Baitikan da na fi so a waƙoƙin Alhaji Sani Sabulu Kanoma su na cikin waƙar sa ta "Taimaka Rabbana". Ga su na zauna na rubuta su kamar haka:
In ka na yawo cikin duniya,
Kag ga abin mamaki bai kamar ƙarewa,
Sai kullum ƙaruwa za ya yi.
Sai ka samu mutum cikakken mutum,
Ka iske mutum kamak kamili,
Hannu na mutum, idanun mutum,
In ka koma cikin zuciya tasa sai ka ga ƙwamma kura da shi!
Ka san sha'anin duniya wuya ce garai,
In an ka iya shi daɗi garai.
In kay yi kure, akwai 'yaw wuya.
Ya ikon Allah, ka tserad da mu ka hana mu faɗa ka ganar da mu gaskiya.
Taimaka Rabbana, ya Jallah ka ceci 'yan zamani.
Ka san sha'anin duniyag ga sai Rabbana.
Ka san sha'anin duniya wuya ag garai,
In ka ga mutum ka na ra'ayi nai malam,
Kafin ku zam jiki kai da shi, na so ka yi bincike nai kaɗan,
Ka bar dubin fuska da kaurin jiki,
Na so ka yi binciken zuciya da irin halin da duk ag garai.
Ka san cinikin ɗan'adam wuya ag garai,
Ko an bar ma sule goma nan a cikin naira rage sule biyar,
Watakila ka na zaton faɗuwa.
Ka san hikima - eh?
Sha'anin duniya wuya ag garai.
Amma inji mai waƙa uban Zainaba, Sani,
Amma inji mai waƙa uban A'isha, Sani.
Sha'anin duniya wuya ag garai,
Sannan cinikin ɗan'adam wuya ag garai,
In an ka biyo ana bincike, ka je ka hwaɗi garan an ka ji.
Taimaka Rabbana, ya Jallah ka ceci 'yan zamani.
Ya ikon Allah, ka tserad da mu ka hana mu faɗa ka ganar da mu gaskiya.
Ka san sha'anin duniyag ga sai Rabbana.
Ka samu mutum cikakken mutum,
Hannu na mutum, idanun mutum, a'ah!
Daidai ya yi godiyar Rabbana, sai ka iske ana ta'asa da shi.
Allah ya yi ma jiki na mutum,
Kuma yai maka lafiya ta mutum,
Daidai ka yi godiyar Rabbana, sai ka iske ana ta'adi da kai.
Ka san sha'anin duniyag ga sai Rabbana.
Ka samu mutum kamar kamili,
Ka iske mutum cikakken mutum, (2x)
Ga riga, cikin rawani,
Da ka koma cikin zuciya tasa sai ka ga ƙwamma kura da shi!
Ka san sha'anin duniyag ga sai Rabbana. (2x)
3 comments:
Barka da kokari rankaidade Allah Ya kara kwakwalwa da basira
Dan Allah ta ina xanyi downloading wannan waqar?
Inasob naayi downloading din wakan me
Post a Comment