Sunday, 29 June 2008

Saadou Bori, Popular Hausa Musician, Dies In Accident


Popular Hausa musician Saadou Bori is dead. He died in a tragic road accident on Thursday on his way from Maiduguri, Borno State, Nigeria, sources told me.

He was said to be about 50 years of age.

Bori, who hailed from Niger Republic, was a practitioner of Dango (Hausa spirit music) and trance-dancing. His best known songs, recorded together with another notable Nigerien artiste, Moussa Poussy, include "Toro," "Nabo Nabo", "Weino," "Gossi," "Gaweizo," "Gazera," "Dango," "Yallerou," "Bori," "Boudje," "Hadiza," and "Soyeya."

Many of these songs are played on radio stations in all Hausa-speaking areas in Nigeria.

Saadou Bori and Moussa Poussy are two singer-songwriters who worked together in Niger's national music school's house band, Takeda, and went on to bigger things in Abidjan, Cote d'Ivoire. Both have spiritual backgrounds, Djerma performer Poussy as the grandson of a traditional healer and Hausa-speaker Bori as a performer of Dango.

Their album, "Niamey Twice," is an international sensation. It combines the talents of the two popular musicians, both renowned performers of trance music and dance. With no domestic music industry to turn to, they joined forces and with a backing band featuring members of Saadou's band, Carnaval, travelled to Abidjan to record Niger's first international album.

In recent years, the late Saadou Bori had made Nigeria virtually his second home, performing at weddings and other engagements.

Information on his death is scanty, but a well-known Hausa movie singer, Mudassiru Kasim, who was Bori's associate, confirmed to me that Bori died on the road to Maiduguri, adding that he was buried in his home town of Maradi, Niger Republic, on Friday.

Kasim said he and some of his friends would travel to Niger yesterday in order to condole the family of the late musician.

(The above photograph shows Bori on the right, together with his boon-companion Moussa Poussy)

Wednesday, 25 June 2008

Bayan Shekara 27: Me Ya Sa Aka Manta Da Abubakar Imam?


A bana, littafin Magana Jari Ce, wanda Alhaji Abubakar Imam ya rubuta, ya cika shekara 80 cif da wallafawa. Sannan a jiya Alhamis, 19 ga Yuni, 2008 Imam, wanda shi ne kakan marubutan Hausa, ya cika shekara 27 da rasuwa. Wannan sharhin ya na yi mana hannun-ka-mai-sanda kan yadda mutane su ka yi watsi da juyayin Imam da ayyukan sa, ciki kuwa har da wad'anda nauyin yin ayyukan tunawa da Imam da karrama shi ya fi rataya a wuyan su.

Daga Ibrahim Sheme

A wata ranar Asabar a cikin shekara ta 2004, na yi wani sharhi kan marigayi Alhaji Abubakar Imam, ya fito a filn adabi na jaridar Weekly Trust, wanda na ke gabatarwa a lokacin. Sharhin, kwaskwarima ne na wani sharhin da na tab'a yi a Majalisar Marubuta ta Intanet, inda na nuna cewa ba a yi wa Alhaji Imam adalci ba wajen ayyukan tunawa da shi, musamman a hanyoyin sadarwa na zamani. Na yi nuni da cewa idan mutum ya yi amfani da na’urar Google ta intanet, zai gano cewa babu wurare da dama da aka ambaci wannan hazik'i, fasihi, kakan marubutan Hausa a intanet. Har na ce idan a misali ka kwatanta Imam da ni d'in nan Ibrahim Sheme, za ka taras da cewa an ambace ni a intanet sau ninkin baninkin fiye da Imam - ga shi kuwa ni ba kowan kowa ba ne a fagen adabin Hausa, idan ana maganar gagarau irin su Imam!
Na d'ora laifin a kan mutanen da ya kamata a ce sun karrama Imam, sun tabbatar da cewa ya na da cikakken wakilci a yanar gizo da duk wani dandali da ya kamata a ji amon sunan sa. Wad'annan mutane sun had'a da marubutan Hausa, da malaman makarantu tun daga firamare har zuwa jami’a, da su kan su iyalan marigayin.

Shi dai Imam, haifaffen Kagara ne a Jihar Neja. An haife shi a 1911. Asalin asalin sa Babarbare ne, amma kakan kakan sa ya yi hijira zuwa k'asar Kwantagora, daga nan ya tafi Sakkwato a zamanin Shehu Usmanu D'anfodiyo, ya zauna a k'ark'ashin Shehu. A can aka haifi mahaifin Imam, wato Malam Shehu Usman, wanda daga baya ya dawo Kagara bayan ya yi yawon malanta a k'asar Katsina da ta Kano.

Imam ya yi makaranta a Katsina, inda daga bisani ya zama malamin makaranta. A nan ne ya had'u da Dakta R.M. East, Baturen nan jami’in ilmi wanda ya jagorance shi wajen rubuta wasu daga cikin littattafan sa, ciki har da Magana Jari Ce da kuma K'aramin Sani K'uk'umi. Har ila yau Imam shi ne editan Hausa na farko na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo. Ya rasu a ranar Juma’a, 19 ga Yuni, 1981 a Zariya, ya na da shekara 70 a duniya. Ya bar matar sa d'aya, da ’ya’ya 14, da kuma jikoki 42.

Imam ya kasance jagaba a harkar rubuce-rubucen hikaya na Hausa, ta yadda a yau da wuya a ce ga wanda ya fi shi. To amma ban da rubutu, ya na daga cikin ’yan kishin k'asa na farko da su ka nemi mulkin kan Nijeriya daga hannun Turawa ’yan mulkin mallaka. Haka kuma ya taka rawa k'warai a harkokin addinin Musulunci.

Rasuwar Imam ta gigita jama’a, musamman saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a fagage da dama na rayuwar jama’ar Arewa. Tun daga lokacin da ya mutu ake ta tunanin hanyoyin da za a bi a karrama shi, a rik'a tunawa da shi a kai a kai. Abin mamaki, har yanzu ba a gama tunanin ba, don haka ba a yi wani abin kirki a kan haka d'in ba - shekaru 27 bayan rasuwar sa!

Sakamakon rubutun da na yi a Weekly Trust, wanda babban k'alubale ne a gare mu duka mu masu hank'oron son Imam, an samu yunk'uri mai alfanu daga wasu sassa. A Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi wuf ya k'irk'iri dandalin tattaunawa (chat group) kan Imam a intanet, wanda ya sa wa suna www.abubakarimam@yahoogroups.com. An samu membobi a wannan dandali, to amma yawan su bai taka kara ya karya ba.

Yunk'uri mafi girma da aka samu na karrama Imam ya fito ne daga iyalan sa. Sun kira mutanen da abin ya shafa, ciki har da Farfesa Abdalla da Dakta Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Usmanu D'anfodiyo da kuma ni. Shi Malumfashi, ya yi digirin sa na dakta ne a kan rubuce-rubucen Imam kuma tun tuni ya nad'a kan sa Sarkin Yak'in Imam a fagage da dama. To amma a yayin da mu ka amsa gayyatar iyalan Imam mu ka je Zariya wurin taro na farko don tattauna hanyoyin da za a bi a karrama Imam, a ranar 29 ga Agusta, 2004, Malumfashi k'in zuwa ya yi. Bai kuma aika da sak'on uzuri ba. Zargin da mu ke da shi shi ne, adawar da ya ke yi da wasu daga cikin mu ce ta hana shi zuwa. A gani na, ya na ganin cewa tun da ba shawarar sa ba ce tun farko, ba zai shiga ciki ba. Ka ji halin Bahaushe – mai ban haushi, na Tanko mai kan bashi!

Duk da haka, taron ya yi albarka. Akwai dattawa da dama a taron, kuma yawancin ’ya’yan Imam maza, da wasu jikokin sa, duk sun halarta. An tattauna kan hanyoyin da za a bi a karrama marubucin, musamman ma yadda za a sa a rik'a jin amon sunan sa a k'asar nan kwatankwacin yadda ake jin na gwaraza irin su Janar Murtala da Janar Yar’Adua.

Bayan wannan taron, an sake yin wasu tarurrukan a wasu ranakun. A k'arshe, an yi abubuwa biyu. Na d'aya, an gina gidan yana a intanet mai suna www.abubakarimam.com, wanda Dakta Haroun Adamu, mamallakin makarantar nan Zaria Academy, ya d'auki nauyin gina shi. Wani masanin intanet da bai dad'e da dawowa daga Amerika ba inda ya yi tsawon shekaru, wato Malam Salisu U. D'anyaro, shi ya yi gidan yanar kuma ya ke gudanar da ita. Na biyu, an kafa cibiyar tunawa da Imam, wadda a Turance za a iya kiran ta Abubakar Imam Documentation Centre. Ta na cikin wani gidan sama da ke kallon randabawul na Babban Dodo a Zariya.

A yayin da gidan yanar ya ke d'auke da tarihin Imam da rubuce-rubucen sa, a ita cibiyar kuma an adana wasu kayan tarihi da su ka jib'inci marubucin, ciki har da samfurin rubutun sa na hannu, da takardun sa, da littattafan sa, da lambon girma da ya samu, da hotunan sa, kai har ma da rigunan sa!

Wad'annan abubuwa uku, babu shakka, manyan hanyoyi ne na karrama Imam. To amma a yau, idan na waiwaya baya, sai in ga ai ba su isa ba. Kuma ma tuni an yi watsi da su. Na farko, dandalin tattaunawar da Malam Abdalla ya bud'e a intanet, bai hab'aka ba. Mutane k'alilan ne a ciki. Kuma babu sak'wanni a kai a kai a ciki. Don haka dandalin bai cimma nasarar bud'e shi. Mai yiwuwa dalilin shi ne saboda Malam Abdalla ya gina wani dandalin tun da fari mai suna www.marubuta@yahoogroups.com wanda ya shafe na Imam d'in. Yawancin marubuta ma ba su san da dandalin Imam d'in ba.
Ta b'angaren gidan yanar da Malam Salisu D'anyaro ke gudanarwa kuwa, ya yi kyau k'warai, domin hatta littattafan Imam za ka iya sauko da su kyauta. Sai ai ya kamata a ce ana saka sababbin abubuwa a cikin sa, kamar labaran marubuta da mak'aloli kan harkar rubutun Hausa. Kafin a yi hakan tilas sai an samu ’yan rahoto ko marubuta da za su rik'a aikawa da sak'wannin da za a rubuta.

Haka kuma ya dace a ga hotuna da bayanai daban-daban a ciki wad'anda su ka danganci Imam da iyalan sa har da mu ’yan amshi.

Ban da haka, shin har an k'ure tunani kan Imam daga yin ’yan wad'annan abubuwan kenan? To ai ba a ma fara yak'in ba! Dalili shi ne har yanzu ba a yi wa Imam karramawar da ta dace da mutum irin sa ba, wanda ya bauta wa k'asa ta hanyoyin da Allah ya hore masa - kama daga kaifin alk'amin sa har zuwa fagen siyasa inda ya taimaka wajen k'wato wa Nijeriya ’yanci daga hannun ’yan mallaka. Domin fa Imam ba marubuci kad'ai ba ne, a’a d'an siyasa ne na sahun gaba, kuma malamin addini ne wanda ya taimaka gaya wajen fito da al’umma daga duhun jahilci. Kuma d'an jarida ne wanda ya gina dandamalin da mu jikokin sa mu ke cin abinci a kai a yau.

Akwai hanyoyi da dama da za a bi don inganta tunanin mu kan wannan bawan Allah. Na d'aya, a fitar da rana d'aya a kowace shekara don yin laccoci kan rayuwar Imam da ayyukan sa. Wato dai kamar yadda ake yi kan su Murtala da Yar’adua da ire-iren su. A taron, za a dubi ayyukan da ya yi, a d'ora su bisa jigo ko sikelin da aka zab'a a shekarar da ake laccar; misali: rubutun hikaya, aikin hajji, siyasa, karatun boko da na addini, aikin jarida, wallafa, ds. Wannan hak'k'i ne na iyalan sa da sauran masoyan sa; idan sun yi jagora, sai abin ya yiwu.

Na biyu, ya kamata a rik'a shirya laccoci kan rubuce-rubucen Imam, wanda su kan su marubutan Hausa ya dace su yi. Misali, a yau d'in nan a K'ungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) ta Turanci, babu b'ab'atun da ake yi sai na karrama marubucin nan d'an k'abilar Ibo, Farfesa Chinua Achebe, wanda a bana gwarzon littafin sa Things Fall Apart ya cika shekara 50 cur da bugawa. To, mu mu na ina Magana Jari Ce littafi na 1 ya cika shekara 69 da bugawa a cikin 2007? Ko ‘ihn’ ban ce su Malumfashi sun furta ba, ballantana Allah-maimaita-mana! To, ba a makara ba, domin littafi na 2 da na 3 na Magana Jari Ce an buga su ne a cikin 1938 - wato shekara 70 cur a yau. A cewar Dakta R.M. East, wanda ya jagoranci wallafa littafin, an buga littafin ne a wajajen watan Satumba 1938. Kun ga kenan akwai damar a yi wani abu, ko da na rana d'aya ne, don tunawa da wallafar littafin da aka yi.

Na uku, ya kamata a gina gida na musamman wanda zai d'auki Cibiyar Tunawa da Abubakar Imam kamar yadda ake da Shehu Musa Yar’Adua Centre a Abuja ko Murtala Muhammed Foundation a Legas da Abuja. Idan iyalan Imam sun ga cewa ba su da halin yin hakan, to su rungumi gwamnati, ko da ta Kaduna ce, domin a taru a san yadda za a fitar da jaki daga duma. A tunani na, wannan ba abu ba ne da zai gagare su.
Na hud'u, a fito da babbar gasa ta rubutun littattafan hikaya masu ma’ana na Hausa ta shekara-shekara da sunan Imam. A rik'a kafa kwamiti da zai duba littattafan da su ka shiga gasar don fidda zakarun da su ka cika k'a’idojin da gasar ta tanada. Yin haka zai k'ara saka juyayin Imam a zukatan marubuta da manazarta. Idan an tuna, babbar gasar rubutun littattafan Hausa a yau ita ce ta tunawa da Injiniya Bashir K'araye wadda maid'akin sa Hajiya Bilkisu ta sa. Gasar ta samu nasara. An yi ta farko a bara, kuma har an fara ta bana a yanzu. Wannan gasa ta Imam za a iya bai wa k'ungiyar ANA ta k'asa ita domin ta rik'a gudanarwa.

Na biyar, a inganta gidan yanar www.abubakarimam.com, ta yadda zai k'unshi abubuwan da bai da su a yanzu.

Na shida, ina labarin littafin tarihin rayuwar Imam na Hausa da Malumfashi ya ce ya na yi ya kwana? Shekaru kamar biyar da su ka wuce, Malumfashi ya fad'a mani cewa har ya k'are aikin, wai “zai fito kwanan nan.” To, amma shiru ka ke ji, wai malam ya cinye shirwa! Ya zuwa yanzu, tarihin Imam a littafi guda d'aya ne, wato Abubakar Imam Memoirs wanda surukin sa marigayi Dakta Abdurrahman Mora ya fito da shi a cikin 1989. Wannan littafi shi kad'ai ne madgora wajen samun ingantaccen tarihin Imam, amma da Turanci aka yi shi! Kuma ba “kammalalle” ba ne, domin babu bayanai kan iyalan Imam a ciki, da ya ke shi Imam d'in ne ya rubuta shi, kuma ya fi maida hankali kan ayyukan sa na harkokin addini da na siyasa fiye da na adabi. In dai ba Malumfashi ya lak'ume shirwa ba ne, to don Allah ya fito mana da wancan littafin da ya ke magana. Mun gaji da gafara sa, ba mu ga k'aho ba. Idan kuma shi ba zai iya ba, to ya ba yara wuri, su su yi!

Na bakwai, malamai masu sha’awar Imam tare da nazarin ayyukan sa su cire gasa/kishi//hassada/gaba da ke cikin ran su, su had'a kai, su taru su fito da hanyoyin karrama Imam da su ka dace. Al’ummomi daban-daban a duk duniya su kan yi wasu ayyuka na musamman don tunawa da gwarazan su, to amma mu “ninanci” (kamar yadda Malam Abdalla ke cewa) ya yi mana tarnak'i. “In ba ni na yi abu ba, babu wanda ya isa ya yi shi,” ko kuma “Wane ai ba fagen nazarin sa ba ne wannan, da har zai zo ya na yi mana shiga-sharo-ba-shanu.”

Mu sani cewa idan fa ba mu karrama gwarzayen mu da kan mu ba, babu wanda zai karrama ma mana su. Su dai sun taka rawar su sun tafi, sun bar mu a fagen. Don haka, hak'k'in tunawa da su ya rataya a wuyan mu, ba a wuyan kowa ba. Kamar yadda marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ya tab'a fad'a, idan har ba mu buga tambarin kirakin kan mu ba, babu wani bare da zai zo ya buga mana shi. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa!

-----
An buga wannan sharhin a jaridar LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'a, 20 ga Yuni 2008 makon jiya

Monday, 9 June 2008

HIRA DA HAFSATU ABDULWAHEED

Gwagwarmayar jikanyar Mujaddadi a fagen rubutu

HIRA DA HAFSATU ABDULWAHEED

Macen da ta fara rubuta littafin hikaya a Arewa, wato HAJIYA HAFSATU AHMAD ABDULWAHEED, ta samu karramawa ta musamman daga {ungiyar Marubuta ta Nijeriya. Shin yaya ta ji a ran ta? Kuma ina ta sa gaba yanzu?


Daga IBRAHIM SHEME

HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafi aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, So Aljannar Duniya, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wad'anda ba su fito ba, kuma ta dad'e ta na fad'i-tashin ganin yadda littattafan ta za su fito, amma rashin kud'i ya hana.

Kwanan nan, abubuwa biyu sun faru ga Hajiyar. Na farko, ana nan ana shirin fito da wasu daga cikin littattafan ta, ciki har da wani na gajerun k'irk'irarrun labarai. Na biyu, lokacin da aka yi wani gagarumin bikin karrama marubutan Arewa a Minna, Jihar neja, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin marubutan Hausa da aka karrama da kyautar lambar girma.

Ba wannan ba ne karo na farko da na yi hira da Hajiyar, domin idan kun tuna a ‘yan shekarun baya mun tab'a kawo muku wata hira da ita. A wannan karon, mun tattauna ne kan wad'annan abubuwa biyu da su ka faru gare ta, wad'anda duk na alheri ne.

Wani abu da ya kamata ku sani shi ne, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin manyan mutanen k'asar nan. Na farko, ita jinin Mujaddadi Shehu Usmanu D'anfodiyo ce. A Jihar Zamfara kuma, fitacciyar ‘yar siyasa ce, domin a zab'en 2003 da aka yi, ta yi takarar zama Gwamnar jihar. Ta na da ‘ya’ya maza da mata; d'aya daga cikin ‘ya’yan ta, Hajiya K'adiria Ahmad, ta tab'a aiki a gidan rediyon BBC a London, yanzu kuma babbar ma’aikaciya ce a wani kamfanin kula da filayen jiragen sama a Legas. Haka kuma wata d'iyar ta Hajiya Hafsatu, wato Hajiya Asiya, ta na auren tsohon Ministan Abuja, Malam Nasir El-Rufa’i. Hasali ma dai, mun yi wannan tattaunawar ne da ita a gidan shi Malam Nasir da ke unguwar Jabi, a Abuja, kwana d'aya bayan an karrama ta. To bugu da k'ari kuma Hajiya Hafsatu ta kafa tarihin kasancewa mace ta farko da ta wallafa littafin hikaya a Arewa.

Ran ki ya dad'e, ki na daga cikin marubuta na Arewa wad'anda aka karrama su da lambar girma a Minna. Yaya ki ka ji a kan wannan karramawa da aka yi maki?
Alhamdu lillahi, na ji dad'i sosai. Sai dai bak'in ciki na kawai shi ne, uba na da uwa ta da miji na ba su da rai, balle su san abin da na samu. Amma murna kam na yi murna k'warai da gaske. Alhamdu lillahi.

Wannan shi ne karo na farko da aka tab'a karrama ki a kan harkar rubutu?
E, an tab'a yi a Kano, har su ka ba ni kamar lambar girma haka. Amma gaskiya na manta lokacin. Ina jin bara ne ko bara waccan.

Su waye su ka yi waccan karramawar?
Wata k'ungiya ce ta matasa marubuta.

Yaya ki ke ganin batun karrama marubuta, wanda ba a cika yi ba, yanzu ga shi ana yi? A farkon shekerar nan an yi a Abuja, sai kuma ga shi an yi a Minna. Shin wannan ya fara sauya tunanin mutane ne game da marubuta?
Ina ganin ’yan Arewa sun fara gane muhimmancin marubutan su. Ka san a da mutanen mu ba su damu da marubuta ba, musamman ma dai mata, ba a cika gane muhimmancin mu sosai ba, saboda an d'auka rubuce-rubucen mu shirme ne; na soyayya kawai. To, ina ji yanzu lokaci ya zo da aka soma gane muhimmancin mu. Saboda haka aka k'irk'iro wannan. Ya yi daidai kuma ya kamata a ci gaba da yin haka d'in.

A wurin bikin wannan karramawar a Minna, lokacin da ake karanta tak'aitaccen tarihin ki, an nuna cewa ke jikanya ce ko jinin Mujaddadi Shehu Usman D'anfodiyo ce. Mutane za su so ki yi k'arin bayani a kan wannan salsala taki.
To, ni dai sunan uba na Alhaji Abubakar Garba, sunan baban sa Sa’idu. Sa’idu kuma Hayatu ne ya haife shi. Hayatu kuma Sa’idu ne ya haife shi. To, shi kuma Sa’idu Muhamman Bello ne ya haife shi. Muhamman Bello kuma d'an Shehu Usmanu D'anfodiyo ne. Saboda haka ya zamana ni jikanyar jikanyar Shehu ce.

To, ko daga nan za ki ba mu tak'aitaccen tarihin ki?
An haife ni a 1952 a Kano, cikin unguwar K'ofar Mata, kuma na yi karatu a Shahuci da Provincial Girls School da Shekara Secondry School. Bayan nan na yi aure, inda miji na da shi ne manajan John Holt a Kano, daga baya aka mayar da shi Gusau. Bayan nan na yi ‘enrolling’ a Beneth Correspondence College, Landan, inda na d'an k'ok'arta na sami difloma. To, bayan nan dai na ci gaba da rubuce-rubuce. Na yi d'an aiki tak'aitacce a Kano, kamar part-time haka a gidan Rediyon Kano, amma ban dad'e ba, saboda ban dad'e da somawa ba na koma Gusau d'in. To, bayan nan dai sai rubuce-rubuce kawai da na ci gaba da yi a gida.

A bincike da na yi na fahimci cewa ke ce mace ta farko a Arewa da ta fara wallafa littafin k'irk'ira, wato littafin ki So Aljannar Duniya. Shin ki na da masaniyar cewa mata sun yi rubutu kafin ke ko kuwa a iyakar sanin ki ke ce ki ka fara d'in?
To, gaskiya ni dai ban tab'a ganin littafin wata ba ko da a jarida ko a wani guri da aka ce ta yi rubutu, sai da nawa ya fito tukunna. To, kuma bayan nawa ya fito - ina ji da kusan shekara 12 ma - na Zaynab Alk'ali ya fito. Koda ya ke akwai bambanci tsakanin nawa da ita, don ita na Turanci ta yi, ni kuwa da Hausa na yi.

Ko za ki gaya mana tarihin rubuta So Aljannar Duniya? Na farko ma dai menene ya fara ba ki tunanin rubuta littafi a lokacin da mata ba sa yi?
To, gaskiya a makarantar da na yi an d'an ba mu k'arfin gwiwar rubuta ’yan labarai a aji, har mu kan karb'i ’yan kyautuka a kai. A lokacin da na rubuta wannan ma da Turanci na soma rubuta shi duk da cewa Turancin nawa bai nuna ba, saboda yaya ta da ta auri Balaraben Libya ta sami ’yan tangard'od'i wajen dangi, haka da iyaye, wad'anda ba su so ta auri wani bak'o ba. To, daga baya kuma bayan na rubuta wannan sai na zo na auri wani Balaraben Yemen. To, sai labarin ya zamo kusan iri d'aya ne. To, da na rubuta shi da Turanci ban sami bugawa ba har lokacin da kamfanin NNPC Zaria ta yi gasa d'in nan, sai na fassara shi da Hausa na shiga gasar. A 1970 kenan. Na sami zuwa ta biyu a matsayi na na mace kad'ai da ta shiga wannan takara. To, bayan nan ne aka buga shi a 1972.

Tunda da Turanci ki ka fara rubuta shi, da yaya sunan sa?
Wallahi a lokacin ban sanya ma sa suna ba, don d'aya daga cikin abin da su ka hana ita yayar tawa a buga littafin shi ne mu na ta k'ok'arin mu ga wanne irin suna ya kamata a sanya masa. Saboda haka a lokacin ban sanya masa suna ba. (Murmushi) Amma dai Malam Sheme ya sanya masa suna a jarida (Weekly Trust); na gani. To, ina jin idan za mu yi shi da Turanci abin da za mu kira shi kenan.

Akwai yiwuwar za a fassara shi ne nan gaba?
E. An ma fassara shi da Turanci da Filatanci, kuma Jami’ar Usmanu D'anfodiyo, Sokoto, sun yi shi da Arabiyya. To, amma dai duk da haka har yanzu babu wanda aka rubuta a ciki.

Me ya tsayar da aikin bugun?
Gaskiya rashin kud'i ne a lokacin. Amma shi na Arabiyyar na sami wani mutumin Saudiyya da ya ce zai buga. To, amma abin bak'in ciki na yi gobara a 1995, saboda haka wannan kwafin na Arabiyya d'in ya k'one, kuma na yi k'ok'arin samun kwafi a hannun jami’ar ta Sokoto, don in kwafa, ban samu ba. Amma yanzu wani yaro ya sake buga shi da Larabci d'in. Saboda haka yanzu ina da rubutun hannu na Larabci d'in.

Labarin So Aljannar Duniya labari ne na Fulani, ku kuma ga shi a gari ku ke zaune. Me ya ba ki tunanin ki rubuta labarin Fulani maimakon labarin Hausawa wanda ki ka fi sabawa da shi?
To, ai ni Bafillatana ce, kuma duk da yake mu na cikin Hausawa, gidan mu ba mu zubar da yawancin al’adun mu na Fulani ba, domin ba a ma Hausa a gidan mu. Idan yaro ya tashi ba ya yin Hausa sai ya kai irin shekara bakwai d'in nan; sannan ya soma fita waje, ya koyi Hausa. Saboda haka ba wai wani abin a zo a gani ba ne don na rubuta al’adun mu.

Bayan wannan littafi sai aka d'auki tsawon lokaci ba ki yi wani littafin ba har zuwa lokacin da ki ka yi ’Yar Dubu Mai Tambotsai. Me ya sa aka sami wannan tsawon lokaci, kuma shekara nawa aka yi a wannan tsakanin?
Gaskiya ban san yawan shekarun ba, amma ina da littattafan da ma a rubuce; bugawa ne kawai ba a yi ba, saboda yanayin yadda babu kud'in da mutum zai buga d'in.

Wani abu da mu ka yi la’akari da shi shi ne, a matsayin ki na wacce ta soma rubuta littafin k'irk'ira a Arewa, sai ya kasance k'waya biyu kad'ai ki ka rubuta, ban da littattafan addini da mu ka san kin rubuta daga baya. Me ya sa ba ki rubuta littattafai da yawa ba kamar yadda sauran marubuta su kan yi?
(Murmushi) A’a! don littattafai ina da littattafai da dama; matsalar dai yadda na gaya maka ita ce bugawa. Domin ni ina ganin in buga su da k'ark'o sosai, wato abin da Bature ya ke cewa da quality, ya fi in buga su irin yadda sauran mutanen mu su ke yi da araha d'in nan su shiga kasuwa. To, shi ne kawai matsalar da ta hana ni bugawa da yawa, su fito. Amma akwai su nan a ajiye.

Ki na ta kukan rashin kud'i, amma wasu za su kalle ki a matsayin attajira, saboda ’ya’yan ki manya ne; an san su na auren manyan mutane da sauran su, kuma ke d'in ma dai babba ce. Anya za a yarda da maganar rashin kud'in nan, na dai a buga littafi?
A’a, to ai kamar nawa da na ke yi su na da tsada da yawa. Ka ga kamar wanda za a fitar wannan watan - Saba D'an Sababi - na k'irk'irarrun k'ananan labarai, abin da na biya mai bugawar shi ne N200,000 a kan kwafi 1,000 kacal. To, ka ga kuwa kud'in ba kad'an ba ne kenan. Kuma yara su na yin iyakar gwargwadon iyawar su, amma kowa ya na da iyali na kan su; ba za ka d'auki nauyin da ya fi k'arfin mutum ka d'ora masa ba, ballantana tun da baban su ya rasu. Kuma duk ba su dad'e da kawo k'arfi ba ai, saboda ba su dad'e da gama makaranta da kama aiki ba. To, ka ga akwai matsaloli da yawa a irin wannan.

Sannan kuma kallon kud'i da ake yi min, to alhamdu lillahi, sai in ce Allah ya k'ara min! Amma dai suna ne. Sarakuta kuma da masu kud'i, wannan ba hujja ba ce ta mutum ya na da shi. Domin sai surukin ya bayar sannan za ka karb'a. To, saboda haka ana dai k'ok'artawa. Yanzu dai mun yi da su za a tara duk ’yan rubuce-rubucen a tsinci wanda za a tsinta, su had'a kud'i su buga, wanda su ka ga ya dace da wanda za su iya.

Yanzu kin nuna mana cewa a a aiki a kan sabon littafin ki. Shi ma na k'irk'ira ne kenan?
E, na k'irk'ira ne. Wato na rubuta k'ananan labarai guda 46, wad'anda mu ka ce za mu kasa su kamar kashi uku ko hud'u. Ya danganta da dai yadda abin ya ke. To, kashi na farko ne zai fito; ya kamata ma a ce tun bara ya fito. To, harkar masu bugawa d'in ce…, sai dai ya yi min alk'awari, ya ce k'arshen watan nan idan Allah ya yarda zai fito. To, akwai kuma da yawa littattafan ai. Akwai biyu ma da Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano su ka d'auka za su buga, wanda na yi a kan mu’ujizojin Alk'ur’ani mai girma. Sannan akwai d'aya da na yi kan wani labari na gaskiya da na k'irk'iro na rubuta, na sanya masa suna Aibin Doka. To, sun d'auki wad'annan biyun za su buga.

Akwai yiwuwar ki rubuta wak'ok'i ko wasan kwaikwayo?
E to, biyu daga cikin k'ananan labaran nawa na mayar da su wasan kwaikwayo, sannan kuma ina da rubutattun wak'ok'i - amma na Turanci - da yawa, domin gaskiya na gwada rubutawa da Hausar, na kasa!

Ashe ki kan yi rubutu da Turanci? Amma har yanzu ba a ga ko guda d'aya ba!
Wallahi ina yi, amma duk dai harkar idan aka juya ta batun dai bugawa d'in ce. Har yanzu ban sami wanda zai d'auki nauyin bugawar ba. Ni kud'in ba su dame ni ba, amma dai a ce aikin ya fito, shi ne muhimmanci a wuri na, amma har yanzu ban sami wanda zai d'auki nauyin ba. Amma na Turancin dai a kwanan nan mu ka zauna da yara mu ka tsinci wad'anda za a buga d'in. To, ban san dai abin da su ke ciki ba dai yanzu, amma sun yi min alk'awarin za su buga, to amma ban san lokacin ba.

Me ya sa kamfanin Gaskiya Corporation ko NNPC Zaria ba su buga littattafan ki da yawa ba, musamman tunda a wancan lokacin su na cikin aikin buga littattafai da yawa, ba kamar yadda daga baya su ka durk'ushe ba?
Wallahi ni dai abin da su ka gaya min shi ne ba su da kud'i. Duk dai magana guda ce a lokacin da na kai musu nawa guda biyu, wad'anda har da ma na ‘Dare Dubu Da D'aya’ da na rubuta yadda yara za su iya karantawa, saboda na farkon nan bai kamata yara k'ananan su karanta shi ba. To, na rubuta daga na 1 zuwa na 5 kamar yadda aka yi shi na Hausa d'in nan. Har yanzu ma kwafin ya na hannun su, ba su dawo min da shi ba, don sun ce min yanzu su na ‘yan shirye-shiryen soma buge-bugen littattafai.

Yaya ki ke ganin harkar wallafa a Arewa?
To, gaskiya abin ya na da ciwo. Kuma duk a wasu taruka da aka yi na marubuta na kan bayar da shawarar cewa su kan su marubutan su na da laifi, saboda za a iya had'in gwiwa, a saka ‘yan kud'ad'e; kowa ya bayar da gudunmuwar sa, a had'a kud'in nan a ajiye. Idan marubuci ya rubuta littafi a duba, idan ya cancanta a buga shi, sai a d'auki nauyin bugawar. In ya so bayan an buga, an sayar ko an k'addamar, abin da aka sayar, sai a mayar a ajiye. Kuma nan gaba sai a sake samun wani ya yi. Amma duk shawarwarori na da na ke bayarwa, har yanzu babu wacce ta sami shiga.

Ita gwamnati da masu hannu da shuni fa?
To, gwamnati dai ba ta san da zaman marubuta ba, sai dai kwanan nan da ake ta abubuwan nan na ga gwamnatin Neja ta d'auki nauyi. To, kuma gwamnatin mu ma ta Jihar Zamfara ta yi alk'awarin za ta bud'e mana wani asusu wanda idan an yi littafi, a bincika shi a gani; idan ya cancanta, a buga. Sai mu yi fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da su.

Wane kira za ki yi ga marubuta wad'anda ke kasa fito da littattafan su, har ma wani sai ya yi fushi ya daina?
Bai kamata mutum ya yi fushi ya daina ba, domin idan Allah ya ba ka basira, ka daina amfani da ita, kamar ka yi masa butulci ne. Shi kuma rubutu ko da mutum ba shi da rai ya na da amfani. Kamar yadda mu ka ga littattafan Shehu da Asma’u d'aruruwan shekaru ga su nan yanzu ana morar su. Saboda haka kada mutum ya bari. Kada rashin bugawar nan ta karya masa gwiwa; ya yi ta rubutun ya na ajiyewa har Allah ya kawo wanda zai zo ya buga masa. Saboda komai ya na da lokaci. Idan lokacin abu bai yi ba, babu yadda za a yi ka tilasta lokacin ya yi.

To, Hajiya mun gode, k'warai.
To, madalla. Ni ma na gode.

(An ciro daga mujallar Fim ta watan Yuni 2008)

Sannu da zuwa, Talatu Danny!

A makon jiya na samu wasikar i-mel daga Malama Talatu Danny, inda ta gaya mani (tare da sauran abokan ta a Nijeriya) cewa ta iso Nijeriya daga Amurka. Talatu ta ce a yanzu ta na hutawa a gidan mahaifin ta a Jos kafin ta fantsama zuwa Kano da sauran garuruwa.

Talatu dai k'awar mu ce 'yar kasar Amurka da ke koyon Hausa da al'adun Hausawa, musamman a bangaren littattafai da finafinai. Ta kan kira kan ta daliba (ko da yake mu a wurin mu malama mu ka dauke ta!) a wata jami'a a Amurka.

Ta na da fitaccen gidan yana a intanet mai sunan ta, inda ta kan bayyana tunanin ta kan al'amura daban-daban da su ka shafi al'adun Afrika kamar yadda ake nuna su a hanyoyin sadarwa na zamani. Ta kan kuma bayyana labarai da tunani a kan rayuwar ita kan ta.

Talatu, ina yi maki barka da zuwa (ko in ce barka da dawowa) Nijeriya. Tare da fatan za ki ji dad'in wannan zaman, kuma ya kasance kin ci moriyar wannan balaguro da ki ka yi.

Lale marhabin!