Sunday, 17 February 2008
HIRA DA RAHMA A. MAJID
Ashe Mace Ma Mutum Ce?
HIRA DA RAHMA A. MAJID
Daga Ibrahim Sheme
Hajiya Rahama A. Majid ta na daga cikin fitattun marubutan Hausa na wannan zamanin. Ta rubuta litattafan hikaya masu damar gaske, kuma ta ci moriyar su, ciki kuwa har da littafin ta da ta fi so, wato ‘Za Ta Iya.’ A yanzu haka d'aliba ce a Jami’ar Al-Azhar ta k'asar Masar. To, kwanan nan ta yi wani hob'b'asa, inda ta fito da wani jibgegen littafin hikaya mai suna MACE MUTUM, wanda girman sa ya fi na kowane littafin Hausa da aka tab'a bugawa, domin kuwa ya haura shafi 520 ne. Kamfanin Gidan Dabino Publishers ne su ka wallafa littafin.
Shin wacece Rahma A. Majid? Menene tunanin ta game da rubuce-rubucen Hausa, da rayuwar mata a k'asar Hausa, da kuma makarantan littattafan Hausa? Rahma dai za a iya cewa mace ce mai kamar maza-kwari ne babu! Ta na da kazar-kazar da nuna k'wazo da bajin ta a duk harkar da ta sa kan ta. Idan aka ce maka za ta iya yin abu kaza na bajin ta, to kai da ganin ta ka san za ta iya.
Wannan hirar da za ku karanta, mun yi ta da Rahma ne tun a cikin shekarar 2005, a lokacin da ake ta yin kici-kicin buga littafin ‘Mace Mutum.’ An buga hirar a mujallar Fim ta Nuwamba da Disamba 2005. Kafin mu kawo muku sabuwar hira da marubuciyar, mun ga ya dace ku fara karyawa da wannan, domin kuwa ko me za ta fad'a a yanzu, bai dai wuce wanda ta fad'a a wannan hirar ba.
A sha karatu lafiya.
Hajiya Rahma Abdulmajid, mu fara da jin tak'aitaccen tarihin ki.
Assalamu alaikum. Suna na Rahma Abdulmajid. An haife ni a shekarar 1980 a Agege, Legas, kuma a can na yi makarantar firamare, na fara sakandare, amma daga bisani na k'arasa karatun sakandare d'i na a Zariya, bayan da aka yi mana canjin wurin aiki a shekara ta 1998. A Zariya ne na yi difiloma a Shari’a, k'ark'ashin Jama’atul Nasarul Islam.
A wace makaranta kenan?
A Jama’atu Institute ne na yi karatun difiloma daga shekarar 1999 zuwa 2000. Bayan nan ne na koma gida Legas, na yi kwasakwasai irin na komfuta har zuwa shekarar 2002, lokacin da mu ka fara cuku-cukun neman tallafin karatu zuwa k'asar Misra. A halin yanzu ina karatu a Jami’ar Al-Azhar, shekara ta 3 zuwa ta 4, ina b'angaren Tarihi da Al’adu. Wannan shi ne tak'aitaccen tarihi na.
Bari mu koma baya kad'an; ki gaya mana sunayen makarantun da ki ka yi na boko.
Da farko dai na yi makarantar firamare d'i na a K. K. Primary School da ke Agege d'in, kuma bayan kammalawa ta a dai nan Agege d'in na ci gaba a Dairy Farm Secondary School. Wannan kenan ta b'angaren boko. A b'angaren Arabiyya kuma na soma a makarantar gidan mu ne da ake ce wa Nubrasul Huda, wacce bayan mun yi sauka na sake shiga wata wadda ake ce mata Rahmatu Islamiyya wadda ta ke Ikeja. Bayan na kammala aji shida sai na wuce Danmarkazul Illumi Islami ta Sheikh Adam El-Uluriy na yi aji 3, lokacin ne kuma ya yi daidai da tafiyar mu Zariya.
A bayanin ki, kin ce an haife ki a Legas, to ko za ki iya bayyana asalin jihar ki?
Gaskiya idan aka cire Legas to sai dai a yi waje da ni, domin mahaifin mu mutumin Sudan ne, mahaifiyar mu kuma ’yar asalin Jihar Adamawa ce. Amma na tashi ne a matsayin cikakkiyar Bahaushiya ko in ce cikakkun Hausawa a gidan mu, domin ita ce al’adar da mahaifin mu ya karb'a tun zuwan sa a matsayin sa na Musulmi.
Ku nawa ne a gidan ku, kuma ke ta nawa ce?
Mu 22 ne, kuma ni ce ta cikon 22 d'in.
Idan mu ka koma b'angaren rubutun adabi, da yaushe ki ka fara yin rubutu?
Sanannen abu ne ga duk wanda ya yi makaranta a Kudu cewa yaren Nijeriya da zai iya d'auka zai zama Yarbanci ne. Ni dai Yarbanci na koya kuma shi na iya rubutawa, to amma a wannan lokutan da wasu littattafai ke tashe, akwai wasu gidajen rediyo a Legas d'in, Sashen Hausa, su na karanta littattafan Hausa, mu kuma mu kan d'an bi. To amma da yake ya na d'aukar sati kafin mutum ya ji ina aka kwana a wannan labarin, to bayan zuwan mu Kano wata ziyara, sai na sayi wasu littattafan na rik'a bi ina karantawa, wanda ta cikin su ne zan iya cewa na koyi Hausa. Kuma abin da ya ja hankali na wajen yin rubutun littafi shi ne wani littafi da na tab'a karantawa, wato ‘In Da So Da K'auna’ na Ado Ahmed. A wannan littafi da akwai wani babi na musamman wanda aka ce "Kishi Kumallon Mata." A gani na, wannan karin magana ta sab'a al’ada, ganin ba mata kad'ai ne su ke yin kishi ba. A wannan lokacin ne na fara rubuta duk wani labari da na ji, ko ya zo kai na, a kan kishin maza da na mata. To wannan sai ya zama kamar wani raddi ne a kan wancan karin magana, wanda a kan sa na fitar da littafi na na farko, ‘Wa Ya Fi Kishi?’
Daga wannan littafi zuwa yanzu, kin yi kamar littattafai nawa?
Bisa lissafin sunaye akwai ‘Wa Ya Fi Kishi?,’ ‘Tashin Hankali,’ ‘Menene So?’ ‘Ha’inci Ko K'auna,’ ‘Za Ta Iya,’ ‘Shekaru Ashirin,’ ‘Baya Yana Suka,’ ‘Tuwon K'aya,’ ‘Laifin Wani...’ ‘Ba Ita Ba Ce,’ sannan kuma sai ‘Hadari Sa Gaban Ka...’ Wad'annan littattafai na goma sha d'aya kenan, to amma da akwai masu zuwa da kuma na d'aya da na biyu.
Ko menene ya sa ki ke rubutu da Hausa kad'ai bayan kuma kamar yadda ki ka yi bayani, kin iya yaren Yarbanci da kuma Larabci?
Bahaushe dai mutum ne mai son k'aruwar ilimi da kuma abubuwan karatu, musamman na d'ebe kewa. To kuma sai ya zamanto ya rasa wad'anda za su yi masa wannan hidimar kamar yadda ya kamata, to wasu yarurruka gaskiya suna da shi. Domin akwai wasu da su ka tab'a kirawo ni in yi wani rubutu da harshen Larabci, sai na ga wannan wani abu ne wanda ba a buk'ata, domin su Larabawa su na da masu yi masu wannan d'in, to amma Bahaushe ya na da k'arancin wad'anda za su yi wa nasa yaren hidima, ya zamanto cewa ya amfana da shi. Wannan shi ne tunani na a kan cewa e, ana buk'atar wad'anda su ke ganin cewa su na da wani sak'o na a zo a gani, to su shigo cikin adabin Hausa su dawo wa da Bahaushe abin da ya ke so ta k'aruwar ilimi.
Ko wane marubuci ya na da lokacin da ya ke samu ya yi rubutu, to da alama dai abubuwa sun yi maki yawa saboda karatu da tafiye-tafiye. Ko da wane lokaci ki ke samu ki yi naki rubutun?
Kamar yadda kowa ya sani, rubutu na da alak'a da baiwa daga Allah (SWT), to amma na fi yin rubutu a lokacin da jarrabawa ta zo min, domin a lokacin ne na ke samun natsuwa, ba na tafiye-tafiye.
Daga cikin littattafan da ki ka rubuta, wanne ne ki ke jin ya fi kwanta maki a rai?
Littafin ‘Za Ta Iya’ ne ya fi kwanta mini a rai. Sannan kuma littafin da na ke ganin ya fi saurin tafiya da sak'on da ya dame ni shi ne littafi na na farko, wato ‘Wa Ya Fi Kishi?’
Menene ya sa kusan duk littattafan ki su na magana ne a kan zaman aure, ba kya tab'o wasu jigogin?
Ba duk littattafai na ne su ke da jigo a kan zaman aure ba. Kamar ‘Za Ta Iya’ da kuma ‘Tashin Hankali’ jigon su ba ya na magana ba ne a kan zaman aure.
Me ya sa ki ka fi yin rubutun zube, ba kya rubutun wak'a ko wasan kwaikwayo ko dai wani abu da ya shafi adabin Hausa?
Wato babban abin da ya kan kiyaye mutum daga jin kunya shi ne ya rik'e fagen sa, wannan shi ne dalili.
Daga cikin wad'annan littattafai, da akwai labarin da yake magana a kan rayuwar ki?
A’a, babu.
Ga shi kin yi sabon littafi, ‘Mace Mutum’; wanda kuma ba ma karin magana ba ne. Ko menene hikimar wannan suna?
E, to, shi ainahin sunan ‘Mace Mutum’ wani suna ne wanda ya na kira ne ga duniya da mu ka fuskanta yanzu, cewa kowacce halitta ta na da k'ima, sannan halitta mafi k'ima ita ce halittar d'an’adam. D'an’adam dai a wajen Bahaushe shi ne mutum, to mace ta kan ci sunan ta ne kawai ‘mace,’ amma ba ta cin gajiyar ‘mutum.’ To, sai na yi k'ok'arin had'a wannan littafin domin ya yi nuni da cewa mace ma mutum ce kuma ta na da hak'k'ok'i da k'ima kamar na kowane d'an’adam.
Kusan duk littattafan Hausa a yanzu babu littafin da ya kai yawan wannan. Shin sak'on ne yake da yawa ko kuwa domin ki burge ne?
Abu na farko dai shi ne, k'ananan littattafan da ake yi na yanzu na saka kasala ga masu karatu. Domin na san kafin zuwa na fagen rubutu, an samu masu k'alubalanta, su na ta yin kira a kan cewa ya kamata marubuta su juya su na yin rubutu mai yawa saboda a kawo canji a adabin Hausa, ya zamanto ya samu k'ima daidai da adabi na duniya. Sannan kuma abu na biyu, ya zamanto ya kawar da kasala ta karatu, to amma sai aka kasa samun wanda zai bugi k'irji har yau ya yi, kowa ya koma daga gefe ya na jiran wani ya yi tukunna. Sai na ga cewa a wannan lokaci ana buk'atar wani ya bugi k'irji ya ce bari in je in yi wannan.
Wasu na ganin idan su ka yi littafi mai yawa, wai ’yan kasuwa ba za su amince ba domin zai yi tsada. Ke ba ki yi tunanin haka ba ki ka rubuta wannan wagegen littafi?
Kasuwar littafi ta na da alak'a da kowace k'a’idar kasuwanci. K'a’idar kasuwanci ta na buk'atar ka kyautata abu, sannan ka tallata wa jama’a cewa lallai wannan abin mai kyau ne, sannan kuma ka sa ido kan ganin yaya za a yi su saya. To amma kasuwar littattafan mu na Hausa da ake ganin shin za ta tafi ko ba za ta tafi ba? Shin ina ta tsaya tukunna? Littafi zai fito a sati, amma babu wanda ya san zai fito sai marubucin. Watak'ila ma shi mai shagon da za a kai wa littafin domin ya sayar bai san da littafin ba sai a ranar, a wannan lokacin ake tunanin cewa za a iya tantance shin ko wannan littafin ya na da kasuwa ko kuma ba shi da shi? Bisa ga tsarin kasuwanci, littafin da ya zamo cewa na d'aya ko ka kyautata aikin sa, misali tafiyar ka ta baya ta nuna wa mutane cewa e, lallai wannan aikin da gaske ka ke. Ina k'ok'arin ganin na tallata littafi na tare da sanar da isowar wannan littafi da inganta aikin sa. Kuma wannan shi ne zai nuna wa mutum cewa e, na gama duk abin da zan iya. Abin da ya yi saura kuma shi ne k'addara da za ta biyo baya a kan me littafin ya k'unsa?
Menene labarin da ke cikin ‘Mace Mutum’?
Labarin ‘Mace Mutum,’ a tak'aice, labari ne na mata biyu, uwa da ’ya. Uwa ce wadda ta tashi a cikin rayuwa ta k'auye, sannan ta ga yadda mata su ke ci-baya a k'auyuka, yadda su ka yi daga rayuwar ta har da ma ta ’yan’uwan ta. Hakan ya sanya bisa yarinta su ke tsammanin cewa duk abubuwan da su ka yi kaca-kaca da rayuwar mata a k'auye kamar wasu dodanni ne da ya kamata a guje su. To sai ta yi yarinta ta gudu daga k'auyen zuwa birni, ta ga yadda lafiya ta ke a k'auye, mata na mutuwa wajen nak'uda, a ce an yi camfin mazan su ne ko kuma akwai wata cuta da za a iya magance ta, a ce a’a akwai wani macijin aljani ko menene da ya ke giftawa shi ne ya ke janyowa. To tunda a k'auyen su ya ke, sai ta yi tunanin ta gudu. Bayan ta gudu ka ga ta gudu daga matsalar mata da ke cikin k'auyen, sai ta ke tsammanin cewa mace mutum ce a cikin birni.
A yayin da ta shigo birni, shi kuma ya na da nau’in tasa matsalar ta daban. Idan mace a k'auye ba ta wuce daraja irin ta doki ba misali, wanda shi sai ranar Juma’a ake hawan sa, ita kuwa idan ta fita aiki tun da safe ba ta dawowa sai k'arfe 11 na dare, to sai ta zo ta samu ga mata nan a cikin birni wad'anda babbar matsalar su shi ne, idan za ka tafi asibitin k'auye ka same su a kwance su na fama da ciwon yoyon fitsari, to za ka zo asibitin birni ka samu mata na fama da ciwon zuciya domin su sun san ’yanci, an gaya musu akwai, amma kuma ba za su iya magance shi ba.
To wad'annan matsalolin da ta gani ya sa ta fara tunanin neman wani wurin zaman tsaka-tsaki wanda shi ba k'auye ba kuma ba birni ba, domin ta rayu. Daga nan sai ta fad'a wani waje wanda al’ada ce ta ke mulkin wajen ba k'auyanci ko birnanci ba. A irin wannan waje ne ta samu ta yi aure har ta haifi ’yar ta mace. Ita dai wannan ’ya kasancewar ta zo ne a gidan sarauta, sannan kuma gidan da ba a tab'a haihuwa ba. Ciroma ya ke buk'atar wanda zai gaji sarauta ba wadda za ta saci sarauta a matsayin ta na mace ta kai gidan wani ba. To wad'annan matsalolin da ta samu sun had'a da matsalolin da ake samu a k'asar nan, misali ta b'angaren kafa shari’a ko al’ada, ya zamanto cewa an hukunta mace. Hakan ne ya sanya ta gudu da ’yar ta sannan ta tafi wani sashen daban wanda a yanzu kuma ba nema ta ke ta zama mace mutum ba, nema ta ke ta zama mace, ta tsira, ta rayu domin ta san cewa tata ta k'are a wannan lokaci, domin duk abubuwan da ta samu a duniyar ta ta yi asarar sa, sai dai a kan hanyar yadda za ta raini ’yar ta duka-duka ba ta wuce shekara 2 ba. Ita kuma ta mutu a sakamakon wata wahala da ta sha.
To ita wannan ’yar ta samu kundin tarihin rayuwar ta, domin ita uwar ta shirya shi ne a matsayin ta san ba za ta raini wannan ’ya tata ba, saboda ta na buk'atar ta yi wani wanda zai zama shi ne ruhi na tayar da k'aimin ’yar ta, sannan kuma ta bayar da amanar cewa a taimake ta.
To wannan ’ya ta yi duk abin da ta ga ya dace wajen ganin mace ta cika mutum ta hanyar addini da al’ada, siyasa da kuma lafiya, har ma da wasu abubuwa wad'anda mata su ka rasa a halin yanzu, domin ganin ta tabbatar wa da mata hak'k'in su.
Tirk'ashi! Jigon littafin ya zama wani mataki na gwagwarmaya domin tabbatar da ’yancin matan Hausawa kenan?
E, haka ne. Ina magana ne a kan matan Hausawa ko matan Nijeriya ko kuma matan Afrika ta Yamma, to amma matan Hausawa su ne a kan gaba wajen tsintar kan su a irin wannan hali. Wannan ne ya sa na zab'i matan Hausawa su zama ‘characters’ na labarin.
Shin ko ki na da shirin wata rana ki fassara littattafan ki, musamman ‘Mace Mutum,’ zuwa wasu harsuna kamar Turanci, saboda mata su amfana da shawarwarin da su ke ciki maimakon a tak'aita a wani yare kad'ai?
E, ina da nufin fara rubuta na Turanci.
Da ki na daga cikin marubutan Hausa da ake suka, ana kiran ayyukan su "adabin kasuwar Kano." Shin wane k'ok'ari ki ke yi da wannan littafi ki fita daga cikin wannan k'angin?
E, to, "adabin kasuwar Kano" yadda na fuskance shi wani suna ne na alfahari, ya danganta da yadda kowa ya juya shi. Zai iya kasancewa kamar ana buk'atar mutum ne ya zamanto ya na zaune ne kan sa, ba ya na tsaye ne da abin da mutane su ka ce ba. Adabi ya na buk'atar masu k'alubalantar sa, kamar yadda "adabin kasuwar Kano" ya ke da masu k'alubalantar sa. Haka ma ya ke da wad'anda su ke son sa. To wannan ya nuna cewa ba k'ok'arin fita daga "adabin kasuwar Kano" ba ne, illa cewa ra’ayi na da tunani na shi ne ya yi mani wahayin wannan littafin.
Wacce irin alak'a ce tsakanin ki da masu karatu?
Alak'ar da ke tsakani na da masu karatu ta fi komai dad'i a wuri na. Na d'auki masu karatun littafi kamar wani k'ashin baya ne, kuma su ne za su iya gaya maka cewa abin da ka rubuta ya yi dad'i ko kuma an samu kuskure domin ka gyara a rubutun gaba. Hakan ya sa akwai alak'a mai kyau tsakani na da su.
Alak'ar ki da sauran marubuta fa, domin masu kula da harkokin marubuta na ganin babu alak'a mai kyau a tsakanin ku marubuta.
Alak'a tsakani na da mafi yawan marubuta alak'a ce mai kyau. Ko da yake ni ba a k'asar nan na ke zaune ba, to amma na samu an kafa k'ungiyoyi wanda kuma manufar kafa su shi ne wata ta yi gaba da wata, wanda hakan ko kad'an bai kamata ba. Amma ni ba na cikin kowace k'ungiya; kusan in ce ni marubuciya ce mai zaman kan ta.
Ga shi ke monita ce a wani zauren tattaunawa a intanet a kan rubuce-rubucen Hausa (Majalisar Marubuta). Ko za ki yi mana bayani a tak'aice kan yadda wannan zaure ya ke, da manufofin sa?
Wannan ya na da labari ne na shiga ta ita k'ungiyar. Kafin in shiga ban san cewa Hausa adabi ba ne wanda ya na da masu k'alubalantar wata kasuwa wadda saboda nisa na da ita, iyakaci na in yi littafi in ajiye, amma da shiga ta wannan k'ungiyar kafin ma in zama monita a ciki na ga wad'annan amfanonin da dama. A cikin wannan majalisar na samu sanin wasu littattafan Hausa da aka yi masu k'ima, da kuma abubuwan da ake k'alubalantar marubuta da su, sai in je in d'auka wanda zan gyara ya zamanto cewa na gyara. Sannan kusan zan iya cewa a da ina da d'an shakku wajen cewa yaya za a yi in yi littafin Hausa mai yawa ya tafi? To amma shiga ta wannan majalisa ya nuna min cewa lallai ashe ana iya yin, kuma zai iya tafiya. Misali, na tarar ana tattaunawa a kan ‘Ruwan Raina,’ wanda a lokacin ban san shi ba, da kuma ‘’Yartsana,’ wanda shi ma ban san shi ba sai a cikin wannan majalisar na samu cewa littattafai ne masu yawan shafuka, kuma aka yi masu kyakkyawan bugu. Sai ga shi ba su samu wata matsala ta kasuwa ba, sannan marubutan da su ka yi su sun cancanci yabo.
Saboda haka ina shawartar marubuta da su shiga cikin wannan k'ungiya ko majalisa domin akwai abubuwan k'aruwa masu tarin yawa; haka ma masu karatu, domin su samu damar k'alubalantar abin da marubuta su ke ciki. Wannan ita ce hanya ta had'uwa da ’yan’uwan su masu rubutu a tattauna da manazarta wad'anda su ka yi fice da fuskantar ina adabin ya dosa. Hakan a gani na zai taimaka wajen kawo ci-gaba ga ita wannan harka tamu.
Yaya ki ke ganin adabin Hausa zai iya kasancewa nan da wasu shekaru?
E, ai Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake ganewa. Daga cikin kashi biyu, wato marubuta da masu karatu yanzu ya zamanto su ne su ke canza adabin Hausa, wanda wannan kuma alamomi ne na nasara. Da farko idan na soma da masu karanta littafi a zamanin baya, kamar k'arshen k'arnin da ya wuce, littattafan Hausa su na samun suka domin babbar matsalar da na sha fad'i ita ce masu bayar da sak'on su na da wani sak'o da su ka ga cewa lallai ya damu Hausawa, ya kamata kuma a tashi a yi fama da matsalolin, kamar na auren dole da makamantan su, domin haka na da illolin sa na b'acin ’ya’ya, to amma sai su ka manta da wani abu guda d'aya, wato ba iyayen ba ne su ke karanta littafin za su iya kwafar b'acin da aka nuna a cikin littafin, maimakon iyayen wanda da aka yi wasu wannan salon. Hakan ya janyo ’yan matsaloli wad'anda littattafan baya su ka samu kan su a ciki. To amma masu karatun da ake samu a yanzu su ne ’ya’ya na wancan zamanin wad'anda su ka karanta kuma su ka k'aru da wani abu, su ne su ka zama iyaye, su ke karatu a yanzu. Adabin Hausa ya samu iyaye da ’ya’yan su su na iya karantawa, sab'anin zamanin baya.
Na biyu, masu karatu na da hanyoyin sabuwa ko huld'a da marubuta kamar ta wayar tafi-da-gdan-ka ko kuma ta intanet, domin yi masu gyare-gyare ko sharhi da makamantan su. Ta b'angaren marubuta kuma, ban da masu yin canjin shek'a ma da akwai wad'anda su ka ce adabi ko na menene ya na da amfani, don haka sun bayar da lokacin su wajen yi wa adabin Hausa hidima wacce ta cancanta za su rubuta da kan su, za kuma su yi kira ga marubuta su ce kuma ku rubuta abu kaza. Saboda haka adabin yanzu idan za mu lura da littattafan da ake rubutawa masu yawan shafuka da kyawu, zai nuna mana cewa duk wani littafi da yake kamar wata annoba ce a cikin adabin Hausa a baya kamar shekara goma, zai zamanto cewa ya kwanta dama.
Akwai wani kira da za ki yi ga su marubutan Hausa?
Kiran dai a kowane lokaci shi ne wad'ansu abubuwa ne wad'anda da zarar an same su komai zai daidaita. Marubuci ya kamata ya san cewa ga inda sak'on sa za shi. Na biyu, ana buk'atar marubuci ya san menene adabi. Na uku shi ne menene na sak'o wato adabin da na ke yi wa hidima? Sannan kuma bai kamata marubuci ya yi tsoro ba, ba wai ina nufin sai ranar da marubuci ya fito ya zagi wani babba ba, a’a, tsoron kasuwa ma bai kamata a ce marubuci ya ji shi ba, domin ba a tab'a yin masu yi wa adabi hidima iyakacin sa ya damu da kasuwar sa ba ko inda adabin za shi ba. Don haka ya kamata ya zamanto cewa wannan ya na kan gaba.
To menene zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ daga alk'alamin ki?
Abin da zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ shi ne ina so in ci gaba da yin rubutu a manyan shafuka mai ingantaccen bugu, kuma wanda zai zamanto ya na da sak'on da zamanin ya ke so. Wannan ya sanya ba zan iya sanin menene zai biyo bayan ‘Mace Mutum’ ba, domin ina so ne in kasance kowace shekara a ce da littafin da zai fito, ya zamanto cewa ainahin sak'on da ake buk'ata shi littafin ya taho da shi.
Yaushe ne za ki kammala karatun ki ki dawo Nijeriya da zama?
Shekara mai zuwa ne zan kammala karatu na, to amma da yake ina da buk'atar k'are digiri na na biyu shi ne ya sa ba ni da masaniyar lokacin da zan dawo.
A can Alk'ahiran ko kuwa?
E, ko a Alk'ahira ko kuma a gaba da ita.
A’a, to shikenan kin dinga karatu? Aure fa?
(ta yi dariya) Ai aure ba ya hana karatu.
To yaushe za a yi auren? Wasu za su so sanin haka daga gare ku.
To ai kada wanda ake so a yi da shi ya ji, kuma ya matsu ya ce an sa marad'a magana! (ta k'yalk'yace da dariya)
Hajiya Rahma, mun gode.
To, ni ma na gode.
-----
KARIN BAYANI: An sake buga wannan hirar a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'a da ta gabata, 15 ga Fabrairu 2008
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
6 comments:
inviting you to visit my blog...
Na karanta hira da kuka yi da Rahma a mujallar fim (na da)kuma na jinjina mata.Abin mamaki shine ita ba bahaushiya bace amma tana kirkiro labarbare da ke fadakardamu kuma nishadantardamu.Allah ya kara mata basira,Ameen.
Ga address din blog din na inda na rubuta akan fulani da kuma hausa fim dss.
http://jinni-musingsofalostsoul.blogspot.com/
Who reads this crap? Nobody I see! Get the fuck real!
cheap wow power leveling buy wow gold cheapest wow power leveling CHEAP wow gold BUY power leveling CHEAPEST wow powerleveling
wow goldwow goldwow goldwow goldweiwei
Hira Da Rahman AL. Majid ay isang kahanga-hanga babae dahil siya ay tapos na marami para sa kanyang bansa. Gusto ko na salubungin siya dahil isaalang-alang ko ang kanyang tunay na marunong. Gusto kong talakayin sa kanya ang tungkol sa ilang mga paksa tungkol sa kanyang kultura.
Hira Da Rahman AL. Majid ay isang kahanga-hanga babae dahil siya ay tapos na marami para sa kanyang bansa. Gusto ko na salubungin siya dahil isaalang-alang ko ang kanyang tunay na marunong. Gusto kong talakayin sa kanya ang tungkol sa ilang mga paksa tungkol sa
kanyang kultura tulad ng kanilang mga pananaw tungkol sa buy kamagra
Post a Comment