Showing posts with label carmen mccain. Show all posts
Showing posts with label carmen mccain. Show all posts

Monday, 9 June 2008

Sannu da zuwa, Talatu Danny!

A makon jiya na samu wasikar i-mel daga Malama Talatu Danny, inda ta gaya mani (tare da sauran abokan ta a Nijeriya) cewa ta iso Nijeriya daga Amurka. Talatu ta ce a yanzu ta na hutawa a gidan mahaifin ta a Jos kafin ta fantsama zuwa Kano da sauran garuruwa.

Talatu dai k'awar mu ce 'yar kasar Amurka da ke koyon Hausa da al'adun Hausawa, musamman a bangaren littattafai da finafinai. Ta kan kira kan ta daliba (ko da yake mu a wurin mu malama mu ka dauke ta!) a wata jami'a a Amurka.

Ta na da fitaccen gidan yana a intanet mai sunan ta, inda ta kan bayyana tunanin ta kan al'amura daban-daban da su ka shafi al'adun Afrika kamar yadda ake nuna su a hanyoyin sadarwa na zamani. Ta kan kuma bayyana labarai da tunani a kan rayuwar ita kan ta.

Talatu, ina yi maki barka da zuwa (ko in ce barka da dawowa) Nijeriya. Tare da fatan za ki ji dad'in wannan zaman, kuma ya kasance kin ci moriyar wannan balaguro da ki ka yi.

Lale marhabin!