Thursday, 6 August 2009

AN KULLE BASHIR DANDAGO A JARUN

Shugaban Hukumar Hukunta 'Yan Fim ta Jihar Kano, Malam Abubakar Rabo, ya cika alkawarin sa na cewa sai ya d'aure daya daga cikin fitattun mawakan Kano, wato Malam Bashir Dandago. Domin kuwa a yau dai jami'an hukumar sun kama shi, sun gurfanar da shi a gaban kotun hukunta 'yan fim.

Haka kuma an kama wani matashi mai suna Kabir Maulana.

Laifin da ake tuhumar su da shi, shi ne: wai sun saki faifan wakar 'Tsangayar Kura' (mai dauke da wakar nan ta "Hasbunallahu" ) bayan hukuma ta hana sakin faifan a Kano.

A kotu, su Dandago sun ce, "Not guilty." To amma Alkali Mukhtar Ahmed, kamar yadda ya saba yi, ya hana belin su, ya tura su gidan yari. Ya ce a dawo ran Litinin a ci gaba da magana. Manufa ita ce, su ma dai sun yi zaman jarun.

Ga wadanda su ka saurari wakar "Hasbunallahu, " za su tuna da cewa akwai muryar Malam Bashir Dandago a ciki. To, da ma kaska ta na da haushin kifi.

Shi dai Dandago, ya yi fice ne a fagen wakokin yabon Manzon Allah (SAW), wato wakokin bege. A cikin 2009 ne aka ji muryar sa a wakar "Hasbunallahu, " wanda hakan ya kara wa wakar karfi da karsashi. A wata hira da ya yi da 'yan jarida kwanan baya, Dandago ya ce ya yi wakar ne domin ya taimaka wajen murkushe zaluncin da ake yi a Kano.

Kwanan nan kotun ta su "Asabe Murtala" ta daure jagaban wakar "Hasbunallahu, " wato Malam Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA), a gidan yari. Za a ci gaba da shari'ar sa a makon gobe.

Majiya ta ce gurfanar da Rabo da 'yan fim su ka yi a ofishin 'yan sanda na Metro kwanan nan ya k'ara hayaka malamin, har ya sha alwashin yin ramuwa.

Majiyar ta ce don haka dai kwanan nan hukumar za ta kama wasu mata daga cikin 'yan fim, musamman mawakan da ke cikin su. Sannan majiyar ta ce ana nan ana hak'on wani dan fim, tare da shan alwashin cewa a gidan yari zai yi azumin Ramadan.

"Zalunci ba zai dore ba" - Maryam A. Baba, a wakar "Rabo, Rabo"

No comments: