Friday 4 April 2008

Daga 'Mace Mutum,' Sai Me?


Hira da Rahma A. Majid a mujallar Fim ta watan
Afrilu 2008, shafi na 60 - 61

Daga 'Mace Mutum,' Sai Me?

Daga IRO MAMMAN

Fitacciyar marubuciya Rahma A. Majid ta yi bayani kan sakamakon da ta gani bayan fitar jibgegen littafin ta a kasuwa. Ina ta sa gaba yanzu?

KWANAN nan ne fitacciyar marubuciyar nan Rahma A. Majid ta fitar da sabon littafin ta mai suna ‘Mace Mutum.’ K'aton littafi ne, domin rabon ka da ganin littafin hikaya mai yawan shafukan sa tun ‘K'arshen Alewa K'asa’ na marigayi Bature Gagare; shafi 520 ne, don haka ya ma fi ‘K'arshen Alewa’ yawa kenan.

Jigon littafin shi ne yadda ba a yi wa mata adalci a zamantakewar yau da kulluma a k'asar Hausa, saboda irin danniyar da maza ke yi musu.

Mun tattauna da marubuciyar kan littafin, da kuma inda ta sa gaba bayan fitar sa. Bismillan ku:



Kwanan nan littafin ki, ‘Mace Mutum,’ ya shiga duniya. Yaya ki ka ga karbuwar sa a wurin jama’a?

Alhamdulillah washukuralillah!!! Gaskiya batun karb'uwar wannan littafi sai godiya ga Maiduka, domin kamar yadda mu ka zata littafi mai yawan shafuka da yawan farashi kasuwar sa na tafiya ne a hankali, don haka ne ma a lokacin da na ke ganawa da wasu cikin dilolin mu na yi ta yi musu matashiya kan yadda za su jure wa wannan kasuwa mai tafiyar hawainiya. Amma cikin ikon Allah sai ga shi littafi a satin farko an soma neman sa a wasu guraren ya k'are. Sannan ina mai tabbatar maka da har yau bai gama karad'e inda ake neman sa ba saboda saurin tafiyar da ya yi a wasu wuraren da aka fara k'addamar da shi. Gaskiya makaranta sun yi rawar gani, sai godiya gare su da Ubangijin mu.

Ba a taba yin littafin hikaya na Hausa wanda farashin sa ya kai yawan na ‘Mace Mutum’ ba. To akwai tsoro a zukatun marubutan Hausa cewa wai idan marubuci ya "tsuga" kudi, ba za a saya ba. Ke ya abin ya shafe ki?

Kamar yadda na gaya maka a tambayar farko, ni da kai na ina cikin masu irin wannan tsoro, musamman ma da na lura da cewa mafiya yawan makaranta matan cikin gida ne sannan ga littafin ya yi kud'in wata atamfar biki, don haka na zaci kowa ya zo saye zai ce ya yi tsada, amma sai ga shi mafi yawa na cewa ai ma ya yi arha. Watak'ila wannan ne ya sanya wasu dilolin su ka dinga zabga kud'i bayan da su ka fahimci cewa za a saye shi a ko nawa ne. Don zan iya tunawa cewa an kawo min kukan an sayi littafin a Gombe kan farashi N1,500, sab'anin kud'in-bai-d'aya da ake sayar da shi N820.

Jigon littafin ya ta’allaka ne kan wahalhalun da mata ke sha a kauyuka da birane, ta yadda har akan ga cewa kamar mace ba bil’adama ba ce. Ki na ganin matan Hausawa sun shirya karbar wannan sakon?

Eh, daga yadda na ke hange ko fata, matan mu na Hausawa za su so karb'ar sak'on littafin, sai dai ba zan yi wa kai na alk'awarin cin karo da zafafan k'alubale ba, ba ma daga maza ba har matan da ake yi wa yak'in. Domin bayan na kammala rubutun ‘Mace Mutum,’ na lura da cewa akwai dubban mata da su ka fi gwammace wa rayuwar da mu ke yak'a fiye da wadda mu ke son ganin su a ciki. Wannan ba zai rasa nasaba da imanin su kan maganar nan mai cewa bayan wuya sai daK'i ba. Don haka ‘Mace Mutum’ na iya samun karb'uwa ko tirjiya daga waK'anda ake abin domin su.

Shin ki na ganin cewa kin fice daga kangin "adabin kasuwar Kano", ko har yanzu ki na ciki?

Da cewa ka yi na fita ko ina cikin adabin kasuwar Kano? da na ce ina ciki, domin ba na k'yamar adabin wanda shi ya haife ni ni da alk'alami na. Amma tun da k'angi ka ce, ina jin zan iya cewa na kama hanyar fita daga k'angin ci-baya da adabin namu ke fama da shi. Kamar yadda hasashe ya nuna, marubuta da dama sun yunk'uro don ficewa daga wannan k'angi. Kada ka manta, daga cikin littattafan da su ka ci gasar Abuja akwai adabin kasuwar Kano, wanda hakan ba k'aramin ci-gaba ba ne ga wannan adabi ba. Don haka ina jin wannan adabi da kan sa ya na jajibirin ficewa daga k'angin da ya sami kan sa ba ma mu ’ya’yan sa kawai ba.

Shin wannan littafi kirkira ne gaba daya ko kuwa akwai wasu sassa da ki ka dauko kai-tsaye daga rayuwar zahiri taki ko ta wasu mutane da ki ka yi bincike a kan su?

Labarin ‘Mace Mutum’ k'agagge ne, sai dai halin da mata ke ciki a wannan littafi gaskiya ne, don haka labarin na iya yin saurin kama da rayuwar wata ko wasu gungun mata.

Littafin ya fito da kurakurai na dab’i (printing) inda za ki ga wasu shafukan babu rubutu ko kuma wasu kwafen littafin ba a yanke gefe-gefen ba. Me ya faru?

Lallai an sami matsaloli wajen aikin wannan littafi. Ina ga wannan bai zai rasa nasaba da gaggawar da mu ka yi a kusan k'arshen aikin ba, domin a yayin da mu ka zak'u da mu biya hak'k'in masu jiran wannan littafi da su ke ta sauraro su na k'orafi kan daK'ewar sa bai je kasuwa ba. Amma cikin ikon Allah mun shawo kan kashi 90% na wannan matsala domin mun bi kasuwa mun karb'i mafi akasarin wannan littattafai da su ka sami matsala don a maida su kamfani a sake masu aiki. A halin yanzu akwai ak'alla kwafe 288 da aka dawo mana da su don mu sake maida su cikin mahaifiya.

Bayan ‘Mace Mutum,’ sai me kuma zai biyo baya? A wata hira da ki ka taba yi da mujallar Fim a cikin 2005 kin nuna cewa za ki rika fitar da littafi makamancin wannan akalla guda daya a shekara. To za mu sa ran ganin wani littafin nan da 2009 kenan?

Lallai zan iya tuna wannan alk'awari nawa a can baya, kuma ina da niyyar tabbatar da shi, sai dai kowa na nasa Allah na nasa. Dubi ‘Mace Mutum,’ tun 2005 ake fama da matsalar da ba ta fi k'arfin mu ba, amma har sai da ya kai 2008. Don haka in har na kasa cika wannan alk'awari sai na yi fatan samun uzuri daga makaranta don sanin ba da niyya ba ne.

Wane kira za ki yi ga marubuta kan batun yin littafi mai inganci, mai yawan shafuka, mai jigon da ba na soyayya ba, da sauran su?

A kullum kira na ga takwarori na kuma ’yan’uwa na marubuta, shi ne mu daina tunanin abin da za mu kashe da wanda za mu samu a wannan aiki, domin muddin za mu rik'e wannan tunani ba za mu iya yin aiki mai inganci ba. A k'asa irin tamu babu abu mai riba kamar abu mara inganci, don haka in fa mu ka zab'i inganci dole mu ajiye tunanin riba, ita ce kan sanya mu jin babu wani jigo ga labari sai wanda kwastamomin mu su ka zab'a. Sannan mu tuna iya zubi da salo wajen bayar da labari na iya jan hankalin makaranci ba sai jigo ba. Don haka kada mu ji tsoron zab'en jigo kowane iri muddin mun iya zubi da salo.

Sannan batun yawan shafuka, kada wani ya ga ‘Mace Mutum’ ya je ya takura kan sa da cewa sai ya had'a labari mai yawa ko da ba ma’ana sai surutu da maimaici. Kada mu manta, ingancin labari da ma’ana ya fi yawan shafuka amfani.

Don haka kira na a nan shi ne in za a yi littafi mai yawan shafukan a tabbatar yawan mai amfani ne ba haihuwar yuyuyu ba. Sannan mu sani, akwai bambanci tsakanin yawan labari mai amfani da k'arami mara amfani. Akwai wasu littattafai da mu ke yi da ba su fi shafi 40 ba, ba wai don labarin ba zai iya kaiwa shafi 200 ko 300 in an bud'a shi ba sai don tsoron yawan kud'in aiki da k'arancin riba. Mu tuna, bai wa labarin hak'k'in sa na cika shi shi ma wata riba ce. Allah ya sa mu dace.

--------------------

An taba buga cikakkiyar hira da Rahma A. Majid kan littafin ‘Mace Mutum’ a mujallar Fim ta Nuwamba da ta Disamba 2005.

Za a iya tuntubar marubuciyar ta i-mel: