Wannan rubutun da ke kasa ba nawa ba ne, na Aliyu Ibrahim Kankara ne. Shi ya wallafa abin sa a turakar sa mai suna Taskar Mamman Shata a ranar Alhamis, 16 ga Satumba, 2010 (wato shekara takwas da su ka gabata). A ciki, ya yi bayani kan taron kaddamar da littafin mu na "Shata Ikon Allah!" a cikin shekarar 2006. A cikin 'yan kwanakin nan, Kankara ya wallafa zargin cewa wai ni, Ibrahim Sheme, ni ne na cinye kudin taron kaddamar da littafin Shata wanda aka yi a 2006.
Ban yi karambanin yin editin din wannan rubutun nasa ba, don haka duk yadda aka gan shi haka ya rubuta kuma ya gabatar da kayan sa. In da hali ma, ya kamata mai karatu ya ziyarci turakar ta Dr Kankara, ya gane wa idon sa. Adireshin shi ne:
http://taskarmammanshata.blogspot.com/2010/09/budaddiyar-wasika-zuwa-ga-dokta-mamman.html
BUDADDIYAR WASIKA: Zuwa Ga Dokta Mamman Shata
Daga Aliyu Ibrahim Kankara
Ranka shi dade Yallabai,
Ban yi niyyar rubuta maka wannan ‘yar guntuwar takarda ba,ban kuma yi
niyyar rubuta ta da wata manufa don birgewa ko don in matsa maka a inda
kake kwance ba, a’a Allah shi baka nasara tun lokacin da muka zanta da
kai ranar asabar 19/9/1998 akan wallafawa da kaddamar da littafinka
tun a sannan ka ga irin kokarinmu da kishin mu na ganin mun tallata
abubuwan da ka yi a rayuwar ka.Littafi dai bai kammala ba sai bayan da
ka bar wannan sararin.
Kai kanka ka yi kokarin ganin littafin ya fito da wuri sai dai kash,a
sannan rashin lafiya ta addabeka,wanda qarshe Allah bai yi zaka ga
kaddamar da littafin ba. To, an qaddamar da littafi ranar asabar
7/8/2006 amma kusan ba’a taru ba a yanda ya kamata. Cikin aminanka da
basu da adadi ina iya kirga maka waxanda suka halarci wurin:daga Sa’in
Katsina Amadu Na Funtuwa sai Ammani Inuwa Fage Kano, sai Umaru xan Duna
na Gwandu(direba) sai Alhaji Hassan Hadi da marigayi Dan Tireda Ali
Gombe sai Hakiman Funtuwa(sarkin Maska Mainasara Idris kenan) da Musawa
sai Alhaji Adamu Yusuf BBC marigayi. Ni kaina na tafi da Hajiya Maimuna
Mairo Munari daga Funtuwa. A wurin, naga wasu da ban iya tantancewa ko
kunyi alaqa tare ko a’a ba, kamar su ritaya Kanar Bello Kaliyal(tsohon
Gwamnan Bauchi) da Janar Garba Duba(ko da yake shi aiko shi akayi ba
zuwan kanshi ba ne), na kuma ga Musa Gwadabe(tsohon ministan ma’adinai)
da shugaban Jami’ar Bayero, farfesa Attahiru Jega. Shi ASD(Alhaji Sani
Dauda) ba’a ma gayyace shi ba a rediyo yaji ana shirin ya tashi ya je ya
kuma bada naira dubu 100 saboda kaunar ka.Sarkin Zazzau ma ya aika da
naira dubu 250 duk sabili da son ka.A nan mutane da dama masu qaunar
tsakani da Allah sun je wurin da ban ma yi tsammanin za su je ba.
Amma duk ‘yan siyasar nan da sarakuna da manyan sojoji da masu hali da
ka wake duk basu je ba,alhali mun taka har gidajensu mun kai masu
katunan gayyata.
Sannan an kaddamar da littafi amma duk alkawurran da masu kaddamarwa
suka yi basu bamu kudaden ba. Ga dai jerin sunayen wadanda muka biyo
bashi na littatafan da suka kwasa:
1.Alhaji Sama’ila Isa Funtuwa(shine ma babban mai kaddamarwa)= naira
2,000,000.
2.Janar Ibrahim Badamasi Babangida =naira 1,000,000.
3.Gwamnatin Jihar Gombe =naira 250,000
4.Alhaji Dahiru Barau Mangal= naira 250,000
5.Alhaji AY Gombe= naira 100,000.
6.Alhaji Muntari Dandutse(shugaban karamar Hukumar Funtuwa)=naira
150,000
7.Alhaji Maitama Sule Danmasanin Kano= naira 100,000
8.Alhaji Sahabi Liman Kaura ya bamu ceki na kudi mun je Banki ba
kudin=naira 50,000
Dokta Aliyu Modibbo shi ya biya kudi kaka buga littafin ya kuma buga
katin gayyata ya kuma kama mana hayar wurin bukin, shi kuma ya jagoranci
nemo masu kaddamarwa.Shima din ya taba kiran mu Abuja don mu amso kudin
karshe bamu samu dammar ganin sa ba.Munje ga Alhaji Sama’ila Isa sai
yace mu je mu samu Modibbo.Muka sake komawa Modibbo ba halin mu
ganshi,don alokacin ministan Ciniki ne bashi ganuwa.Muka gaji da
gararanba cikin Abuja kamar shegu marasa galihu muka dawo gida.Saima
asarar kudi har dubu 14 da nayi.Na shiga mota na neme sun a rasa.Kaga
garin nemo qiba na rame a Abuja.
A waje daya ga wasu ‘ya’yan ka mazan suna ta azalzalarmu cewa mu basu
kudi,sun dauka ko dai munyi sakacin qin amso masu kudin ko kuma mun amsa
mun kashe.
Yau shekara uku kenan ba wata magana ba alamar kudin za su fito, mu kuma
wallafe-wallafen da muke yi da hirarrakin da mu keyi a rediyo na
bayyanawa duniya wanene Shata bamu fasa ba, ba za kuma mu fasa ba.
Ka duba kaga irin yanda ka sadaukar da rayuwar ka ka taimaka wa
jama’a:ka yi hanya an ba wasu sarautu,ka yi hanya an ba wasu mukamai a
gwamnati,arzikin wasu yak are ka taimaka masu,wasu sun rasa muqaman su
ka taimakesu an mayar masu,wasu kuma ka basu kudi da abinci saboda
tausaya masu.Amma yau gashi saboda an ga ba ka a duniya kowa ya watsar
da hidimarka da abinda ya shafe ka. Yanzu an yi maka adalci kenan?
Alhali kai da kana raye na tare da kai har tausayink a suke,don in ka
xauko kudi da dukiya kana badawa kamar ba zaka bar ma iyalanka komi ba.
Jama’a da dama sunce kyautar ka irin ta mutanen da ce:kyautar da in
mutum yazo maka da matsalar kudi to bazaka bashi rabin kuxin ba ka ce ya
tafi ya nemi sauran a’a gaba daya zaka bashi.
Shata, ka tuna fa a da can duk maroqanka kusan ka kaisu Makka. A cikin
1970 kawai, a Kano ka biya wa mutum ashirin Hajji gaba daya.
Ka yi waqoqi sama da 8,000 da bama nan nahiyar ta Afirka ba kawai har
ma Jami’o’in Amurka da Turai suna nazarin su suna amfana da su.Tun cikin
shekarun 1940 da 1950 aka fara nazarin waqoqin ka a can. Domin a
Jami’ar Kalifoniya da ke Los Angeles a Amurka kawai Turawa kusan shidda
suka amshi digiri na Ukku ta hanyar nazarin waqoqin ka da rayuwarka.Amma
daga karshe yallabai kaga sakayyar da akayi maka.
No comments:
Post a Comment