Friday, 23 March 2007

WANENE MU'AZU HADEJIA? Amsa ga Sheme

Ina da tarihin Malam Mu'azu Hadejia, amma dan takaitacce ne. Na san dai ya rasu yana da Shekara 38, domin acikin 1958 ya rasu. an haifi Malam Mu'azu Hadeja a garin Hadeja, cikin 1920. shine Bahaushe na farko da ya fara rubuta Wakokinsa da rubutun Boko. Wannan kuwa ya faru ne, saboda acikin marubuta mawakan Hausa, shine wanda ya fara samun cikakken illimin boko. Dan gidan Sarautar Hadejia ne, shine dalilin da wakokinsa suka fi maida himma wajen yada akidun NPC a madadin NEPU. Kila wannan ne ya janyo takaddama tsakaninsa da Malam Mudi Spikin. Bayan kammala karatunsa ne, ya fara aikin koyarwa a birnin Kano, har kuma ya rasu aikin da yake yi kenan.

Nayi ta kokarin in san ko ya bar baya, amma har yanzu ban samu abin kamawa ba. Na kuma yi kokarin in san ko yana da iyali a birnin Kano, shi ma dai ban samu abin kamawa ba. Sai dai na ji Shata na yi wa Inuwa Mai mai kirari da "Baban Mu'azu, wanne Mu'azu? Mu'azun Hadeja. Haji Inuwa Baban Yahaya" Na kuwa so hakan ne don ko zan sami wasu wakokinsa da ba'a buga ba. Na ji ya kan yiwa kansa kirari da V T mai neman albarka.

Da fatan wannan zai zama wata kafa ta fadada bincike akan mawakin. Allah ya jikansa ya rahamshe shi, Ya sa Ya huta, mu kuma ya kyauta namu zuwan.

Muhammad Fatuhu Mustapha

No comments:

Post a Comment