Sunday 26 August 2007

GYARAN GANGAR ABZINAWA!

Na saurari jama'a a cikin 'yan kwanakin nan tun lokacin da hayaniyar Hiyana ta taso, kuma na karanta wasu ra'ayoyi a kan lamarin. Akwai mutane da na ga suna cewa wai ya kamata a dakatar da harkar shirya fim baki daya a kasar Hausa. A yanzu haka ma akwai masu cewa harkar finafinan ta mutu har abada!

Ni ra'ayi na ya bambanta. Ba na tsammanin za a daina yin fim saboda Hiyana. Ga dalilai na:

1. Fim al'amari ne na ci-gaban fasaha (technological development) da ya shigo kasar Hausa. Kamar ka ce a daina amfani da wayar GSM ne. Fim ya riga ya zo, ko mu ce ya ci gaba (domin kuwa tun tale-tale akwai shi). Ba zai dainu ba.

2. Fim sana'a ce. Ko tana da kyau ko ba ta da kyau, sai an yi shi. Ni a gani na, sana'a ce mai kyau idan za a gyara ta, ta yadda za ta tafi daidai da addinin mu da al'adun mu. To mu dauka ma ba ta da kyau din kamar yadda wasu ke cewa; shin an hana sata? An hana karuwanci? An hana zamba? An hana shan wiwi? Me ka hana?

3. Idan aka hana yin fim (wai wa ma zai hana? Gwamnati ko malamai ko mutanen gari?), to za a samu 'yan sunkuru su rika shirya "finafinai" wadanda suka fi wannan da ake yi yanzu muni. Wato za su yi ramuwa kan hana su harkar da aka yi. Su rika sayarwa ta bayan gida (underground).

4. Idan an hana yin fim a Kano, za a hana yi ne a Filato ko Bauchi da Kaduna da duk sauran jihohi? Za a hana a Legas da sauran jihohin Kudu? Ko kuwa idan an je Legas an yi fim din Hausa, sai a hana sayar da shi a ko'ina a Nijeriya? A lura, Gwamnatin Tarayya ba za ta hana yin fim din wani yare ba.

5. A gani na, Gwamnatin Jihar Kano din ma ba za ta hana yin fim ba domin 1. harkar fim ta rage wa gwamnatin matasa marasa aikin yi. Na biyu, sana'ar fim ta kasance hanyar samun dimbin kudaden shiga ga gwamnatin Jihar Kano ta hanyar kudaden harajin tace fim da sauran su. Na uku, sana'ar fim ta taimaka wa harkar kasuwanci a Kano. Akwai manyan 'yan kasuwa da aka samu ta hanyar sana'ar fim. Shin gwamnatin Kano za ta kashe harkar fim a daidai lokacin da sauran harkokin kasuwanci na Kano (misali, masana'antu) suke durkushewa?

Ga mafita.

Na sha gaya wa wasu mutane cewa shirin fim kamar d'aki ne -- idan ka zuba shara ciki, za ka tarar da shara a ciki; idan ka zuba tabarmi masu kyau a ciki, su za ka tarar. Don haka kamata ya yi a gyara sana'ar don ta tafi daidai da tarbiyya tagari. Dakatar da harkar zai kasance gyaran gangar Abzinawa.

Duk masu cewa a dakatar da fim -- daga 'yan boko zuwa malamai da sauran masu surutu -- suna yi ne saboda wani dalili na son rai nasu. Wasu don a ce sun ce. Wasu don su nuna su malamai ne. Wasu don su nuna cewa su 'yan gurguzu ne (radicals). Wasu don son a sani. Kai, wasu ma don sun jahilci abin ne. A tuna, tun kafin al'amarin Hiyana, akwai masu sukar harkar fim. Gyaran ne aka ki yi. Amma yanzu dama ta samu ta yin gyara, don haka sai a gyara. Akwai sana'o'i da ayyuka da suka fi fim muni, amma ba a dakatar da su ba, sai wannan?

Kuma su masu sukar 'yan fim da sana'ar fim, da me suka fi 'yan fim tarbiyya? Akwai manema mata da 'yan luwadi da mazambata da magulmata da matsafa da sauran mugga a cikin al'umma a cikin su da ske cewa wai a hana yin fim saboda "laifin" Hiyana. Wanzami ba ya son jarfa, ko?

Kai, gaskiyar masu iya magana da suka ce laifi tudu ne - ka taka naka, ka hango na wani.

3 comments:

Zahratique said...
This comment has been removed by the author.
Zahratique said...

Gaskiya ka fadi gaskiya a nan. Kawai ya kamata a gyara kuma a barsu su cigaba da sana'arsu.

Na biyu kuma Nigeria ya kamata a ce kasar democracy ce kuma hana su sana'ar nan kaman kwace musu yanci ne. Ka ga haka bai dace ba kuma yana iya kawo tashin hankalin da bai kamata ba. Allah ya kiyaye.

Unemployment rate ma kawai zai yi leading to so many crimes...

Anonymous said...

cheap wow power leveling buy wow gold cheapest wow power leveling CHEAP wow gold BUY power leveling CHEAPEST wow powerleveling
wow goldwow goldwow goldwow goldweiwei