Monday, 9 June 2008

Sannu da zuwa, Talatu Danny!

A makon jiya na samu wasikar i-mel daga Malama Talatu Danny, inda ta gaya mani (tare da sauran abokan ta a Nijeriya) cewa ta iso Nijeriya daga Amurka. Talatu ta ce a yanzu ta na hutawa a gidan mahaifin ta a Jos kafin ta fantsama zuwa Kano da sauran garuruwa.

Talatu dai k'awar mu ce 'yar kasar Amurka da ke koyon Hausa da al'adun Hausawa, musamman a bangaren littattafai da finafinai. Ta kan kira kan ta daliba (ko da yake mu a wurin mu malama mu ka dauke ta!) a wata jami'a a Amurka.

Ta na da fitaccen gidan yana a intanet mai sunan ta, inda ta kan bayyana tunanin ta kan al'amura daban-daban da su ka shafi al'adun Afrika kamar yadda ake nuna su a hanyoyin sadarwa na zamani. Ta kan kuma bayyana labarai da tunani a kan rayuwar ita kan ta.

Talatu, ina yi maki barka da zuwa (ko in ce barka da dawowa) Nijeriya. Tare da fatan za ki ji dad'in wannan zaman, kuma ya kasance kin ci moriyar wannan balaguro da ki ka yi.

Lale marhabin!

3 comments:

Anonymous said...

Lale! Na gode kwarai da gaske. Ina jin dad'i in dawo Nijeriya, kuma ina yin alla alla in koma Kano sati mai zuwa. Sai mun hadu. Na gode!

Anonymous said...

Nima ina yi miki barka da dawowa gida najeriya!hakika kin amfana da karin maganar bahaushe da yake cewa 'kowa ya bar gida, gida ya barshi'ina miki fatan jin dadin wannan ziyara taki da kuma fatan samun cikakken bayanin abin da zamu karu dashi daga ziyarar taki.za a iya aiko min da karin bayanin darasin da aka karanta a wannan ziyara akan adireshi na kamar haka:sainsuleiman@yahoo.com.Nagode

Anonymous said...

cheap wow power leveling buy wow gold cheapest wow power leveling CHEAP wow gold BUY power leveling CHEAPEST wow powerleveling
wow goldwow goldwow goldwow goldweiwei