Wednesday, 8 December 2010

Tsugunne ba ta kare ba

Akwai alamun cewa sau}i ya fara zuwa masana’antar finafinai ta Nijeriya, wato Nollywood, domin kuwa mako uku da su ka wuce ne Shugaban {asa Goodluck Jonathan ya yi wani ho~~asa na kyautatawa ga masu aikin fasaha da basira na }asar nan. Ku]i ne zunzurutu wuri na gugar wuri har dalar Amurka miliyan 200 ya bayyana bayarwa ga masu sana’ar nisha]antarwa a matsayin rance don ha~aka sana’ar su. A ku]in Nijeriya, sun kama kimanin naira biliyan 30.

Shugaban }asar ya fa]i haka ne a Legas, a wurin bikin cikar shahararren kamfanin nan masu gidajen silima da shirya gasar sarauniyar kyau mai suna Silverbird Group shekara 30 da kafawa. Mamallakin kamfanin, wato tsohon Darakta-Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Mista Ben Murray-Bruce, shi ne ya ro}i shugaban da ya yi wani abu don karrama masana’antar, wadda ta }unshi masu shirya fim da kuma mawa}a. Jonathan, wanda ya halarci taron da kan sa, ya ce wannan jari da gwamnati ta zuba an yi shi ne “ba don komai ba sai don a mara wa masu sana’ar fasaha baya da kuma ha~aka masana’antar mu ta nisha]antarwa.”

Mutane da yawa da ke da ruwa da tsaki a masana’antar sun yi murna da wannan ku]in, su na ganin su a matsayin agajin da ya zo a daidai lokacin da ake bu}atar sa, wato a daidai lokacin da ruwa ya kusa }are wa ]an kada. Su na ganin sa a matsayin wata babbar karramawa da amintaka ga gudunmawar da wa]annan ]imbin masu basirar su ka bayar wajen sa a }ara sanin Nijeriya a fagen ayyukan nisha]i, wato fim da wa}a.

Nollywood, wadda masana’anta ce da ke bun}asa a koyaushe, ta na tafiya kafa]a-da-kafa]a da masana’antar da ta girme ta a fagen, wato ta ki]a da wa}a. Duk an san su a duniya. A wani rahoto da hukumar UNESCO ta buga a cikin watan Mayu 2009, an bayyana cewa masana'antar Nollywood ce ta uku a duniya wajen fito da yawan finafinai, wato ta na bin masana’antar Hollywood ta }asashen Turawa da kuma Bollywood ta }asar Indiya. An }iyasta cewa darajar Nollywood ta fuskar ku]i ta kai kimanin dala miliyan 250, kuma akwai mutum a}alla miliyan ]aya da ke aiki a masana’antar. Wannan masana’anta ta haifar da ’yan wasa wa]anda sunan su ya zama ruwan dare a cikin }asar nan da }asashen waje. Sunaye irin su Genevieve Nnaji, Omotola Jalade-Ekeinde, Ramsey Nouah, Kate Henshaw-Nuttal, Pete Edochie, Ali Nuhu, Segun Arinze, Funke Akindele, da sauran su, sanannu ne. Akwai kuma irin wa]annan sunayen a fagen wa}a. A dalilin haka, akwai manazarta da dama da ke tururuwa daga }asashen duniya su na zuwa nan domin yin nazarin irin tashin gwauron zabon da wannan masana’anta ke yi. Abu sai ka ce tsafi! A yau ]in nan akwai tashoshin talabijin na satalayit da dama da ke nuna finafinan Nollywood dare da rana, ciki kuwa har da shahararriyar tashar Africa Magic, kwatankwacin yadda tashar Fox Movies ke nuna finafinan Hollywood da kuma yadda tashoshin B4U da Zee Aflam ke nuna na Indiya. Wa]annan mutane, mazan su da matan su, wa]anda yawanci matasa ne, su na rayuwa cikin jin da]i a matsayin attajirai, a cikin aikin da su ka }ir}ira da kan su, ba tare da sa hannun hukuma ba.

To amma kuma akwai mutanen da ke kallon wannan gara~asa da Jonathan ya yi ga ’yan fim da mawa}a a matsayin wani abu bambara}wai. Su na ganin cewa ya yi abin ne da ka kawai, ba tare da ya numfasa ya yi tunani ba, don kawai Mista Murray-Bruce ya ro}e shi da ya yi masu ko ma menene don nuna kulawa. Tun daga lokacin da aka bayyana gara~asar, na ji 'yan fim da mawa}a da dama su na yin wasu tambayoyi a kan ta: Shin wannan kyautar yaudara ce ko kuwa? Shin siyasa ce? Shin Jonathan ya na }o}arin samun goyon bayan masu sana’ar nisha]antarwa a daidai lokacin da ’yan adawa ke girgiza kujerar sa? Shin kishin }asa ne ya sa ya ba da wannan babbar kyautar? Ko kuwa ma gwamnati ta na so ta yi wa ’yan fim da mawa}a }ofar raggo ne, wato ta biyo ta bayan fage domin ta mamaye harkar saboda gudun irin sa}wannin da ake iya jefawa a cikin finafinai da wa}o}i?

Bayan haka, wa zai kar~o ku]in daga hannun gwamnati a madadin ’yan fim da mawa}an, wa]anda ba su da wasu tsayayyun shugabanni da kowa da kowa ya yarda da su? A yanzu dai, ba a ma san yadda za a raba ku]in ba. Shugaban }asa dai ya ce gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) tare da ministan ku]i su ne za su je su fito da hanyar da za a bi a fito da ku]in da kuma yadda za a yi da su. Jonathan, a jawabin sa, ya ambaci kalmar Nollywood ne a matsayin masana’antar finafinan Nijeriya, to amma don Allah ainihi su wanene Nollywood ]in? Da yawa in an ce Nollywood, to ana nufin ’yan fim na Kudiu kenan, wa]anda ke zaune a Legas da Anacha. To su kuma ’yan fim na Hausa fa da ke Arewa, wa]anda sunan tasu masana’antar Kannywood? Sannan kuma ina sauran Wood Wood da ke akwai - misali masana’antar finafinai ta Nupawa, wadda }arama ce kuma ba ta kallon kan ta a matsayin wani yanki na Kannywood, da sauran wuraren da ake shirya fim cikin harsunan mu na gado? Su yaya za a yi da su? Bugu da }ari, me ake nufi idan an ce maka]an Nijeriya? Shin sun ha]a da masu wa}o}i da harsunan gargajiya, irin su Nasiru Garba Supa na Kano da Musa [anbade na Kaduna, ko kuma ana nufin mawa}a na zamani masu wa}o}in Naija irin su Dapo Oyebanjo (D’banj), Abolere Akande (9ice), Innocent Idibia (Tuface), 2-Effects da Sound Sultan? Sannan ina za a saka su Aminu Ala, Fati Nijar, Maryam A. Baba da ire-iren su? A gaskiya, akwai bu}atar a fito a yi wa jama’a bayani, kuma a fito da hanyoyin da za a bi wa]annan ku]in su kai ga ’yan fim da mawa}a. Idan har ba a bi a sannu ba, to wannan gara~asa ta gwamnati za ta haifar da babban rikicin shugabanci a industiri, ta jawo rarrabuwar kai tsakanin masu fasaha a ~angarori daban-daban.

Ni a nawa ganin, har yanzu tsugunne ba ta }are ba ga masu shirya finafinai da kuma buga wa}o}i a Nijeriya. Industiri ba ta bu}atar wa]annan ku]in. Dalili: an yanke shawarar ba da su ne kurum a cikin irin tunanin gwamnati da ya da]e ya na addabar }asar nan, wato inda za ka ga an watsa ku]i ga matsala a matsayin magani maimakon a gano dalilin faruwar cutar. Abin da masana’antar nisha]antarwa ke bu}ata shi ne a samar da kyakkyawan sararin da mutum zai yi sana’a har ya ci riba. Mu tuna, wasu ’yan kasuwa masu tarar aradu don fa]in kai ne su ka haifar da industirin Nollywood da rana tsaka kimanin shekara 18 da ta gabata lokacin da su ka fitar da fim mai suna Living in Bondage, kuma tun daga lokacin ta ke ta }ara bun}asa ba tare da jarin gwamnati ba. Na san cewa masana'antar ta na fama da manyan matsaloli. Na farko, matsalar da ke damun Nijeriya ma ita ke damun ta, domin abin da ya ci Doma ba ya barin Awai. Matsalolin sun ha]a da satar basira da wasu ~arayin zaune ke tafkawa, ga rashin tsaro da kuma ta~ar~arewar tattalin arzikin }asar nan. [aya daga cikin manyan matsalolin ita ce satar basira, inda wani zaunannen ~arawo zai ]auki kayan ka ya gurza ya ri}a sayarwa, kai kuwa ko oho. Rashin }arfin doka da oda ya sa masu aikin basira sun kasa cin moriyar shukar su. |arayin zaune sun yi masu talala. Ya kamata a fitar da su daga wannan }angin, su samu sa’ida.

Lokacin da hukumar UNESCO ta ce Nollywood ce ta uku a duniya, ta ba ta wannan matsayin ne a kan yawan finafinan da ake shiryawa kawai, ba wai saboda }arfin arziki ko kuma ingancin finafinan ba. Su finafinan mu na Nijeriya, ana shirya su ne bisa ku]i }alilan, tare da yin amfani da kayan aiki masu araha. Yawanci babu ilimin abin domin su masu ruwa da tsakin ba wani horo su ka samu a makaranta ba; duk a lokeshin ake koyon komai. Shi ya sa za ka ga a finafinan ana nuno abu a duk yadda aka ga dama. Idan ka na kallon finafinan Kudu, sai ka yi tunanin cewa a }asar mu ba abin da ake yi sai tsafe-tsafe da aikata laifuffuka da kuma tsiraici. Rashin doka mai }arfi da kuma han}oron samun }azamar riba sun sa lamarin ya }azanta. Don haka babu mamaki, finafinan Nollowood }alilan ne ake ]aukar su da wata daraja a }asashen da su ka ci gaba, in ban da a unguwannin da ’yan Nijeriya ke zaune, masu }awazucin tunowa da gida. Yanzu dubi wani fim da aka yi a Afrika ta Kudu wai shi Tsotsi, da wani da aka yi a Indiya mai suna Slumdog Millionaire. Wa]annan finafinai ne da ake ji da su a duniya. Shi Tsotsi, dalar Amurka miliyan 3 aka kashe wajen shirya shi, to amma an samu dala miliyan 10 daga nuna shi a silima. Haka kuma ya ci manyan gasa guda biyu na duniya, wato lambar Oscar (a cikin 2005) da lambar Golden Globe (a 2006) a matsayin gwarzon fim cikin harsunan }asashe ban da Ingilishi.

Amma mu finafinan mu na Nijeriya, ba su da labarai masu }arfi, sannan da an fara fim za ka iya cankar inda zai }are. Sakamakon haka, za ka ji ana kuka da finafinan a gida da waje. Yanzu haka a Uganda har wata mata ’yar Majalisar Dokokin }asar mai suna Sarah Wasike Mwebaza ta ]ora laifin }aruwar ayyukan tsafe-tsafe a }asar ga yawaitar finafinan Nijeriya a }asar. Gwamnatin Uganda ta na nan ta na shirin kafa dokar da za ta magance matsalar. Wannan ya nuna cewa ya kamata masu shirya finafinan mu su yi karatun ta-natsu, su maida hankali wajen shirya finafinai masu inganci, da nuna gwaninta wajen ba da labari, da kyan hoto da sauti. Ya kamata su nuna wa sauran }asashen duniya cewa ba wai neman ku]i kawai ya sa su ke shirya fim ba, a’a har ma don su nuna bajinta a basira da fasaha. Saboda haka, kada a dubi gara~asar da Shugaba Jonathan ya bayar a matsayin ku]i kawai, maimakon haka a ]auka cewa alama ce ta nuna goyon baya da kuma karramawa. Idan har aka saka ido a kan ku]in, to ba abin da zai biyo baya sai cacar baki da rarrabuwar kai da fa]ace-fa]ace, daga nan kuma zancen bizines ya }are kenan.

No comments: