Sunday, 5 October 2008

GASAR RUBUTU DON TUNAWA DA BASHIR KARAYE

Malamai,

Tare da sallama. Ga wata gajeriyar sanarwa kan bikin gasar rubutun Hausa don tunawa da marigayi Injiniya Bashir Karaye, kashi na biyu.

Za a yi bikin fidda gwani na gasar ta bana a ranar 22 ga wannan watan na Oktoba, 2008a birnin tarayya, Abuja.

Majiya ta shaida mani cewa kwanan nan za a bayyana sunayen zakaru uku da su ka kai matakin karshe a gasar inda daga cikin su za a fidda gwani na gwanaye da bi masa/mata da kuma na uku.

Idan kun tuna, a bara, gogan naku ne ya zo na daya da littafin sa mai suna "'Yartsana," yayin da Balaraba Ramat Yakubu ta zo ta biyu, sannan Maje El-Hajeej Hotoro ya zo na uku.

Majiyar ta kara shaida mani cewa Dakta Ibrahim Malumfashi na Jami'ar Usmanu Danfodio shi ne Alkalin Alkalan gasar ta bana, wadda ita ma littattafan hikaya ne su ka shiga.

Idan ba a mance ba, maidakin marigayi Injiniya Karaye, wato Mrs Bilkisu A. Bashir, ita ce ta dauki nauyin gudanar da gasar.

Duk littafin da ya zo na daya za a ba shi N150,000; na biyu kuma N100,000, sannan na uku N50,000.

To, Allah Ya ba mai rabo sa'a.

To, kaka tsara kaka!! In ta bi ta daga-daga, na kurya ka sha kashi! Allah Ya nuna mana ranar, amin.

No comments: