Monday, 11 August 2008

KOTU TA SOKE BELIN IYAN-TAMA

A yau ne kotun majistare da ke hanyar zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, karkashin mai shari'a Muktari Ahmed, ta bayar da dokar a kama shahararren mai kamfanin shirya finafinai, wato Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, bisa laifin rashin zuwa kotu a yau, laifin da kotun ta kira tsallake beli.

Alkalin ya ba da oda an kamo Iyan-Tama, aka mayar da shi gidan kaso, har zuwa ranar da kotun za ta kara sauraron karar, wato ran 20 ga Agusta, 2008, kamar yadda lauya mai gabatar da kara, Barista Sanusi Ma'aji, ya bukata a gaban kotun.

Har ila yau, kotun ta ba da dokar cewa a rubuta wa mutanen da su ka sa hannu wajen belin Iyan-Tama a karon farko, takardar sammaci, domin su zo kotun su bayyana dalilin day a hana shi zuwa kotu, kuma ba tare da wani bayani ba. Wadannan mutane su ne Auwalu Yusuf na unguwar Gadanga da kuma Muhammed da ke zaune a unguwar Sarari a birnin Kano.

An gurfanar da Iyan-Tama a gaban kotun ne cikin Mayu bisa tuhumar da Hukumar Tace Finafinai ta ke yi masa na sakin wani fim mai suna 'Tsintsiya' wanda kamfanin sa na Iyan-Tama Multimedia ya shirya, wanda kuma ake tuhumar cewa ya sake shi ne ba tare da hukumar ta tace shi ba.

Haka kuma kotun ta tuhumi Iyan-Tama da laifin mallaka tare da tafiyar da kamfanin shirya finafinai wanda ba shi da rajista da hukumar.

A halin yanzu, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama na tsare a gidan kaso har zuwa lokacin da kotun za ta kara zama a ranar 20 ga Agusta 2008.

No comments:

Post a Comment