda ya yi hirar da ni shi ne Bashir Yahuza Malumfashi.  Ga yadda hirar ta kasance:

*
Littafin "Shata Ikon Allah!"

Ni na fara aikin rubuta littafin tarihin Shata – Ibrahim Sheme

A kwanakin baya ne marubuci kuma ]an jarida, Ibrahim Sheme ya fitar da wani babban kundi da ke }unshed a tarihin shahararren mawa}in Hausa, marigayi Mamman Shata Katsina. Aminiya ta gana das hi, inda ya warware zare da abawa na fa]i-tashin day a sha wajen samar da wannan littafi mai suna SHATA IKON ALLAH!

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Ko za ka bayyana yadda ka fara tunanin tunkarar rubutu game da marigayi Mamman Shata?
Da farko dai, mahaifi na ne ya fara haɗa ni da Alhaji Mamman Shata. Sun san juna matuƙa ta yadda zan iya cewa mutumin sa ne ƙwarai duk da yake bai yi masa waƙa ba. Mahaifi na shi ya ɗauke ni ya kai ni wajen Shata, ya ce masa, "To ga ɗan ka." Har Shatan ya yi ta mamakin cewa na yi girma haka. A lokacin, ban daɗe da gama jami'a ba. To ni kuma sai soyayyar Shata ta ɗarsu a zuciya ta, ya kasance a ko yaushe ina so in je in gan shi. Don haka a duk lokacin da na samu sarari, na kan je in gaida shi a gida.

Ana cikin haka, ina aiki a Kaduna a matsayin Mataimakin Editan jaridar mako-mako ta Nasiha, sai na yi tunanin me zai hana a matsayi na na marubuci in rubuta tarihin Shata? A lokacin, ba a damu da rubuta tarihin mawaƙan Hausa ba, an fi yin ƙoƙarin rubuta tarihin wasu manyan mutanen irin 'yan siyasa da ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa don a kira taron ƙaddamarwa a samu kuɗi. Ni kuma ina yi wa Shata wani irin kallo na fasihin mutum wanda ya kamata a taskace ayyukan da ya yi a rayuwar sa. Ni mutum ne mai yawan karance-karance, don haka na jima da ganin alfanun hakan a wasu al’ummomin. A ƙarshe, sai na tafi Funtuwa na sami Alhaji Shata har gida, na faɗa masa niyya ta, kuma ya amince da buƙata ta. A cikin 1991 na fara aikin, kuma na fara yin hirar farko da shi.

Littafin da ku ka haɗu ku ka samar na farko mai suna “Shata Ikon Allah!”, yaya al’amarin ya gudana kuma me ya biyo baya?
Na dai na fara aikin a 1991, to har na yi shekaru da farawa sai Allah ya hada ni da wani mutum mai suna Aliyu Ibrahim Ƙanƙara. Bari ka ji yadda abin ya faru. Daga 1991 ɗin nan har zuwa 1996 na ɗan yi abubuwa bakin gwargwado. A 1992 na bar jaridar Nasiha, na zama Editan mujallar Rana (ta kamfanin mujallar Hotline). A 1993 na tafi ƙasar Birtaniya domin yin digiri na biyu a Jami'ar Cardiff. Da na dawo, na ɗan yi aiki a matsayin Editan mujallar Hotline kafin in koma jaridar kullum-kullum ta New Nigerian, inda har na yi Mataimakin Edita.

Duk a tsawon wannan lokaci ban daina aiki kan tarihin Shata ba. A daidai lokacin ina da wani aboki mai suna Ibrahim Malumfashi, wanda malami ne a Jami'ar Usmanu Ɗanfodiyo a Sakkwato, yanzu kuma farfesa ne a Jami'ar Jihar Kaduna. Wata rana, ina jin a cikin 1997 ne, sai ya zo har gida na ya ce mani akwai wani mutum da ya ce masa ya na so ya gan ni kan aikin rubuta tarihin Shata. Ya ce mani mutumin ya ce shi ma ya na rubuta tarihin Shata kuma ya na so mu haɗe mu yi littafi ɗaya. Ya ce sunan mutumin Aliyu Ibrahim Ƙanƙara, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna, wato Kaduna Polytechnic.

Kamar ba zan amince ba, amma Malumfashi ya ja hankali na kan cewa mu dai ha]u da wancan ɗin, in ji da wacce ya zo, kafin in yanke shawara. Sai na ce to shi kenan, su zo tare, in ga abin da shi Ƙanƙara ya rubuta.

Washegari, su ka zo gida na. Ƙanƙara ya zo da littafi inda ya yi rubutu mai yawa da biro. Na karɓa na shiga dubawa. Sai na lura da cewa Ƙanƙara na da irin azamar da na ke buƙata, kuma har ya yi hira da wasu mutanen da Shata ya yi wa waƙa waɗanda ina so in yi hira da su. A lokacin ni ma fa na yi hirarraki da mutane da dama waɗanda shi bai kai gare su ba, irin su Indon Musawa, Shehu Maigidaje, Goshin Ɗangude, Amadu Doka, Garban Bichi, dangin Shata a Musawa, da sauran su. To, sai na ga lallai haɗewar mu za ta taimaki dukkan mu; ka ga ai ba sai na tafi wajen waɗancan mutanen da ya yi hira da su ba, shi ma ba sai ya je wurin waɗanda na yi hira da su ba. Saboda haka nan take na ce na yarda mu yi littafi ɗaya. Babban dalili na shi ne ni ba domin in samu kuɗi na ke yin aikin ba, buri na dai in cimma nasarar tattara tarihin Shata, saboda haka ko waye ya zo ya ce mu haɗu mu kai gaci zan amince.

A nan Ƙaanƙara ya bar mani wannan rubutu da ya yi, a matsayi na na jagoran aikin. Haka kuma, bayan wani lokaci, na ɗauke shi a mota ta, na kai shi wajen Shata a Funtuwa na ce, “Baba, wannan shi ne wane. Yanzu da shi mu ke rubuta tarihin ka, ya na taimaka mani.” Shata ya ce to ba komai tunda ni na yarda da hakan.

To, daga nan fa sai mu ka bazama aiki, shi ya yi nan, ni in yi can. Wani lokacin mu tafi waje tare. Da yake aikin tattara tarihin Shata kamar teku ne, sai dai ka ɗebi na ɗiba ka bar sauran, haka mu ka dinga tafi da aikin bakin iyawar mu.

Ina so ka sani cewa babu wata ƙungiya ko wani mutum da su ka ɗau nauyin mu kan wannan aikin; ni ne ke ɗaukar nauyin yawancin aikin, da yake bakin gwargwado na fi Ƙanƙara samu. Duk inda za mu, ni ke ɗaukar nauyin mu. Haka kuma na kan tura Ƙanƙara wasu wuraren, in ba shi kuɗin zuwa da dawowa. Misali, na tura shi Bauchi ya wo mana hira da Garkuwan Bauchi Alhaji Ahmed Kari, na tura shi Gombe ya yi mana hira da Garkuwan Gombe Alhaji Bappa Ahmed, wanda Shata ya yi wa waƙar "Ɗan Liman Uban Ciroma, Ɗan Shehu Garkuwa", na tura shi Musawa ya wo mana hira da Magajin Gari Abdullahi Inde da su Ayuba Mainama da sauran su dai. Amma ya kamata ka sani, ni ma fa ba a kwance na ke ba, ina nawa rangadin. Kuma dai ni ne ke zuwa wajen Shata a kai a kai, ina sanar da shi halin da ake ciki.

Ana cikin haka, rannan na je wajen Shata sai ya sanar da ni cewa wasu mutum biyu sun same shi a Kabo Guest Inn a Kano, wato otal ɗin Jarman Kano Alhaji Muhammadu Adamu Ɗankabo, sun faɗa masa cewa su na rubuta tarihin rayuwar shi. Ya ce, "Ka san su?" Na ce ban san su ba. Sai nan take wasu yaran Shata da na ke da matuƙar kusanci da su, irin su Alhaji Ya'u Wazirin Shata, su ka ce ai kuwa ya kamata a kira su nan Funtuwa a hana su ci gaba da aikin, domin dai ni aka sani, ni aka amince wa.

Shata ya yarda. Ya ce to yaya za a yi a gano su? Na ce ina da abokai marubuta a Kano, zan iya zuwa in gano su. Aka sa ranar da za a ce su zo Funtuwa mu haɗu mu duka idan na gano su. Daga Funtuwa, na ja mota ban zame ko'ina ba sai Kano. Ta hanyar wani aboki na, marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino, na shiga bincike har aka kai ni wani gida a unguwar Daneji, aka ce nan ne gidan su Ali Malami, wato ɗaya daga cikin waɗanda aka samu labarin su na aiki kan tarihin Shata. Na yi masa sallama, ya fito. Da mu ka tattauna, ya tabbatar mani da cewa lallai shi da wani mai suna Yusuf Tijjani Albasu sun fara rubuta tarihin Shata. Na isar da saƙon cewa to Shata na neman su a Funtuwa a rana kaza. Ya ce to in-sha Allah za su je. Ban faɗa masa matsayi na a wajen rubuta tarihin Shata ba.

Daga Kano, sai na zarce zuwa gida Kaduna. Na samu Aliyu na faɗa masa abin da ake ciki. Da ranar ta zo, mu ka rankaya zuwa Funtuwa - ni da Ƙanƙara da wani aboki na da na ɗauka a Zariya, wato Yahaya Umar. Mu ka yi sa’a, Alhaji Shata bai je ko'ina ba. Da ya fito zaure ya zauna, aka taru kamar kullum, ana jiran isowar Kanawan nan. Can kuwa sai ga su sun iso tare da wani abokin su. Kuma sun zo da littafin su kamar yadda aka ce su yi. Abin da aka shirya shi ne idan sun zo, za a ƙwace littafin ne, a kore su bisa hujjar cewa Shata bai ba su izinin rubuta tarihin rayuwar shi ba! To amma sai na ce a ba ni dama in duba aikin da su ka yi. Su duk ba su san shirin da aka yi ba.
Na karɓi littafi biyu da su ka cika da rubutu da biro, mu ka koma waje, na jingina da mota na shiga dubawa. Littafi ɗaya na ƙunshe da matanonin wasu waƙoƙin Shata, yayin da ɗayan - wanda shi ya fi jan hankali na - ya na ɗauke da hirarraki da wasu mutane da Shata ya yi wa waƙa. Kamar dai yadda na gano lokacin haɗewa ta da Ƙanƙara, sai na ga cewa lallai Kanawan nan sun yi aiki irin wanda na ke so; sun yi hira da wasu mutane waɗanda mu ke da burin ganawa da su, irin su Delun Kunya, Abubakar Uwawu, Umaru Ɗanduna, Liman ’Yalleman, Laila Dogonyaro, da sauran su.
Da mu ka koma gaban Shata, sai na ce masa, "Baba, ni ina ganin ya kamata mu haɗe da waɗannan su ma, a yi littafi ɗaya."
Sai mamaki ya kama kowa. Shata ya ce, "Haka ka ke so?" Na ce, "E." Ya ce, "To ai shi kenan." Sai na bada shawarar mu koma waje mu tattauna tare da Ali Malami da Yusuf Tijjani Albasu. Da mu ka koma, na faɗa masu irin aikin da mu ka yi, kuma na nuna masu namu aikin tare da ɗimbin hotunan da mu ka tara. Nan take su ma su ka amince da cewa mu haɗe mu huɗu mu yi littafi ɗaya.

Bayan mun tattauna, na rubuta takardar yarjejeniya, mu ka koma gaban Shata, na karanta ta kowa ya ji. Aka amince, kowa ya rattaba hannu a kan cewa mun haɗe.

Daga nan, aiki ya koma ɗanye. A matsayi na na jagoran aikin, na kira taro a Kaduna, inda mu ka tattauna kan yadda aikin zai kasance, musamman abin da ya rage mana, da kuma yadda za a yi mu ci gaba da tunkarar aikin. Kowannen mu zai ci gaba da bincike kamar yadda mu ka faro, sannan ni ne marubucin littafin, wato ni ne zan karanta abin da kowannen mu ya farauto, in saƙa shi cikin sassan littafin kamar yadda na tsara shi.

A tsawon lokacin da mu ka yi, na lura da wani abu. Abokan aiki na sun damu matuƙa kan lallai in gama littafi a ƙaddamar da shi. Ni kuma gani na ke ta yi har yanzu ban samu kaiwa inda na ke so littafin ya kai ba; kullum gani na ke yi akwai giɓi nan da can. Ana haka, har Shata ya fara ciwon ajali, ya koma ga Mahaliccin shi. A ƙarshe, littafin bai fito ba sai a cikin 2006, wato shekara bakwai bayan rasuwar Shata.

Ga shi bayan wasu shekaru masu yawa, ka fito da sabon littafin “Shata Ikon Allah!” Yaya aka yi haka ta faru?
Da aka ƙaddamar da littafin mu na farko a Gidan Arewa a Kaduna, sai mu ka lura da cewa ba mu samu kuɗi ba kamar yadda mu ke so. Yawancin mutanen da su ka yi alƙawarin bada kuɗi a wurin, ciki har da babban mai ƙaddamarwa, ba su cika alƙawarin su ba - har yau ɗin nan! Wasu ma cakin kuɗi na bogi su ka bayar a bikin ƙaddamarwar. Sannan kwafen littafin guda 1,000 da aka ce za a buga mana, ba mu samu ko da 600 ba, saboda haka babu ma na sayarwa. Aka bar mu da basussuka. Hakan ya sa mu ka kasa ba iyalin Shata ko sisi kamar yadda yarjejeniya ta buƙaci mu yi.

Sai mu ka zauna mu ka shawarta cewa mu yi ƙoƙarin sake fito da littafin don mu sayar, mu ga ko za mu fanshe ta nan. Sai na ce kowannen mu ya je ya karanta littafin ya ga ko akwai kurakurai da ya kamata mu gyara, da yake ni na rubuta shi na bayar aka buga ba tare da sauran sun samu lokacin karanta shi kafin a buga ba. Haka kuma na ce ya kamata mu zurfafa bincike, tare da tattaunawa da wasu mutanen waɗanda ba mu samu zantawa da su ba kafin a buga littafin. Mu ka rabu a kan haka.

To, tun daga nan fa sai na fara Allahn-ba-ku da abokan aikin nawa. Kusan kowannen su ya ƙi ba ni haɗin kai kan abin da na ke so mu yi. A gani na, sun gaji da aikin. Mutum ɗaya ne ma ya karanta littafin ya ba ni wuraren da ya gano an yi kuskuren rubutu, misali a rubuta 'Shta' maimakon 'Shata' ko 'Dara' maimakon 'Daura'. Amma su kurakuran ma ba su da yawa sosai. Daga nan babu wanda ya ba ni ko kalma ɗaya a matsayin ƙarin bayani na bincike ko hira da wani mutum. Duk wanda na nemi ya yi wani abu, sai ya goce. Kai, akwai ma wanda ya turo mani da saƙon tes daga Kano ya ce don Allah don Annabi in rabu da shi, shi ya fita in dai aikin littafin Shata ne, ba ya so! Na kira abokin aikin mu ɗayan, na faɗa masa, ya ce e, shi ma ya faɗa masa haka. Shi kenan, ni sai na ci gaba da bincike na.

Abin ban-mamakin ma, sai na samu labarin cewa Aliyu Ibrahim Ƙanƙara na can ya na ƙoƙarin fito da wani littafin kan Shata. Da na tuntuɓe shi kan maganar, da farko ya ce ƙarya ake masa. Mun ɗau shekaru ina fama da shi a kai, domin an kai lokacin da na tabbatar da cewa lallai ya na kan aikin, ina nuna masa cewa sake fito da wani littafin zai kasance cin amanar mu duka. Na zauna da shi a Kaduna da Katsina ba sau ɗaya ba, ina nuna masa cewa abin da ya ke so ya yi bai dace ba, musamman tunda babu yadda za a yi ya rubuta wani littafi ba tare da ya kwashe bayanan da ke cikin wanda na rubuta ba, kuma idan ya yi hakan zai kasance ya karya dokar haƙƙin mallaka tare da satar basira. Na ce masa kamata ya yi ya ba ni duk wani sabon bincike da ya yi, in haɗa da wanda na yi, a zuba cikin sabon littafin da mu ka amince mu yi.

Da ƙyar na samu ya ba ni wani sashe na littafin, daga babi na 1 zuwa na 6; ya aiko mani da shi ta hanyar Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, ya kawo mani a Kaduna. Ya haɗo da hotuna kaɗan, sannan ya turo mani wasu hotunan ta imel.  Da na duba, sai na kira shi na ce to ina sauran littafin? Ya ce iyakar abin da ya rubuta kenan. Na san ba haka ba ne. Duk da haka, na karanta na ɗauki abin ɗauka, na watsar da yawancin abin da ke ciki domin kuwa an kwaso wajen kashi 80 cikin ɗari ne daga bugun farko na "Shata Ikon Allah!" A ƙarshe ma dai, sai na bi wata hanya na samo sauran littafin da ya hana ni, wato babi na 7 zuwa ƙarshe, kuma na kira shi na faɗa masa, har na karanta masa abubuwan da ke ciki. Ya yi ta mamaki.

Na ɗauka zai karaya, ya bari mu haɗe kamar yadda ya amince. Amma sai na riƙa jin cewa ya na fa ci gaba da ƙoƙarin fito da littafin, har ya rubuta takardu zuwa ga gwamnatin Jihar Katsina, ya na roƙon ta ba shi kuɗi ya buga littafin. Duk na samu takardun da ya rubuta, kuma na sanar da shi.

A ƙarshe dai, kwatsam sai na ji Aliyu ya fitar da littafi. Ina jin ko a 2016 ne? Da na ga haka, sai na ƙyale shi. Na ce in dai don ya na ganin zai samu kuɗi da littafin ne kamar yadda ya ke ta tsinkaya, to ya je ya samu. Ni dai ba domin kuɗi na ke fafutikar tattara tarihin Shata ba. Don haka sai na yi bakam, na ci gaba da nawa binciken ni kaɗai, ina yi ina rubuta littafi, har tsawon shekarun nan goma sha biyu. A ƙarshe, na ƙare, na gamsu da cewa littafin ya kai matsayin a fito da shi.

Kada ka manta, wannan littafin da ya fito ya ƙunshi "Shata Ikon Allah!" na farko, ya ƙunshi littafin Aliyu Ƙanƙara mai suna "Mahadi Mai Dogon Zamani" (wanda shi ne sunan  farko da na raɗa wa namu littafin kafin Dakta Aliyu Modibbo Umar ya ba ni shawarar cewa in canja masa suna zuwa "Shata Ikon Allah!"), sannan ya ƙunshi sabon binciken da na yi. Saboda haka wannan sabon littafin da na fito da shi, in dai ka same shi, to ba ka buƙatar wancan namu na farkon da kuma na Ƙanƙara domin ya ƙunshi dukkan su. Abin da babu a ciki daga na Ƙanƙara yawanci shi ne irin almarorin nan da ya ke yaɗawa game da Shata, misali wai an yi wa mahaifin Shata girka har aljanu su ka yi bushara da haihuwar mawaƙin ko a daren da aka haifi Shata an ji kiɗan kalangai na tashi a sararin samaniyar garin Musawa ko kuma Shata ba mutum ba ne aljani ne.


Menene bambance-bambancen da ke tsakanin wannan sabon littafin da na farko?
Bambanci na farko shi ne wanda ido ke gani tun kafin mutum ya buɗa littafin. A bugun farko, shafi sama da 600 ne, wannan kuwa shafi 921 ne; a da, ya ma haura shafi 1,000. Na biyu shi ne a wajen ingancin ɗab'i ya ninka wancan. Na uku, za ka ga duk da yake sunayen mu huɗu duk sun fito, amma suna na ne mafi girman rubutu domin in nuna cewa ni ne na rubuta littafin, to amma na amince da cewa akwai gudunmawar sauran masu binciken a ciki. Kuma ba handame littafin na yi ba, domin ko jiya mun yi waya da Yusuf Albasu cewa za mu kira taron mu huɗu mu zauna mu tattauna kan haƙƙin kowa a littafin. Na biyar, a wannan karon littafin kala biyu ne, wato mai ƙarfin bango da mai laushin bango.

Idan ka shiga cikin littafin, za ka ga shafuka masu kala fiye da na da, da ɗaruruwan hotuna kuma masu faɗi.

To amma babban bambancin shi ne bayanan da littafin ya ƙunsa. Sun fi na farkon yawa, da kuma inganci. A wannan sabon littafin akwai hirarraki da ƙarin wasu mutanen waɗanda Shata ya yi wa waƙa ko ya yi hulɗa da su, akwai tarihe-tarihe na wasu mawaƙan da wasu mutanen. Sannan a littafin farko, akwai kurakurai na wasu bayanan. Misali, ko Jami'ar Ahmadu Bello da za ta ba Shata digiri cewa ta yi mahaifiyar Shata "Fulata-Borno" ce - wato Fulanin da su ka fito daga gabas, su ka zo ƙasar Hausa kafin da bayan Jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Mu ma a littafin farko (da ma na Ƙanƙara ɗin) haka mu ka rubuta. To amma da na je Tofa, garin mahaifiyar Shata, sai na gano cewa ashe ita Babarbara ce, domin mahaifin ta Kanuri ne.
mawa
Sannan a da, ana cewa wani aminin Shata tun su na yara a Musawa, mai suna Malam Ɗanƙane, wai ɗan'uwan Shata ne na jini. Ashe ba haka ba ne, ba su haɗa komai ba sai maƙwabtaka da kuma amintaka. Na yi sabuwar hira da Alhaji Balan Guzun, ɗan'uwan Shata, da shi kan shi Ɗanƙane ɗin, mako uku kafin a buga littafin, inda na gano ashe ba ɗan'uwan su ba ne na jini. Sannan a da ana cewa mahaifiyar Shata ta taɓa yin aure a Ingawa, ashe ba haka ba ne. Kai, ga su nan dai!

Ganin cewa marigayi Shata ya rasu bai ga littafin na farko ba balle wannan, yaya dangantakar ku ta ke da iyalan sa?
Tun farko ina da kyakkyawar dangantaka da iyalin Shata. Farkon mu'amala ta da shi ma, 'ya'yan nasa yawanci ƙanana ne, amma yanzu duk sun girma, sun hayayyafa. Yaran Shata irin su marigayi Alhaji Ya'u Waziri da marigayi Alhaji Bawa Dungun-Mu'azu sun san ni da Shata, don haka kowannen su har gida na ke samun shi mu yi hira. Sannan ina da amini a gidan Shata, wato Alhaji Mustapha Sulaiman Shata, wanda ɗa ne ga mawaƙin, to ya taimaka ƙwarai wajen buɗe mani ƙofofi a farkon fara bincike na.

Bayan rasuwar Shata kuma, sai uwargidan shi, wato marigayiya Hajiya Furera, ta riƙe ni kamar ɗan ta; ko wane irin bayani na nema game da Alhaji, za ta ba ni ko da a waya ne. Akwai kuma kishiyar ta, Hajiya Dije (mahaifiyar Sanusi Shata), ita ma mu na zumunci sosai, kuma har zuwa daf da buga wannan sabon littafin ta taimaka mani sosai. Misali, lokacin da na ke neman wani hoto, sai ta tashi takanas daga Funtuwa ta tafi garin mahaifin ta, wato Falgore, ta kwaso dukkan hotunan ta na rayuwar ta da Shata, ta ba ni. Da yake Hajiya Furera kuma ta rasu, sai ɗan ta, Bishir, wanda ke aiki a Maiduguri, ya bada umurni ga matar sa cewa ta kwaso dukkan hotunan mahaifiyar tasa da ke cikin wani buhu, a ba ni. To ka ga akwai kyakkyawar dangantaka tsakani na da iyalin Shata. Kuma har yau ɗin nan ina kallon kai na a matsayin ɗan'uwan su, tunda ni mai ƙaunar Alhaji ne irin na har abada. Don haka ina matuƙar son ganin cewa rayuwar zuri'ar sa ta inganta ƙwarai da gaske.

Wane irin shiri ka ke yi game da wannan littafi na Shata yadda zai shiga duniya kuma ya zama wata sila na taskace ayyukan mawaƙan Hausa, ban a Shata kaɗai ba?
Shekaru masu yawa da su ka gabata, na taɓa jagorantar wani yunƙuri na kafa wata ƙungiya mai suna Gidauniyar Mamman Shata ko Cibiyar Mawaƙa Da Kaɗe-Kaɗe ta Mamman Shata, ba domin komai ba sai domin a taskace ayyukan da Shata da sauran mawaƙan Hausa su ka yi wajen adana adabin malam Bahaushe. Shugaban ƙungiyar shi ne Alhaji Hamisu Gamarali Funtuwa, ni kuma sakatare. Ƙungiyar ba ta siyasa ba ce, kuma ba ta neman kuɗi ko riba ba ce. Amma tun tashin farko mun samu matsala domin wani kuskure da mu ka tafka. In-sha Allah za mu sake zama domin farfaɗo da ƙungiyar da gyara mata fasali.

Burin ƙungiyar shi ne ta samar da wani gida inda za a riƙa tara dukkan waƙoƙin Hausa, ba na makaɗan zamanin da ba kaɗai, har da na yanzu, irin su Aminu Ala da Mudassir Ƙasim da Fati Nijar da Maryam Fantimoti da Yahaya Makaho da Umar M. Shareef da sauran su, ta yadda duk mai nema zai je ya samu. Na yi la'akari da cewa idan wasu mutane da ke rirriƙe da waƙoƙin su ka shuɗe, to wasu waƙoƙin sun salwanta kenan. A yanzu haka ma akwai waƙoƙin Hausa da su ka ɓata, sai ka sha wuya kafin ka samu wata waƙar.

Wane kira za ka yi ga gwamnati da cibiyoyin ilimi da attajirai da ma al’ummar Hausa gaba ɗaya dangane da Shata?
Kiran da zan yi shi ne su yi ƙoƙari su ga an taskace dukkan ayyukan adabi na Malam Bahaushe. A nan, ba waƙa kaɗai ba, har ma finafinai da littattafai da hotuna da sauran su. Waɗannan abubuwan su ne ke ɗauke da tarihin al'adun mu, waɗanda zamani ke shafewa a hankali. Ba cewa na yi a kafe kan al'ada ba, domin sauyawa ta ke yi, to amma a riƙa adana ta saboda 'yan baya su gani kuma su ji yadda kakannin su su ke a da. Misali, yanzu kayan kiɗan Hausawa da dama sun ɓace; haka abinci da sutura da magunguna. Ko gidan tattara kayan tarihi ka je ba za ka samu wani abin ba. Yanzu ina hoton Narambaɗa? Babu! Hotunan Ɗan'anace guda nawa ka gani? Ba su da yawa! Ko Abubakar Imam hotunan shi guda nawa ake da su? Ba yawa! Shin akwai ma muryar sa a wani faifai kuwa? Ban taɓa ji ba! To, haƙƙi ne da ya rataya a wuyan duk wanda zai iya da ya bayar da tasa gudunmawar don adana irin waɗannan abubuwan. Haka ake yi a duk ƙasashen da su ka ci gaba.

Bayan fitar da wannan babban kundi kan Shata, me kuma al’umma za su tsimaya daga gare ka a nan gaba?
Ina da wasu shirye-shirye na waɗansu abubuwan da na ke so in yi. Idan har Allah ya ara mani tsawon kwana da lafiya da lokaci, za a ji ni na sake fito da wani abin.

Shafin da Aminiya ta fara bugawa na hirar


No comments:

Post a Comment