Thursday 28 February 2008

BUK Alumni: Karramawar har da ni!

A ranar Lahadi, 24 ga Fabrairu 2008 da safe ina checking out daga Zaranda Hotel, Bauchi, sai ga text daga Dr Yusuf Adamu mai dauke da kalma daya rak, "Congrats."

Na mayar masa da, "For what?" A rai na, ina jin wata tsokanar ce. To amma gaba na ya na faduwa: Ko an ba ni sadakar aure ne, ban sani ba?

Can sai ya maido da amsar cewa ban ga abin da aka buga a shafi na 7 na Sunday Trust ta ranar ba?

Na buga text, na ce wallahi ban gani ba. Me su ka rubuta ne? Nan ma a rai na ina ta wasiwasi. Kai, ko an nada ni Ministan Harkokin Fetur ne?! (Wai ma!!!)

Gaba na ya na ta faduwa, ina jiran amsa. Can sai Yusuf ya maido da amsar cewa ai ina daga cikin mutanen da ALUMNI (kungiyar tsofaffin daliban Jami'ar Bayero) za ta karrama a wurin gagarumin bikin saukar karatu da za a yi a mako mai zuwa. Malamin ya nanata cewa ina daga cikin MANYA irin su wane da wane da wane fa da za a karrama (har da tsofaffin gwamnoni).

To fa! To kuma ni me na yi da har za a karrama ni? Tambayar da na shiga yi wa kai na kenan lokacin da na bar otal din, ni da aboki na Badamasi Shu'aibu Burji (wanda ya raka ni birnin Bauchi don ganawa da Gwamna Malam Isa Yuguda, wanda mun gana da shi a daren ranar Asabar).

Mu ka shiga garin Bauchi, mu ka sayi jaridar Trust. A shafi na 7, mu ka ga sanarwa har shafi daya. An lissafa jiga-jigan kasar nan da su ka taba yin BUK har mutum 50; ni ne na 15 a jerin: ''Alhaji Ibrahim Sheme, Editor, Leadership Newspaper.'' To fa! Duk a jerin, babu yaro ko talaka kamar ni. Ana maka maganar jan wuya ne irin su:

- Alh. M.D. Yusufu (tsohon Sufeto Janar na 'yansanda)
- Col. Dangiwa Umar (tsohon Gwamnan Jihar Kaduna)
- Gwamnan Neja Dr Mu'azu Babangida
- Brig. Gen Yuuf Bomoi (shugaban hukumar NYSC ta kasa)
- Ambassador Usman Baraya (Ambasadan Nijeriya a Amurka na yanzu)
- Amb. Hassan Tukur (Fitaccen Jakada)
- Prof. Nuhu Yakub (VC, UniAbuja)
- Prof. Attahiru Jega (VC, BUK)
- Prof. Abdullahi Zuru
- Prof. Tijjani Bande (VC, UDU)
- Prof. Ruqayya Rufai (BUK)
- Senator Ahmed Sani Yarima (tsohon Gwamnan Zamfara)
- Hon. Farouk Lawan
- Haj. Aishatu Jibril Dukku (Ministar Ilimi)
- ds

Za a karrama mu a ranar 1 ga Maris, 2008 a Kano.

Har yanzun nan, idan na dubi gaggan manyan mutanen da ke cikin shafin jaridar nan, na kan yi tunanin: wace nasara na cimmawa a rayuwa da har na shiga kwaryar manya haka?

Babu shakka sai godiya ga Allah (SWT) mai kowa mai komai.

Shata ma ya fad'i:

"Ni ko yanzu kasuwa taw watse,
Dankoli da fura goran shi,
To shi ko kasuwa tai riba.."


Alhamdu lillah.

A KULA:
Shugaban kungiyar marubutan Nijeriya (ANA), reshen Abuja, Dr Emman Usman Shehu, shi ma ya na cikin jerin wadanda za a karrama!!!! Shi ne na 7 ma a jerin. Kai, mun gode Allah. Ni ban ma san BUK ya yi ba sai a ranar.

1 comment:

Anonymous said...

and so what? old punk.