Saturday, 12 May 2007

Sashen Hausa na rediyon Faransa

Mahamane Salisu Elh Hamissou, dan jarida mazaunin birnin Yamai na kasar Nijar, ya ba mu labarin cewa a ranar Talata mai zuwa, 15 ga Mayu 2007, da misalin karfe 7: 30 agogon Nijeria da Nijar (bai fadi ba ko na dare ko na safe) sashen Hausa na rediyon kasar Faransa (Radio France International) zai fara watso shirye-shiryen sa kai-tsaye daga birnin Ikko na tarayyar Nijeria. Shi Salisu ya na daya daga cikin ma'aikatan da aka dauka su yi aiki a wannan sabon sashe.

A gaskiya na yi murnar jin wannan albishir da aka yi mana. A gani na, bude sashen Hausa a RFI ya k'ara nuna mana muhimmancin wannan harshe a fagen watsa labarai a duniya. Alhamdu lillahi. Allah ya ba su sa'a amin.

To amma ina da tambayoyi:

1. Salisu ya ce karfe 7:30 ne za a fara shirin, amma bai ce na SAFE ba ne
ko na DARE.
2. Bai fad'i a wace mita da kuma wane zango (wato SW ko MW ko FM)
za a kama rediyon ba.

Ina ba da shawara ga shugabannin gidan rediyon da su saka
talla a kafafen watsa labarai da ke akwai don su sanar da jama'a
labarin kafa wannan sashe na Hausa. Ina nufin kafafe na Hausa kamar
Gaskiya Ta Fi Kwabo, Aminiya, Leadership Hausa, Rediyon Nijeriya
Kaduna, Nagarta Radio, Freedom Radio, da sauran su.

Bayan haka, yaya na ji wai a Legas su ke, maimakon Paris? Wani sabon
salo ne? Anya ba su gudun kada wata rana jami'an tsaron Nijeriya su
kai musu ziyara idan su ka watsa wani labari da jami'an ba su so? Ka san fa daya daga cikin dalilan 'yancin da BBC Hausa da VOA Hausa su ka samu shi ne saboda sun yi wa jami'an Nijeriya nisa! Hattara!

2 comments:

mustapha shykh barnoma said...

wannan cigaba na azo asha kallo
kaima ina gaidaka dakake kokarin yada labaren hausa a wannan shabakah ta internet
sau dayawa nakan duba rubuce rubucenka domin nasamu labari kan nigeria da hausa

Unknown said...

WELCOME TO MAI GIRMA Brotherhood OF THE
Illuminati, Hello Good People Of The World, Shin
ka kasuwanci mutum ko wani artist, a 'yan siyasa, a
fasto kuma kana so ka zama mai arziki, babban, Mai ĩkon
kuma shahara a duniya, shiga mu mu zama daya
mu na aikin memba na Illuminati a yau za mu
bayar da m bayan qaddamarwa Naira Miliyan Xari
Miliyan 20 pounds.you za a ba wani manufa
damar ziyarci Illuminati da
wakilin bayan Registrations da aka kammala da
muku, ba sadaka ba, ko ɗan adam rayuwa da ake bukata, Illuminati
'yan'uwantaka kawo tare dũkiya da shahara a
rayuwa, kana da cikakken access to kauda talauci
daga rayuwarka yanzu. shi ne kawai memba wa
An aka qaddamar a cikin Illuminati da
ikon kawo wani m ga Illuminati,
Saboda haka kafin ka tuntube da wani jiki dole ne ka zama mahada
da suka riga mai m, Join mu a yau da kuma
yi mafarki. muna kuma taimakawa wajen fitar da mu
m, a kare kwayoyi turawa, da zarar ka
zama m za ku zama masu arziki da shahara
kuma mafi sauran ga sauran rayuwarka, Illuminati
yi a can m farin ciki don haka zan so ku duka
to kuma zama mamba na Illuminati Thanks.
Kirki lamba kasance a saman yau da kuma sa ka
mafarkai zo true.BENEFITS AKA TO NEW
Wakilan suke sãdar Illuminati. (1). A Cash
Sakamakon 20,000,000,00 fam, (2). A New
Sumul Dream CAR mai daraja a 120,000 fam, (3).
A Dream House sayi a kasar na
own zabi Daya Watan biki (cikakken biya) to
barcinka yawon shakatawa makõma. (4). Daya shekara Golf
Membobinsu kunshin (5). A V.I.P magani a duk
Airports a duniya (6). A total Salon canji
Access to Bohemian Garka Monthly biyan
10.000.000 fam a cikin bank account
kowane wata. (7). Kamar yadda wani mamba Daya Watan
kama da alƙawari da Top 5 shugabannin duniya
kuma Top 5 Celebrities a World.If kai ne
Yake sha'awar ... kiran mu ko whatsapp /
+2349066579253 Ko email (illuminat
inigeria27@yhaoo.com