Kamar mako biyu da suka gabata na je sayen jaridu a bakin Post Office na Kano, sai na ga babban labarin jaridar SUNDAY TRIUMPH ta ranar ya na cewa Gwamnatin Jihar Kano ta yi bikin k'ona littattafan Hausa a wata makarantar sakandare ta 'yanmata. Na sayi jaridar saboda wannan labarin, a matsayi na na marubuci.
Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano, wadda ke aikin tsaftace halayyar al'umma, ita ce ta shirya bikin kona littattafan. Kuma Gwamnan Kano da Sarkin Kano duk sun halarta.
Washegari, mun tattauna al'amarin da Dr Yusuf Adamu, wanda ya ce ya aika da sakon rashin amincewa da wannan matakin ga shugaban A Daidaita Sahu din, wato Malam Bala Muhammad. Daga bisani, mun kuma tattauna al'amarin da wasu marubutan, wadanda suka hada da Maje El-Hajeej Hotoro.
Ita hukumar ta ce ta kona littattafan ne saboda a ganin ta su na gurbata tarbiyyar yara, musamman 'yan makaranta, domin akwai batsa a cikin su. Kada a manta, hukumar ta taba shirya taron marubutan Hausa na zamani da ke Kano, a otal din Tiga, aka yi musu jawabai kan al'amarin adabi. Tare da hadin gwiwar Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano, aka yi taron. An kuma biya marubutan ladar rubuta wasu kananan littattafai a bisa ruhin adabin da A Daidaita Sahu ta ke son a rika rubutawa. Tuni aka buga littattafan, aka raba su.
Shin kona littattafan ya dace? Me hakan zai haifar a nan gaba? Shin ya kamata marubuta su goyi bayan kona littattafai ko kuma su nuna rashin amincewa?
1 comment:
Tunawa da Kisan Gillar Thomas Sankara*
A cikin tarihin mulkar al’umma akwai mutane wadanda jagorancin jama’a bai zama musu wata hanya ta su cika aljihunsu da kudaden jama’a ba sai dai wata hanya ta yin aiyukan kishin kasa ga dumbin jama’a. Irin wadannan mutane sun sha fada cewa yin mafarki kawai na gyaran al’umma wani abu ne da ba zai je ko’ina ba sai an aiwatar da shi a aikace. Kaftin Thomas Isidore Noël Sankara yana daga cikin irin wadannan mutanen wanda ya kasance wani gwarzo ba kawai a kasarsa ba ta Burkina Faso har ma da Afirka.
Ranar 15 ga watan Oktoban da ta wuce ita ce ta zama shekara ashirin da kisan gillar da aka yi wa Thomas Sankara, shugaban kasar Burkina Faso – abin da ya kara tuna mana cewa har yanzu dai Afirka da sauran tafiya a gabanmu. Ya zama wajibi a tuna da wannan gwarzo. Muna tunawa da wannan gwarzo ne saboda har yanzu nahiyar Afirka yinkuri take yi wajen samun shugabannin na gari, wadannan ke da hangen nesa, kuma masu gaskiya da rikon amana, ba ‘yan amshin shata ba.
Don kuwa har a yau din nan rayuwa da manufar Thomas Sankara tana da muhimmanci wajen nuna irin mulki na misali a kullum aka wayi gari idan an yi la’akari da irin halin da wannan nahiya ta shiga na badakalar mulki da hayaniyar yake-yake na son zuciya da ke nuna ‘sai kowa ya yi mulki ko da kuwa ba abin da shi mai son mulkin nan zai kawo na ci gaba’ ga dumbin jama’ar da suke cikin kuncin rayuwa. Mafi yawancin kashe-kashen magabata musamman ma shugabanni na nahiyar Afirka sun faru ne saboda son zuciya wanda suka haifar da kashe masu matukar kishin kasa, maza da mata. Duk kuwa ba saboda wani dalili ba na Shari’a sai don wadanda suka aikata hakan su hole tare da wadanda suka ba su kwangilar aikatawa: raba arzikin nahiyar Afirka kamar su gwal, zinariya, sinadarin uranium da kuma ci da gumin mutane.
A nahiyar nan an yi kisan gilla masu yawa, wasu ma an manta da su. Wahalar da nahiyar ta shiga sakamakon mulkin danniya na ‘yan mulkin mallaka da kuma mulkin wariyar launin fata na apartheid da aka yi a Afirka ta Kudu sun haifar da munanan abubuwan da tarihin wannan nahiyar ba zai taba mantawa da su ba. An kashe Victoria Mxenge, Ruth First, Steve Biko, Amilcar Cabral, Samora Machel, Chris Hani, Eduardo Mondlane, Dedan Kimathi, Janar Murtala Ramat Muhammad da sauransu. “Amma abin da ya bambanta kisan gillar da aka yi wa Sankara da Lumumba duk da irin takaicinsu”, kamar yadda Mukoma Wa Ngugi, wani mai yin sharhin al’amuran siyasa a cikin mujallar BBC Focus on Africa, ya fada “shi ne sanin cin amanar da makusantansu suka yi. Kuma wadanda suka gaje sun a fili yake sun komar da al’umominsu da karfi baya sosai daga hanyar da aka fara bi ta ci gaba”.
Sankara, kaftin din soja ne mai farin jini, wanda ya zo karagar mulkin Burkina Faso, bayan wani juyin mulki da aka yi a 1983, juyin da ya samu goyon bayan jama’a sosai a lokacin. Nan da nan bayan hayewa kan gadon mulki sai Thomas Sankara ya kafa wasu shirye-shirye na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki wanda za a iya cewa shi ne wani yinkuri da za a ce gagarimi ne da aka yi a nahiya Afirka. Saboda ya nuna da gaske yake, saboda tun daga farko ma Kaftin Sankara ya canja sunan kasarsa da wanda ‘yan mulkin mallaka suka bayar, na Upper Volta, zuwa Burkina Faso, watau “Kasar Mutanen Kwarai”. Bayan ya hau kan mulki, ya rage yawan albashin jami’an gwamnati, wanda ya hada da nasa, ya kuma hana yin amfani da motar Marsandi irin wanda manyan shugabanni ke amfani da ita da hana sayen tikitin jirgi na babbar kujera idan za su yi tafiya.
Yana daga cikin shugabanni na farko da suka lura da cewa ginshikin ci gaban Burkina Faso da ma na Afirka shi ne a ciyar da matsayin mata gaba. Shi ne shugaba na Afirka da ya fara bai wa mata mukamai da kuma sa su a cikin aiyukan soja. Ya kuma hana auren dole tare da nuna goyon baya ga yin aikinsu da zuwa makaranta ko da kuwa suna da juna biyu. Sankara yana da cikin masu kishin muhalli na farko, inda ya shuka bishiyoyi fiye da miliyan goma saboda a raya kasar noma da kuma dakile kwararowar Hamada ya zuwa yankin Sahel. Ya kuma taimaka an yi kamfe na allurar riga kafi wanda a cikin mako guda aka yi wa fiye da mutane miliyan biyu da rabi, wanda wannan ya kafa abin tarihi a duniya. Ya kuma ciyar da noman auduga gaba da taimakawa masu sana’a’in hannu. Ya raba gonaki wadanda aka karbe daga hannun mahandama zuwa ga talakawa kai tsaye. Wannan ya jawo karuwar noman alkama a cikin shekara uku kacal, wanda ya haifar da samar da abinci mai yawa a kasar. Sankara har ila yau, ya fara wani shiri na gina hanyoyin mota da jiragen kasa wadanda za su hade duk kasar, kuma ba tare da taimakon kasashen waje ba sai kawai da albarkatun da suke cikin gida, da yin amfani da zimmar dogaro da kai da ‘yan kasar ke nunawa.
Abubuwan da Sankara ya so yi sun sami karbuwa a sassa da dama da suka wuce kasarsa ta Burkina Faso, wanda wannan ya jawo tsoro ga masu fada-a-ji, musamman ga halin mamaya da kasar Faransa ke nunawa ga kasashen da yi wa mulkin mallaka a yankin Afrika ta Yamma da kuma shugabanni ‘yan babakere da suke wadannan kasashe da suke kewaye da kasarsa. Sankara ya sha yin jawabai masu gamsarwa a taruka da dama kamar na Kungiyar Hadin Kan Afirka, watau OAU ta lokacin wadanda ke inkarin mulkin mallaka na zamani wanda ake yi ta hanyar kasuwanci da huldodin kudi. Ya yi adawa da taimakon tallafi daga kasashen waje, inda ya ce “duk wanda ya ciyar da kai, to shi ne ke mallakarka.”
A yau ana yawan maganar matsalar basussukan da ake bin kasashen Afrika da kuma hanyar mafita. Sankara kuwa yana da maganin matsalar shekaru da dama kafin ma a zo maganar yafe basussukan da ake bin kasashen Afirka a kewayen tsarin banki na duniya, Sankara ya yi kira cewa a hade kai a ki biyan basussukan na kasashen waje. A cewarsa talakan da aka zalunta ba wajibi ba ne ya biya bashin wanda ke zaluntar sa. “Bashi wata hanya ce ta mulkin mallaka” a fadar Sankara. Ya kuma kara da cewa: “Wadanda suka sa muka shiga harkar bashi caca suke yi, kamar suna gidan yin caca. Idan har suna samun nasara, ba wata matsala. Yanzu kuwa suna samun matsala shi ya sa suke cewa a biya.” A hikimar Sankara sai ya ce “to sun gama yawo” don haka kar a biya. Wannan na daga cikin shawarar da masanin tattalin arziki Jeffrey Sachs, kuma mai bayar da shawara ta musamman ga tsohon Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Kofi Annan, ya taba fada. Mista Sachs a 2004 ya ce ne kamata ya yi Afirka ta manta da bashin fiye da dala biliyan dari biyun da ake binta don ta cimma ci gaban da take bukata. Abin da Sankara ya kara a matsayin ka’idar yin haka a taron Afirka na 1985 shi ne sai da hadin kan kasashen tukuna kowa ya ki biya kawai.
Saboda wadanda ba su san waye Sankara ba, takaitaccen baninsa zai wadatar. A ranar 25 ga Nuwamban 1980, bayan an yi wasu zanga-zanga ta ma’aikatan kwadago a fadin kasar Burkina Faso, wasu gungun sojoji sun yi juyin mulki a karkashin jagorancin Kanar Saye Zerbo, wanda kuma tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje ne a gwamnatin da ta gabata ta lokacin, abin da jawo hambarar da Janar Sangoulé Lamizana wanda ya kasance a kan mulki tun Janairun 1966. Bayan an yi wannan juyin mulki sai kananan sojoji suka nuna rashin jin dadinsu wanda hakan ya sa dole sai da gwamnatin ta zabi daya daga cikinsu, Kaftin Thomas Sankara —ba tare da an tuntube shi ba—sai ta nada shi Ministan Labarai. Wannan ya yi kama da abin da ya faru a Nijeriya. Idan an duba littafin da Janar Joe Garba ya rubuta mai suna, Diplomatic Soldiering, za a ga cewa Janar Murtala ya zama shugaban kasa ne ba da ya nema ba.
To Sankara ya ki wannan mukami da aka ba shi wanda sai da lallami ya karba. Duk da haka sai da ya fada cewa shi zai sauka daga baya, ba zai wuce Janairun 1982 ba. Hakan kuwa aka yi, Sankara ya sauka daga mukaminsa a gaban wani taron ‘yan jarida a Afrilun 1982 wanda ya tabbatar da alkawarinsa a cikin takardar saukarsa cewa ya yi haka ne saboda mulkin ya zama na ‘yan tsiraru, jama’a da yawa ba sa jin dadi. A 1983 Sankara ya zama shugaban kasa bayan wani juyin mulkin soja da aka yi, juyin da ya zama na akida ba kawai saboda ya hau karagar mulki ba.
Saboda ya yaki rashawa, abin da ke cin tuwo a kwarya ga Afrika, Sankara sai ya nuna misali da kansa inda ya ki karbar albashi fiye da kudin albashin kaftin duk da cewa shi ne shugaban kasa. Ire-iren wadannan halaye sune ba su yi dadi ga sauran mukarrabansa ba. Wani mutumin kauye da aka yi hira da shi kwananan a wani shafin intanet ya ce: ‘Bai yi mamaki da kashe shi [Thomas Sankara] da aka yi ba – Juyin juya halin ne ya ba ni mamaki ba kashe shin ba. Yana kewaye ne da mutanen banza, mutanen da ke son su ci bulus da tuka tuka manyan motoci. Abubuwa da yawa sun canja a cikin Juyin juya halin. Kuma ba ta hanyar da ta dace muhimmiya ba. Amma saboda Juyin juya halin mun dan san wani abu kadan game da irin ‘yan siyasar da muke bukata’.
Daman Hausawa suna cewa mutum tara yake bai cika goma ba. Masu yin sharhin sun kawo irin abubuwan da ke sa rashin cimma manufofin gwamnati na gari ko da kuwa shugaban yana da halaye na kwarai. Tsohon shugaban Nijeriya, Alhaji Shehu Shagari ya kawo wannan a cikin littafinsa mai suna Beacon to Serve, inda ya kawo yadda manyan jami’an gwamnati ke bayar da shawara ga shugaba duk da cewa sun san ba ta dace ba, a karshe sai ka ga an kai shugaba an baro shi, jama’a kuwa su rika ganin laifin shugaban kai tsaye.
Thomas Sankara, kamar yadda masu yin sharhin al’amuran yau da kullum suka kara fada, “mutum ne mai gaggawar ganin abubuwa sun tafi daidai”, shi ne wai ya jawo abin da ya faru da shi. To amma wannan hasashe idan an lura da halin da Sankaran ya sami kansa a lokacin dole sai an yi wuta-wuta! Idan ba saboda ya yi abin a zo a gani ba, me zai sa mutanen duniya su yi tarukan tunawa da shi a yau? Wannan kuwa ba sai an je nesa ba saboda shugabannin kasar ba irin abin da ba su yin a ganin cewa an manta da shi, amma sai ga shi abin da Sankara ya ci nasarar yi a zamaninsa suna nan a cikin zukatan mutanen Afirka da ‘yan kishin kasa na sassan duniya. Wadannan abubuwa kuwa sun hada da share basussuka, gwagwarmaya da mulkin danniya, yaki da rashawa, ci gaban mata, ci gaban karkara, son kasa, kiwon lafiya ko ilimi. Mene ne aka daina magana a kansa a yau? Kuma wadanda suke ganin sun kashe shin sun huta da fitina, me suka cimma a karkashin mulkinsu? Idan ka cire rudani da suka jefa al’umma, da rashawa da zalunci me suke da shi da za su nuna ya zuwa yau?
An haifi Thomas Sankara a ranar 21 ga Disambar 1949 a Yako ta Burkina Faso. Ya shiga makarantar share fagen aikin soja ta Ouagadougou a 1966 wanda y agama a 1969. A shekarar 1970 ya koma kara samun horo a makarantar aikin soja a Antsirabe, da ke kasar Madagascar. Ya kuma halarci wani samun horon a Faransa a 1972. A wannan lokacin ne ya sami wayewa a kan harkokin siyasar kishin kasa wanda ya zame masa ja gaba ga fahimtar al’amuransa.
An kashe Thomas Sankara a ranar 15 ga watan Oktoban 1987 tare da wasu abokansa guda goma sha biyu, kisan gillar da ake zargin abokinsa, Blaise Compaoré ya jagoranta. To, Sankara ba ya nan, an kashe shi an binne a cikin rami a gefen titi na wajen Ouagadougou, saboda kawai a ga an manta da shi, amma tarihinsa har yau ana sake fitowa da shi don na baya su gane wasu darussa da za a koya ga irin rikice-rikicen da nahiyar Afirka ke ciki kuma suka ki ci suka ki karewa. Kowa sai ya ware ‘yan sojojinsa ya ce wai gyara yake so ya yi a bisa tsaunukan dazuka ana ta kashe-kashe! Ana ta daidaita hadin kan al’umma don cimma burin kai kawai. Abin fata a nan shi ne darussa dai ga su nan ba iyaka, ko Afirka za ta koyi abin da zai fitar da ita daga cikin wannan kangi na rudani? Haka kuma a mulkin Sankara ma akwai abin darasi, saboda an ce shi ne shugaban kasa a lokacin mafi talauci a duniya (saboda ya bar duniya da mota guda, kekuna hudu, tsohon firji da wasu abubuwa kadan]; shi ne kuma wanda ya ki yin amfani da iyakwandishan din ofis dinsa saboda a fadarsa jin dadi ba kowa da kowa ne ke jin sa ba a kasar! Shin wannan ba darasi ne babba ga wadanda ke cewa su shugabanni ne ba?
* Daga Attahiru Kawu-Bala, I-mail: atkaba@gmail.com.
Post a Comment