Daga Ibrahim Sheme
(An buga wannan sharhin a filin Adabi na jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'a ta makon jiya)
Kwanan nan aka yi wani }asaitaccen biki na karrama marubutan Hausa uku wa]anda su ka yi zarra a gasar rubuta littattafan hikaya na Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Mohammed Bashir {araye, wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kano. Mai]akin marigayin, Hajiya Bilkisu Abdulmalik Bashir, wadda ita ce Sakataren Zartaswa ta Hukumar Aikin Shari’a ta {asa (Executive Secretary, National Judicial Service Council), ita ce ta ]auki nauyin shirya gasar. {ungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA), reshen Babban Birnin Tarayya, Abuja,ita ce ta gudanar da bikin. A tarihin adabin Hausa, ba a ta~a yin gagarumin bikin karrama marubuta irin wannan ba. Taron da za a iya kwatanta shi da wannan shi ne wanda aka yi a kamfanin buga littattafai na Gaskiya Corporation da ke Zariya lokacin da aka }addamar da sabon bugu na wasu daga cikin littattafan Alhaji Abubakar Imam, cikin 1981, wanda ba a da]e da yin taron ba Allah ya ]auki ran shi Alhaji Imam. To amma ko wancan taron na Zariya bai ko kama }afar wannan ba wajen bun}asa da alfarma. Abin sai wanda ya gani!
Wani abu da ya ba mutane da dama mamaki game da wannan gasa shi ne yanayin su wa]anda su ka shirya gasar. Irin abin nan ne da ake cewa ana zaton wuta a ma}era, sai ta tashi a masa}a. Na farko, mutumin da ya fara kawo shawarar shirya gasar, ba Bahaushe ba ne. Inyamiri ne mai suna Mista Patrick Tagbo Ogujiofor. Ma’aikaci ne a wannan hukuma ta aikin shari’a, inda shi ne jami’in ya]a labarai. A bayanin da ya yi a jarida kwanan baya, Ogujiofor ya ce tunanin shirya gasar ta faru ne a bara, lokacin da su ka je ta’aziyyar rasuwar Injiniya Bashir {araye. A lokacin, uwar]akin sa Hajiya Bilkisu ta ]an furta cewa mijin ta mai }aunar karance-karancen littattafan Hausa ne da kuma son ha~aka adabi. Wannan abu ne wanda kusan dukkan masu ruwa da tsaki a harkar adabin Hausa ba su sani ba, domin kuwa yawancin su ba su yi mu’amala da shi Injiniyan ba.
To, inda kaya su ka tsinke a gindin kaba shi ne, shi Patrick wani }usa ne a harkar rubuce-rubuce, amma fa da Turanci. Ya ta~a ri}e mu}amin shugaban }ungiyar ANA ta Jihar Yobe, lokacin ya na aiki a can. Mutum ne mai son al’amuran Hausa, kuma ya na jin Hausa kamar jakin Kano. Kai, matar sa ma Bahaushiya ce!
Saboda haka sai ya ba wa Hajiya shawarar cewa ya kamata ta shirya wani abu wanda zai sa a ri}a tunawa da marigayin. Nan take sai ta amince da hakan. Su ka tsara cewa a shirya gasar rubutu ga marubutan Hausa. Wani abu da zai ba ka mamaki kuma shi ne, ita kan ta Hajiya Bilkisun ba Bahaushiya ba ce. ’Yar }abilar Igbirra ce daga Jihar Kogi. Amma wannan bai hana ta amincewa ta ]auki nauyin shirya gasar ba.
Patrick kuma memba ne a }ungiyar ANA ta Abuja. Sai ya shigo da }ungiyar cikin al’amarin, inda shi da shugaban }ungiyar, wato Dakta Emman Usman Shehu, su ka shiga fafutikar shirya gasar. Ina jin in ban da shi Emman Shehu da kuma wani lauya Bazazzagi, marubuci, mai suna Ahmed Maiwada, babu Bahaushe a }ungiyar. Wa]annan bayin Allah sun yi aiki tu}uru wajen shirya wannan gasa har Allah ya sa aka yi ta aka gama lafiya.
Na ba ku wannan dogon tarihin ne don ku fahimci cewa ba Hausawa ka]ai ba ne su ke da kishin ci-gaban adabin Hausa. Za ma mu iya cewa su Hausawan, musamman Musulmin cikin su, ba su damu sosai da ci-gaban al’adun su ba; sau da yawa su kan bari wasu can su shirya musu hanyoyin ha~aka al’adun su, musamman a fannin rubutu.
Ga hujja. Gasar rubutu ta farko da aka shirya, a cikin 1933, wani Bature ne jigon yin ta. Baturen, Mista Rupert M. East, jami’in ilmi ne a Zariya. Shi Turawan mulkin mallaka su ka ]ora a kan aikin. A wannan gasar ne aka samu marubuta zufin farko, irin su Abubakar Imam, Abubakar Tafawa-|alewa, Bello Kagara, Muhammadu Gwarzo da John Tafida Wusasa. Haka kuma gasar da aka yi a cikin 1982, Garba Asiwaju Malumfashi ne jagoran shirya ta. Bahaushe ne, to amma fa Kirista. Ya shirya gasar a matsayin sa na daraktan al’adu a Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya, ba domin addini ba, sai don ha~aka adabin Hausa. A gasar ne aka samu marubuta irin su Sulaiman Ibrahim Katsina da Bature Gagare.
Ita kan ta wannan gasar da aka yi a bana, yawancin masu shirya ta ba Musulmi ba ne; ina nufin su Patrick, Emman Shehu da Ahmed Maiwada. Biyun }arshe Hausawa ne, to amma ba Musulmi ba ne. Sun shirya gasar ne ba tare da sun sa tunanin addini a ran su ba, a’a sai don su ga yadda za a yi a inganta adabin Hausa, tare da ma}udan ku]in da Hajiya Bilkisu ta bayar.
Shin ina Hausawa su ke? Ina Musulmi? Wa]annan tambayoyin su na daga cikin wa]anda ni da Farfesa Abdalla Uba Adamu, ]aya daga cikin al}alan da su ka yi hukunci kan wannan gasa ta Injiniya Bashir {araye, mu ka yi wa kan mu ita lokacin da shi Malam Abdalla ya zo Abuja don halartar taron karrama marubutan da su ka yi zarra a gasar. Gaskiyar magana ita ce, Hausawa Musulmi ba su damu da ha~aka al’adun su ba, musamman ma dai a wannan zamanin. Ba su ]auki rubutu da wani muhimmanci ba.
Sau da yawa, Hausawa Musulmi so su ke a ma daina rubutun. Kamar yadda Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, ]aya daga cikin zakarun gasar Injiniya {araye, ta fa]a a hirar ta da aka buga a jaridar Leadership Hausa a makon jiya, a Kano an da]e ana }o}arin dur}usar da rubutun hikaya na Hausa na wannan zamanin. An yi tsinuwa da zage-zage a masallatai; an ce marubuta ne manyan masu gur~ata tarbiyya a }asar Hausa. Kuma abin sai }ara gur~acewa ya ke yi. Misalin hakan shi ne yadda kwanan baya Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano ta shirya gangamin }ona littattafan Hausa, inda har Sarkin Kano sai da ya halarta kuma ya jagoranci cinna wa tarin littattafan wuta.
Kwanan nan kuma Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta fito da wata doka mai ban-dariya da takaici, inda ta ce tilas ne duk littafin da za a buga a Jihar Kano sai an kai mata shi ta karanta ta amince tukuna, bayan kuwa ga shi ba ta da masana masu lokacin yin wannan aiki. A kaikaice, manufar dokar ita ce ta hana yin rubutun kwata-kwata.
Wani abin juyayi shi ne, yawancin masu sukar littattafan hikaya na Hausa ba masu karanta su ba ne. Ba su san abin da ke cikin littattafan ba. Su a ]an }aramin tunanin su, babu abin da ke cikin littattafan sai labaran soyayya, sharholiya, batsa, zinace-zinace, shan muggan }wayoyi, da sauran su. Kawai idan an samu littafi }waya ]aya mai ]auke da wani abu wanda bai yi musu da]i ba, ko wata she]ara a cikin wani littafi, shikenan an samu makamin farfaganda, a shiga kafafen ya]a labarai ana kumfar baki. Ba za a fa]i dalilin yin littafin da aka yi ba (misali, idan an ga batsa a wata she]ara, a ce an yi ta ne don ta dace da muhallin ta). Kuma ba za a ta~a yin nuni da duk wani littafi mai ]auke da irin koyarwar da su masu sukar su ke so a yi ba. Ba za su ba da misali da littattafan da su ka dace da tunanin su ba, a’a sai dai wannan }waya ]ayan. Ka ga kenan ana yin al}alanci cikin jahilci. Hakika, na san wani al}alancin ana yin sa ne da gangan don a shafa wa marubuta kashin kaji.
Sannan kuma su masu sukar, daga hukumomi zuwa ]ai]aikun mutane, ba su yin komai don agaza wa marubutan. Ba su shirya taron wayar da kai, ba su yin wa’azantarwa, ba su ba da tagomashi na ku]i, ba su shirya gasar rubutu su gindaya }a’idojin da su ke so, kuma ba su sayen littattafan. Hukumar A Daidaita Sahu ta alamta yun}urin agaza wa marubutan, to amma abin da ta yi kamar ka ]iga ruwa ne a hamadar rairayi. Wani rufin-]uwan-’yan-bori (an rufe gaba, ba a rufe baya ba) kuma da hukumar ta yi shi ne gangamin }ona littattafan marubuta da ta yi, wa]anda kamata ya yi ta ja su a jika, ta saka su kan hanyar da ta ga ya dace.
Abin mamaki, akwai daga cikin masu nazari da marubuta wa]anda ke yin furutan da ke }ara iza wutar }yama ga marubutan. A marubuta, akwai }yashi da hassada da kuma tunanin in-ba-ni-ba-to-ba-wanda-ya-iya. Idan ka dubi surutan da ake yi wa juna a tsakanin }ungiyoyin marubuta na Kano, to ka san lallai da sauran aiki.
Sannan manazarta/masana irin su Malam Ibrahim Malumfashi (wanda ke kan hanyar zama cikakken farfesa a fagen adabi) sun yi ayyukan da ke tabbatar da cewa manufar su ba ta kawo gyara ba ce; kawai su na yin sukar neman suna su ke yi, ba tare da sun kawo tabbatattun hujjoji na sukar da su ke yi ba. Haka kuma abin ba}in ciki shi ne, duk da yake wai a jami’a su ke, su ma a tsakanin su akwai }yashi da hassada irin ta malaman zaure. Babu shakka, Malumfashi shi ne kan gaba wajen ~ata sunan marubutan Hausa na wannan zamani; da gangan ya }i yarda ya fito rana a gan shi, ya la~e cikin duhun tarihi, ya na bautar shu]a]]un gumaka. Idan wani al’amari ya taso na yadda za a yi a inganta adabin Hausa, to ba ya ciki.
Babu wata }asa mamallakiyar babban harshe da ya kai gawurtar harshen Hausa inda tsirarun manazarta da ’yan kazagin su masu }aramin ilmi su ke farfagandar jawo koma-baya a fagen adabi kamar }asar Hausa. Sai dai abin mamaki, da yake sukar adabi ba ta hana adabi ya]o, har yanzu rubutun ake. Ya }i mutuwa ballantana a yi jana’izar sa. Masu jiran ganin kushewar sa sun ha}a kabari mai zurfi, su na ri}e da farin alawayyon yi masa likkafani, to amma akwai alamun cewa har su mutu shi adabin Hausar ba zai mutu ba. Wannan kabarin da su ka ha}a, su za a rufe a ciki.
No comments:
Post a Comment