Tuesday 4 August 2009

Ba gyara Rabo ya zo yi ba

A gaskiya, ko kadan ba da nufin gyaran harkar fim Malam Abubakar Rabo ya zo ba. Ya dai zo yin gyaran gangar Abzinawa ne - wato kid'an ganga da lauje! Abin da ya sa na fadi haka shi ne, kusan dukkan muhimman matakan da Rabo ya dauka a kan wannan harkar, ya dauke su ne da nufin durkusar da harkar. Ga hujjoji na:

1. Tun daga ranar farko ta kama aikin sa, ya dukufa wajen b'ata sunan 'yan fim. Ba wai a yau ya fara ba.

2. Duk wasu shawarwari nagari da 'yan fim din da sauran jama'ar gari su ka ba shi na yin gyaran da ya dace, bai dauka ba.

3. Duk wani zaman shawara da 'yan fim su ka yi da shi, aka zartar da shawarwari, bai taba aiwatar da ko daya ba; sai ma ya rika yi masu yankan baya bayan an tashi daga zaman.

4. Rabo ya zagaya jihohin Arewa da dama inda ya bukaci magabatan jihohin da su zartar da kudirorin hana yin sana'ar fim.

5. A kan d'an k'aramin laifi, Rabo ba ya tausaya wa d'an fim, sai kurum ya sa a kulle shi ko kuma kotu ta yi masa babbar tara.

6. Ya sa an kulle 'yan fim din da ba su aikata laifin komai ba, musamman Hamisu Iyan-Tama, don kurum ya fashe wani haushi nasa na son rai.

7. Har yau bai karbo wani agajin kudi daga gwamnati ya raba wa 'yan fim ba don inganta sana'ar su ko kuma ci gaba da yin sana'ar.

8. Ya dauki masu shawara tagari a matsayin abokan adawa ko ma abokan gaba, duk da yake su ba hakan su ka dauke shi ba.

9. Ba ya yarda ya tafi tare da masu ba shi shawara, sai 'yan kore wadanda ke gaya masa abin da kunnen sa ya ke so ya ji.

10. A kullum kokarin sa shi ne ya gano hanyar da zai bi ya nakasa 'yan fim da sana'ar su, ba hanyar da zai taimaka masu su ci gaba ba.

11. Duk wata bita da ya shirya da nufin wai gyaran fim, idan ka duba da kyau sai ka ga da biyu aka yi, ba wai an yi ba ne don gyara sana'ar. Domin ko su wadanda ake zaba su shiga bitar, sai an tsamo 'yan kore, 'yan a-bi-Yarima- a-sha-kida, sannan a yi da su.

12. Yau shekarar Rabo biyu a kan mulkin, me ya kulla na kawo gyara?

No comments: