Sunday, 10 August 2008

Hiyana: An Yi Suna, An Samu 'Daddy'!

A yau Lahadi aka yi sunan d'an da Maryam Hiyana ta haifa. Majiya mai tushe ta sanar da ni cewa Usman aka rad'a wa yaron, wato sunan mahaifin maijegon. Kun ga kenan labarin da na bayar a makon jiya (cewa an ce Usman za a rad'a masa) ya zama gaskiya.

To, Allah Ya raya, Ya kuma ba uwa lafiyar mama. Shi kuma angon k'arni, Ado Ahmad D'angulla, Allah Ya ba shi ikon rike iyalin sa a mutunce, amin.

1 comment:

  1. thank you for this info. i wish her and the baby the best.

    ReplyDelete