Sunday 24 June 2018

Waƙar 'Baƙar Rama' ta Haruna Uji


Haruna Uji ya na kaɗa gurmin sa
Na rubuta wannan waƙar daga wani faifai na Alhaji Haruna Uji a ranar 21 ga Mayu, 2015. A lura da cewar da yake Uji ya rera wannan waƙar a lokuta daban-daban, mai yiwuwa ne ka ji wani samfur na waƙar wanda ya bambanta da wannan da na rubuto.

Waƙar "Baƙar Rama" dai Haruna Uji ya yi wa matar sa Tasalla ne, don nuna shauƙin soyayya da ke tsakanin su. Bismilla:

*

 Ruwa isa gayya, Baƙar Rama,
Ruwa isa gayya, ya ki!
Allah Sarki, Baƙar Rama,
Ke 'yar masara mai yawan zani,
Sannu da rana, Tasalla!

Na kaɗa gangar Baƙar Rama
Wa'yansu mutane su na faɗi: "Baƙar Rama ko ba mutum ba ce?!"
Na ce musu, "A'a, ku bar faɗi, Bakar Rama amma mutum ta ke."

Ai sai su ka ce min: "Haru Uji, Baƙar Rama in dai mutum ta ke,
Ka yi mana taɗin Baƙar Rama."
Sai na ce "Na yarda!"

Sai ku matso zan gaya muku,
Na farko zancen Baƙar Rama,
Mai son 'yar nan Baƙar Rama,
In gan shi ga kogo kamar guza kamar gansheƙa, ya ja ciki,
Ta ce ba ta so, ba za ta ba.

Ina mai son ki?
In kai shi ga kogi,
Iy yi nutso ya ɗebo yashi,
Sai ya ƙirge yashi,
Baƙar Rama ta ce ba ta so, ba za ta ba!

In ya haɗa wannan,
In kai shi ga rairai ya tandara,
Ta ce ba ta so!
Ya hau kan rimi,
Sai ya kere rimi, ya faɗi da ƙirji,
Baƙar Rama ta ce ba ta so, ba za ta ba!

Mai son 'yar nan Baƙar Rama,
Ya zabura sosai,
Ya je dawa ya samu giginya,
Ya hau giginya da baya,
Baƙar Rama ta ce ba ta so!

In ya haɗa wannan,
Ya zauna ya yi mata kukan wata bakwai da kwana hamsin,
Sai ta ce ba ta so, ba za ta ba.

Allah Sarki, Baƙar Rama!