Wednesday 22 August 2007

JARABA 1

JARABA wani sabon littafi ne da na ke rubutawa, ana bugawa a jaridar Leadership Hausa kowace Juma'a. Wannan shi ne kashi na farko, wanda zai fito jibi Juma'a a jaridar idan Allah ya kai mu. A sha karatu lafiya.

BABI NA DAYA

Tara ta gota. Lokacin da Tanimu ke karyawa, ya ji lokacin da tamburan gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna su ka buga, kuma ya ji mai gabatarwa na cewa, “Yanzu }arfe tara. Ku na tare da Sashen Hausa na Rediyon Tarayya na Kaduna.” Daga nan sai aka sako ki]a a filin ‘Za~en Mai Gabatarwa.’ Kassu Zurmi ne aka sako ya na rera wa}ar Shayi [an Gidan Labbo. A duk lokacin da Tanimu ya ji wannan wa}a, ba abin da ya ke tunani sai dalilin da ya sa Shayi ya zama talasuru haka.
Bara ya yi jidalin bi]ar aure sai da yas samu,
Kai ta gidan maigidan su yah hwa]i,
Tsoho ya hwa]i ba abin ]iba
Kuma ba abin gado,
Su ko masu gari, dan}o ba ka hwa]uwa }asa banza.
To amma kuma daga baya sai ga shi Shayi ya nuna mana cewa ya san abin da yake yi. Ba wawa ba ne. Ba gaula ba ne. In ba haka ba, ya aka yi har ya “hwara sassaben gonas su”? Kuma ya aka yi bayan masu gari sun sayar da gonar, ya yi tawaye har aka mayar masa da gonar ala tilas? Anya Shayi talasuru ne? Tanimu ya tambayi kan sa a yayin da amon gangunan Kassu ya cika masa falo, ya na fitowa daga cikin wata ]ibgegiyar rikoda da ke kan dibaida.
Can sai ga Tsahare ta shigo. Ta na sanye da ba}ar abaya mai ratsin kore tare da wata }awanya a }asan ta mai ruwan gwal.
“Yanzu za ka tafi ne?” ta tambaye shi.
Tanimu ya tsotse yatsun sa, ya ture kwanon ]umamen nan gefe, sa’annan ya amsa, “{warai kuwa. Ban son Alhaji ya riga ni zuwa shago, ko da yake dai ya ce zai je ]aurin aure da safen nan. In ya riga ni, zai yi min fa]a. Kin dai san shi da fa]a – kamar sabon kuturu.”
Tsahare ta yi ‘yar dariya, ta ce, “Uh hm! Kada dai ka ciji yatsan da ke }osar da kai.” Ta je ta nemi wuri a kan kushin ta zauna da }yar. Ta na da tsohon ciki, wanda ya maida ita ta na harkokin yau da kullum a takure kamar mai ta~arya a cikin ciki. “In ka na ruwa, kada ka zagi kada.”
“Tsaharatu kenan! Wallahi shi ya sa na ke son hira da ke. Ba ki ganin laifin kowa,” inji shi.
“Ba haka ba ne, Tanimu. Kai da Alhaji dai ai ba a cewa komai. Duk wanda ya san ka, tare ya gan ku. Kuma wane abu na alheri ne bai yi maka ba? Kar ka manta, shi ne fa ya biya maka sadaki; kai, shi ne ma ya yi ma wannan auren.”
“Oho! Gori kuma za a yi mana? To, ko za a maida amaryar gidan shi ne, ni a bar ni haka nan?”
“Allah ya huci zuciyar ka. Ba nufi na kenan ba.”
Tanimu ya mi}e daga kan tabarma inda ya zauna ya yi kalaci. Sai ya tuna bai sha ruwa ba, don haka ya du}a ya ]auki goran roba, ya kwankwa]i ruwa.
Tsahare, hannayen ta a kan cinyoyin ta, ta na kallon ma}ogwaron sa, kamar ta na kallon ruwan ya na wucewa a kwararon sa tamkar wani }aton kogi.
“Wannan irin shan ruwa haka – sai ka ce wanda ya cinye giwa?” ta tsokane shi.
Ya aje goran, ya dube ta, ya ce, “Tsahare ai wannan malmalar da na cinye, ]aya ta ke da giwa. Zakaran ka, ra}umin ka. Kuma ga shi kin yi mani irin miyar da na ke so – kuka da man shanu da ]an yajin tattasai.”
“Miyar kuka Baha]ejiya! An gaishe ki mai sa maigida santi!” Tsahare ta yi dariya, ta mi}e.
Tanimu ya ]auki hular sa da ke kan kujera, ya sa. Shi da matar sa su ka fita daga ]akin, su ka doshi babur ]in sa da ya aje kusa da }ofar shiga gidan. Da ma a duk lokacin da zai tafi aiki, sai Tsahare ta raka shi inda mashin ]in sa ya ke.
Gidan nasu ya na }unshe da gidaje uku, kowannen su flat ne mai ]aki biyu da falo da ban]aki da madafa. A tsakar gidan akwai bedi inda matan gidan su kan taru su na yin hirar su da ‘yan aikace-aikace. Domin fa a gidan matan aure uku ne. [aya sunan ta Lami, matar wani ma’aikacin reluwe mai suna Abdullahi; ]ayar kuma Magajiya, matar Ustaz.
Da su ka isa, Tanimu ya dudduba mashin ]in, sannan ya buga shi ya tayar. Gidan ya cika da rugugin sa. Da ya hau mashin ]in, sai ya dubi Tsahare, ya ce, “Allah gama fuskokin mu da alheri!”
Ta kara hannu a jikin kunnen ta, ta ce, “Me ka ce? Wallahi ban ji ba!”
Ya ce, “Cewa na yi gamon katar!”
Sai ta sa hannu ta kama makullin mashin ]in, ta juya shi. Mashin ya mutu.
Ta ce, “Ai da sai ka bari sai mun gama magana sannan ka tafi. Ba na jin ka, saboda }arar mashin. Me ka ce?”
“Cewa na yi sai mun ha]u. Anya lafiya wannan kunnen naki? Ko ~ur~ushin kurunta ya soma shigowa ne?”
“Wallahi lafiya ta lau. Haba Tanimu, mashin ]in naka ne ya cika rugugi, abu kamar jirgin sama! Shi ya sa na ran nan na ce ka sayi Besfa, ta fi da]in sha’ani. Ka san ni abin da ke shero ni Besfa shi ne ‘yar gu]ar nan tata mai da]i idan an murza ta. Ni in da namiji ce, ba yadda za a yi in sayi mashin bayan ga Besfa. Da za ka sayi Besfa, zai dace. Ka ga idan ma mutane sun gan ka, sun san ba ]an aca~a ba ne.”
“Kin fara ko? Ke dai Tsahare ba ki rabuwa da tsokana.” Ya dubi rigar sa, wadda shu]iya ce mai kyakkwan aiki a wuyan ta. “Ya za a gan ni a haka a ce min ]an aca~a? Ai su ‘yan aca~a da ka gan su ka san su ne; abu za ki ga wani ma kamar ]an sama jannati! Wasu za su saka irin hular nan hana-salla da burgujejen wando irin wanda ake kira buhun mahaukata, da tsohuwar rigar sanyi ‘yar Rasha wadda kila ma mai ita ya da]e da she}awa barzahu. Wani ma sai ki ga har da ba}in gilashi ya }wamo, wai shi niga. Abin babu ko kyan gani.”
“Ni fa wannan shigar tasu ta na ]aya daga cikin abubuwan da ya sa ba na hawan express lokacin ina budurwa. Wani ]an express ]in ma sai ka ji ya na wari.”
“To me zai hana su yi wari tunda dai kullum su na cikin gumi, sun ]ibga kaya kamar gawa a makara? To yanzu da irin wa]annan ne za ki kwatanta ni, ni da ke cikin shigar mutunci? Ai yaro ko da ganin birni ya san ya fi garin su.”
“A cikin ‘yan express akwai masu shigar mutunci. Irin magidanta ]in nan masu shekaru da ]an kauri-kauri. Su ba sa yin irin shigar nigogin nan. Ni na fi son hawa mashin ]in su. Ga shi kuma ba su gudun fitar hankali irin na sauran ‘yan mutuwar. To wasu za su iya ]auka kai irin su ne.”
“Ke dai ki na tsokana ta kawai. Na san manufar ki – ke dai in canja zuwa Besfa. To ba komai Tsahare ta. In da rai da rabo, ko? Wata rana sai ki ga mutum a mota ma.”
“Haka ne. Allah ya ba mu sa’a.”
Su ka kalli juna. Tsahare ta yi masa murmushi, shi kuma ya ci gaba da kallon ta babu }iftawa har abin ya so ya ba ta kunya.
“Lafiya ka ke kallo na haka kamar maye? To, kurwa ta kur!”
Tanimu ya yi murmushi, ya ce, “Ai ni da maye ne, ke zan fara cinyewa – don kada in ta~a rabuwa da ke. Kin ga idan kin shiga cikin jinni na, ai shikenan kullum mu na tare kenan.”
“To ai kuma za ka daina gani na kenan.”
Tanimu ya ce, “Wai yau me za ki dafa mana ne – abincin dare?”
Ta ce, “Me ka ke so? Na san dai kai sarkin cin tuwo ne.”
“E, haka ne. Kin san Shata ya ce sai wawa sai mahaukaci ke raina mafari. Tuwo da hura kuwa su ne mafarin Bahaushe.”
“Ka na nufin dai a yi tuwon, ko?”
Ya girgiza kai, ya ce, “Rai dangin goro ne, ban iska ya ke so. Gara mu sauya abinci. Me zai hana ki yi mana faten tsaki, ki toya mashi man ja, kuma ki dama mana kunun tsamiya mai ]auke da kanumfari?”
Tsahare ta ce, “An gama! Ni ma ina marmarin kunu wallahi. Amma kuma kai ma ka taho mana da gasasshiyar kaza don mu kwantar da yawun marmari.”
“Da kyau, uwar ‘yan biyu! Ai da ma na san a rina, an saci zanin mahaukaciya! Na san sai kin ce a zo maki da nama.”
“{warai, ai ba laifi ba ne. Ka san mai ciki da kwa]ayi… Ka dai bi a hankali, kada wata rana in cinye ka kamar mayya!”
“Wa ma ya sani ko mayyar ce na auro? Wannan cin nama haka?”
“Ai mayu ba sa cin nama, malam, sai dai kurwa.”
“Way a gaya maki? Kul, kada mayen gaske ya ji ki! To, zan zo da kazar, ke kuma ki yi naki aikin. Kin ji ko, uwar ‘yan biyu?”
“To. Amma ka san na ce ka daina kira na haka, ko? Wa ke son ya haifi ‘yan biyu yanzu? [ayan ma ya ishe ni.”
“Ai Allah ke bayarwa. Kuma dai wannan ciki naki, in ba ‘yan biyu ba ne a cikin shi to menene? Abu kamar kin ha]iyi duro!”
Tsahare ta tum~una fuska, ta ce, “A’a, ba duro na ha]iya ba, mota ce tanka mai taya sha takwas!”
Fa]in haka ke da wuya sai duk suka bushe da dariya.
Da su ka gama, Tsahare ta dube shi, ta ce, “Tanimu, don Allah ka yi min wani al}awari.”
Ya gyara zama a kan mashin, ya tambaye ta cikin damuwa, “Al}awarin me?”
Ta ce, “Al}awarin za ka dawo da wuri domin mu ci abincin dare tare.”
Dariya ta kama shi, har ya na }walla. Ya na sharewa, ya ce, “Haba Tsaharatu! Ke ni fa har na ]auka wata babbar magana ce? Wannan ma har wani abin yi ma al}awari ne?”
Ta ce, “Ni dai ka yi min. Domin na san ka, kullum sai ka ce za ka dawo da wuri, amma ba na ganin ka sai tsakar dare. Abincin ma ba ka ci, said a safe a yi maka ]umame. Har ina tunanin ko wata ta sace maka zuciya ne.”
Ya ce, “Sam, ba haka ba ne. Ai na ce maki ba za ki ta~a samun kishiya daga gare ni ba. Haba, ni da na samu mace ]aya tangan da goma! To, in dai batun al}awari ne, na yi maki. Zan dawo da magariba. Ki shirya komai. Ai ba ki sani ba ma, sabon amarci za mu bu]e!”
Cikin farin ciki, ta ce, “Alhamdu lillahi. Ni kuma zan jira ka. Zan shirya komai kafin ka zo. Kuma wallahi ba zan ci abinci na ba sai ka zo mu ci tare, ka ji ko?”
Tanimu ya amsa, “Kalas! Na ji, na yarda.”
Ta ka]a kai, ta ce, “Sai ka yi }o}ari ka tafi, kada Alhaji ya ritsa da kai ka ce mashi ni ce na ri}e ka a gida!”
Daga nan su ka yi sallama. Tsahare ta je get ]in gidan, ta bu]e masa. Ya tada babur ]in sa, ya fice daga gidan tare da ]aga mata hannu. Bayan ya tafi, ta rufe get ]in, ta koma falon ta.

Za mu ci gaba a makon gobe insha Allah

4 comments:

Anonymous said...

Dear Ibrahim,

thank you for publishing your thoughts in Hausa. I am not a Hausa native speaker myself, but I have studied and like the language and I am always looking for interesting reading matter in Hausa.

Maybe you could consider using a different system to represent the "hooked letters".

myabubakar said...

Hi Sheme. Its nice to come across your blog. This is my blog.
more to say later

محمد مصطفى الشيخ محمد برنوما said...

i always enjoy reading blogs articles in hausa as my mother tongue i love those nice people publishing in it
god bless you

Anonymous said...

cheap wow power leveling buy wow gold cheapest wow power leveling CHEAP wow gold BUY power leveling CHEAPEST wow powerleveling
wow goldwow goldwow goldwow goldweiwei