Wednesday, 22 August 2007

'Yartsana za ta sake shiga gari!


Littafi na, "'Yartsana," ya sake fitowa. Tun lokacin da ya fito a cikin 2003, ya ci kasuwa a 2004, ba a k'ara ganin shi ba. Ya k'are! Mutane sun sha tambaya ta cewa don Allah a sake buga shi, amma ina! na kasa saboda yanayin rayuwar kasar mu. To amma yanzu an buga shi, aka gama a makon jiya. Zai fito a ranar 1 ga watan Satumba. Ko yaya mutane za su kalle a yanzu bayan hayaniyar Hiyana? Oho! Ban damu ba.

2 comments:

Talatu-Carmen said...

Madalla! A gaskiya, littafin nan ya burgeni. A ina za a sayo shi?

xpsanusi said...

Sheme ina labarin 'GA CICI NAN' da ka tsegunta min a 2003? Har yanzu ina jira...