Tuesday, 25 September 2007

Censoring Movies and Books in Kano


The following is text of a press briefing by the new, no-nonsense Executive Secretary of the Kano State Censorship Board, Malam Abubakar Rabo Abdulkarim (PICTURED HERE), on the additional guidelines for registration of film production companies, artistes, internet cafes and publishers/authors. It is the biggest censorship operation in Nigeria, couched in the spirit of the Kano State Government's Sharia programme under the state Governor, Malam Ibrahim Shekarau. Both the appointment of Malam Rabo and these new laws were inspired by the heated reaction of Hausawa to the sudden appearance of the Maryam Hiyana sex video. Read it, then we'll talk later!



PRESS STATEMENT BY THE EXECUTIVE SECRETARY, KANO STATE CENSORSHIP BOARD

The Board was established in the year 2001, under the State Censorship Board Law 2001. This law mandated the Board to oversee the activities of film making, cinemas, viewing centers, internet cafes and all literary works intended for sale, distribution or circulation in Kano State.

Sequel to the happenings in the film industry in the state and as well the current development in change of management of the state Censorship Board. More so, the establishment of the task force committee on sanitization of film industry in the state by his excellency the executive Governor, hitherto the following requirements are put in place for the registration of production companies, Artistes as well the censoring of films.

· Henceforth, no producer will go to location for activities without his script being approved by a recognised consultant and vetted by the Board.
· Production companies shall have a minimum of 2.5 million as working capital, confirmation could be obtained from Bank statement of account of the company.
· All members of the productions crew shall have a minimum qualification of Diploma or certificate in related field from a recognised institution.
· The Board would now censor both films on CDs and VHS Cassettes and all films marketed in the state.
· Artistes are now categorised into three, with respective minimum qualifications namely:
a) Artistes in training must have a minimum of primary School Certificate or its equivalent.
b) Median Artistes should ahave a minimum of Secondary School Certificate or its equivalent.
c) Star Artistes minimum of a Diploama, Degree or its equivalent.
· Henceforth the Board has cancelled singing and dancing of any kind in Hausa Film.
· The board is also revisiting the issue of marketing of film s in the state especially in the area of marketer-producer relationship.
· Kano State Association of Printers are to make sure that before they print aany book or poster meant for public use must have clearance from the board.

RAEQUIRMENTS FOR ESTABLISHING A FILM PRODUCTION STUDIO
Th requirments for establishing a film production studio in the state approved by the Board include the following for the mean time:

· A set of computer
· Pinacle Editing system.
· Monitors
· AVC/VCR Player.
· Digital Camera (HD with accessories)
· Two sets of earphones/Microphone.
· Tripod/Crane
· Professional Lights
· Reel.

TIME EXTENSION ON SUSPENSION OF ALL LOCATION ACTIVITIES

The state Censorship board re-iterates its position on all the measures being taken to sanitize the film in dustry and call on the entire stakeholders and the general public to support the task force set up by the state government for the purpose of sanity in the industry.
In this direction, the board hereby extends the period of the suspension imposed earlier. The suspension of all location activities is now from three months to six months effective from 13th August, 2007 toFebruary, 2008.
This policy would be vigourously monitored by the board to ensure stringent penalty imposition on defaulters.

REAVALIDATION FOR THE REGISTRATION OF PRODUCTION COMPANIES.
The wishes to this medium is to call on all proprietors of film production companies that are registered with the board to come forward for the revalidation of their registration on or before 30th November, 2007 and must fulfill the following requirements as stipulated by the law.

· Certificate of incorporation.
· Tax clearance Certificate for 3 years.
· Letter of in troduction from the Local Government Council where the production company is situated.
· Production Company shall employ the service of a film/Video Production Consultant.
a) Such Consultant shall be qualified from a recognised film institute within Nigeria or abroad.
b) Scuh Consultant shall have a working experience of Not less thatn 4 years in the field of porduction.

· All film production companies shall furnish their studios with the necessary facilities in accordance with the broadacasting standards or its equivalent.
· Production companies shall ensure that all technical production crew are registered members of Motion Pictures Practitioners Association of NIgeria (MOPPAN)
· Production com pany should have a clear office identification address.
· Must have a permanent office secretary.
· Production companies must register with Ministry of Commerce, Industry and Co-operatives Kano.
· Production companies must ensure free office environment.
· The aforementioned guidelines are subject to review, depending on monitoring circumstances.

CONDITIONS FOR LITERARY WORKS
In line with the law that established this board as referred to above, and with particular reference to literary works, any person who produces a book, literary or dramatic work in the state and intends to publish such literary material, such person shall apply for Censorship license from the board as contained in the board's law.

It follows therefore that person who for the purpose of ditribution or public exhibiton, makes a product or has in his possession any one or more, a blasphemous, pornographic or obscene writings, drawings, prints, printings, printed matters, pictures, posters, emblems, photographs or any other object tending to corrupt public morals has committed an offence and will not be allowed to go free.
To this end the board wishes to the stakeholders is that their proucts must pass through this board before sale, exhibition oe even before going to production process to avoid wasteful expenses.

Therefore the following stakeholders are expected to register with the board in compliance with the requirements of the Censorship board Law 2001. They include:
· Authors
· Publishers
· Bookshops(Book sellers)
· Poster sellers
· Distributors
· Vendors

A person who therefore exhibits, publishes, sales or distributes in any manner whatso ever, a literary work without censorship board certificate shall be liable to wrath of the relevant provision of the law.

In conclusion, the board implors our stakeholders to view the content of this release with matured understanding and literary works.
Its our hope to restore public confidence in board forward quality and moral delivery.

Signed by
ABUBAKAR RABO ABDULKARIM
Executive Secretary
Kano State Censorship Board
Friday, 21 September 2007

Wednesday, 29 August 2007

Ashe Narambad'a Bai Mutu Ba!

Wani manazarcin adabin Hausa ya na nan ya duk'ufa kan tattara kammalallen tarihi da wak'ok'in d'aya daga cikin shahararrun makad'an Hausa, wato marigayi Ibrahim Narambad'a

Daga Ibrahim Sheme da Ashafa Murnai Barkiya

Duk wanda ya san abin da ake kira “wak'ar Hausa,” to ya san Makad'a Ibrahim Narambad'a. Hasali ma dai akwai muhawara k'wak'k'wara kan waye ya fi fasaha tsakanin Narambad'a da marigayi Alhaji Mamman Shata. Yayin da wasu ke cewa Shata ya fi Narambad'a yawan wak'ok'i ne kurum amma Narambad'a ya fi zalak'a da fasaha, wasu na cewa ai shi Shata ya kere Narambad'a, musamman da yake shi wak'ok'in sa kowa zai iya fahimtar su – Basakkwace da wanda ba Basakkwace ko Bazamfare ba.

A bara, wasu matasa sun k'addamar da kammalallen tarihin Shata, wanda hakan ya k'ara taimakawa wajen fahimtar ko waye mawak'in. Shi kuwa Narambad'a, yawancin wad'anda suka san shi, sanin shanu suka yi masa. Kuma yawancin Hausawa sukan kasa gane wasu kalamai na wak'ok'in sa, musamman wad'anda ba su fito daga tsohon yankin k'asar Sakkwato ba. Bugu da k'ari, in ban da tak'aitaccen tarihin sa da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau na Jami’ar Bayero ta Kano ya rubuta a littafin sa Makad'a Da Mawak'an Hausa, ba kowa ba ne zai ce maka ya san tarihin wannan fasihin mawak'in.

To, yanzu dai an taki sa’a, domin kuwa aiki ya yi nisa wajen tattara kammalallen tarihin Narambad'a. Kuma sai aikin ya fad'a a hannun d'an gida, wanda ya san kan al’amarin, wato Farfesa Aliyu Bunza.

Shi dai Farfesa Bunza, fitaccen manazarci ne a k'asar Hausa. Ya yi rubuce-rubuce kan adabi da kuma al’adun Hausawa, har ma da wasu wak'ok'i na baka da kuma rubutattu. A yanzu shi ne ke rubuta tarihin Makad'a Narambad'a.
Shin yaya wannan aiki nasa yake ciki? A ranar Lahadi da ta wuce, an yi hira da Farfesa Bunza, wanda babban malami ne a Jami’ar Usmanu D'anfodiyo da ke Sakkwato, a sashen Hausa na gidan rediyon BBC. Wakilan gidan rediyon sun zanta da shi lokacin da ya je London kwanan nan. Mu a an Leadershi Hausa mun kalato muku wasu muhimman bayanai daga cikin wannan zantawa tasu ta musamman kan aikin da yake yi na rubuta tarihi da wak'ok'in marigayi Alhaji Ibrahim Narambad'a.

Tun da farko sun sako wak'ar Narambad'a mai taken, “Masu gari mazan gabas tsayayye, Sarkin Rwahi ya wuce a ram mai.” Idan kun tuna, a wannan wak'ar ce makad'in ke cewa, “Ga wani d'an sarki da kunnuwa da hwad'i...”

An tambayi Malam Bunza ya fad'i wani abu kan wak'ar. Sai ya amsa, “Sarki ne aka wa wak'ai na Kuryar Dambo, ba Kurya ta Madaro ba. Ma’ana, kurya guda biyu muke da su a Zamfara: akwai wannan Kurya ta Madaro, akwai waccan Kuryar Dambo. To hakimin Kuryar Dambo ne ya ka wa wak'a. Kuma wannan cewa ‘Da takobi da garkuwa da yak'i,’ daga cikin k'a’idar nazarin wak'a, “lugude” muke kiran sa, luguden tarihi. Wani tarihi ne ya narke wurin, tarihin wani sarkin d'an tauri ne da aka yi a Kurya mai suna Mamman Ina, da ya kashe wani Bature. To shi ya sa ya ke cewa ‘Kurya akwai mazan hwad'a da arna.’

BBC: Abin da ya sa na yi maka wannan wak'a, a da a Zariya idan muka ji wannan wak'a akwai wani gari Kauru a kusa da Zariya, mun d'auka shi ake wa wak'ar da ya ke cewa Makauru. Ashe ba Kauru ba ne. Wai me ake cewa ne a wurin? Ka san wani d'an sark'e-sark'e ne.

BUNZA: Ai da yake cewa ya ke yi, “Ai Kurya ta Dambo ta Makauru an nan, / Zamfara babu makaye kama tai.”

BBC: Za mu so ka d'an ba mu tarihin Narambad'a, watak'ila mutanen zamani ba su san ko wanene ba.

BUNZA: Marigayi Narambad'a shahararren mawak'i ne a duniya. Kuma idan za a yi tarihin Ibrahim Narambad'a, bisa k'a’idar ilmi sai an wa mutane da yawa tambaya wad'anda suka gabace ni a cikin wannan fagen, kamar Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, ya yi bincike musamman a kan Narambad'a; Bello Sodangi ya yi bincike musamman a kan Narambad'a; Sama’ila Yawuri Mazawaje shi ma ya yi bincike musamman a kan Narambad'a.

To sunan Narambad'a na yanka Ibrahim. Sunan uban sa Maidangwale, shi kuma Maidangwale mutumin Nijar ne, cikakken d'an kokawa ne. Amma Narambad'a ya gaji kid'i wajen uwar sa. Don haka shi karen makad'a ne kenan. Uban sa bai yi kid'i ba. An haife shi a garin Tubali, ya yi karatu a nan, ya rayu a nan, ya tashi a matsayin ba d'an gadon wak'a ba. Ya iske kayan kotson kid'in kakan sa na wajen uwa a d'akin mahaifiyar sa. Mahaifin sa mutumin k'asar Filinge ne, ya zo a garin Tubali, ya auri uwar Narambad'a. Kuma ga shi shahararren d'an kokawa ne.

Sai Narambad'a ya d'auki kayan kid'in mahaifin sa ya fara kid'an noma. To, wata shekara a fadar Sarkin Gobir na Isa ya yi kid'in noman k'auyen su. Da jin yadda dad'in wak'a ya ke da zalak'a da k'warewa, suka ce ya fi k'arfin k'auye, sai aka mai da shi birni. Ya tashi daga mawak'in noma ya koma makad'in Gobir. Ka ji tarihin zuwan sa.

BBC: Wato wannan ne kenan ya sa ya koma makad'i na fad'a, na sarakuna.

BUNZA: Gaba d'aya saboda an ga hikimar ta hi k'arhin ta manomi, dole sai an maida shi fada. Don haka ya dawo ya ci gaba da yi wa Amadu Sarkin Gobir wak'a.

(BBC sun sako wak'ar “Ya ci maza ya kwan yana shiri, uban zakara, dodo na Ummaru”)

BBC: To Farfesa Bunza, me za ka ce dangane da wannan wak'a?

BUNZA: Wannan wak'a ta Sarkin Gobir ta na cikin manya-manyan wak'ok'in da ya yi masa. Kuma wannan wak'a ce wasu suke ganin gabanin Narambad'a ya yi Bakandamiyar wak'ar sa. Don a ciki har Narambad'a na cewa duk abin da zai fad'a ga Sarkin Gobir daidai ne, ba kure ba ne:

“Na aje k'arya ko ina kid'i,
Na bar k'arya ko ina kid'i,
Nai sittin, saba’in ni ka hwad'a,
Mai saba’in yai k'arya ana ta zund'e nai,
Ko yaran da ag garai duw wawwatse mashi su kai,
Ya na yawo shi d'ai baram-baram.”


Saboda haka a cikin wannan wak'ar ba mu zaton mu ji abin da ya sab'a wa gaskiya. Don haka ne mu ke ganin wannan wak'a ta Sarkin Gobir na cikin manyan wak'ok'in sa. Amma dab baya da yai Bakandamiya, sai ta shahe hasken ta.

(BBC sun sako wak'ar “Batun da akai na yau babu Sarki yau irin ka,/ Jikan Bello arna suna shakkak ka”)

BBC: Farfesa, ko wanda bai san Narambad'a ba, ya san mutum ne wanda Allah ya ba basira. To amma kuma kamar yadda kowa ya sani, akwai shahararrun mawak'a wad'anda su ma sun yi suna. Ko dai kamar Narambad'an ko kusa da shi. Me ya sa ka d'auki Narambad'a a matsayin wanda za ka yi bincike akai?

BUNZA: Akwai dalilai da yawa. Na farko shi ne, fitattun mawak'an Hausa da mu ke da su k'asar Hausa an fara bincike a kan su – ko bincike ne na jami’a, ko ma na gida ne, duk dai an yi. Shata an yi aiki a kan sa. Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau ya yi bincike kan Salihu Jankid'i. To, na ke ganin a dukkanin k'asar Zamfara ba a yi mawak'in da ya kai Narambad'a ba. Kuma ba a k'asar sa kawai ya ke wak'a ba. Ma’ana, duk duniyar k'asar Hausa. Amma abin takaici, idan an zo neman wak'ok'i nai babu, sun wawwatse, ba a samun su.

Ba a san tarihin sa ba, ba a san ina ya hito ba, ba a san hikimar sa da zalak'ar sa ba. Sai na ga ya na da kyau a yi wani aiki da ak'alla zai fito da shi, zai fito da falsafar sa, zai fito da wak'ok'in sa, da wad'anda ya yi wa wak'ok'in, shi ma ya kasance wani taska daga cikin taskar adabin Hausa da za a aje.

BBC: Ban tari numfashin ka ba. Wasu kalmomi da Narambad'a ke amfani da su a cikin wak'ok'in sa, idan ba fassara wa mutum aka yi ba, ba a fahimtar abin da ya ke fad'i. Ina ganin wannan ma ya na da mahimmanci a yi irin wannan bayani da ka yi. To zuwa yanzu ka rubuta wak'ok'in sa guda nawa?

BUNZA: Sai dai in ce na samu wak'ok'i guda nawa? In na samo su sai in rubuta su…

BBC: Ban tari numfashin ka ba, rubutawar ka na rubuta duk abin da aka ce a cikin wak'a?

BUNZA: E, zan yi k'ok'ari duk abin da ya ce, zan yi k'ok'ari in rubuta kuma a irin lafazin da ya fad'a. Kamar Sarkin Rafi, ai Sarkin Rwahi ya ke cewa. Ni ma Rwahi zan rubuta.

BBC: Wak'ok'i nawa ka samu zuwa yanzu?

BUNZA: Wasu su kan ce ya yi wak'ok'i sun kai d'ari ko d'ari da wani abu, amma iyakar binciken da mu ka yi, kusan sama da shekaru ashirin da wani abu, gaskiya ni hamsin na samu, wad'anda na rubuta da kai na, na saurara, na tabbatar sun rubutu, na ajiye.

BBC: Wad'anda aka d'auke su da faifai kenan?

BUNZA: Ma’ana, shahararrun wak'ok'in da aka sani a kaset, ba dab bakin wani aka ji su aka rubuta ba.

BBC: Dangane da wak'ok'i ko mawak'an Hausa, kamar Alhaji Mamman Shata ana cewa ya na tsayawa nan take ya yi wak'a, don an sha gwada shi, ba tare da ya zauna ya shirya ta ba. Shin Narambad'a ya yake tsara wak'ok'in sa?

BUNZA: Wato ko wane irin mawak'i da irin fasaha da hikima da zalak'a da Allah ya hore masa. Allah ya hore masa wak'a, amma shi (Narambad'a) ba a nan take ya ke yin ta ba. Idan zai yi maka wak'a, zai je gida ya tsara ta; a yinin da zai yi wak'ar, ba zai yi huld'a da kowa ba. Haka wasu yaran sa su ka shaida mana. In ya k'are tsara ta, sai ya kira yaran sa, sai su rera. Wak'ar Narambad'a in zai yi ta, zuba wak'a ake zube-ban-k'warya.

BBC: Kamar yadda ya ce ta Alfazazi…

BUNZA: Cewa ya yi:

“Kullum ji ni kai azanci na hudo min,
Sai zuba wak'a ni kai kama da ta Alfazazi.”


BBC: Rubutawa ya ke yi?

BUNZA: Narambad'a ba ya rubuta wak'a, sai ya samu gindin wak'a ya fara. Da ya k'are abi nai cikin zuciya, sai ya kira yara nai ya ce, “To, ga amshin wak'a kaza,” su rik'a yi a sannu ana maimaitawa. Sai ya k'are sai aje a yi ta.

BBC: Wak'ar Alk'ali Abu fa? Shin wanene Alk'ali Abu d'in nan?

BUNZA: Alk'ali Abu asali mutumin K'auran Namoda ne, alk'alanci ya kai shi Moriki, kuma daga cikin ’ya’yan sa akwai wanda ke raye a Sokoto yanzu. Amma dai zuri’ar na can a K'aura. Ba Alk'ali Abubakar Mahmud Gumi ba ne kamar yadda mutane su ke zato. Ya yi masa wannan wak'a a kan irin adalcin sa, gogewar sa da sanin shari’a.

(BBC sun sako wak'ar “Alk'alin Alk'alai ta aiki nai da tsari…”)

BBC: To amma akwai inda yake cewa “Narambad'a ba ya zuwa lahira...,” kamar ya bugi k'irji…

BUNZA: Ya ce ko ya je dawowa ya kai. Ya na da hujja a wannan wurin. Sai an kamo kan wak'ar za a gane me ya sa ba zai je lahira ba! Ya ce:

“Hwad'awa ku bugan in buge ku
Mui ta fad'an mu gidan duniya,
Kun san ba a hwad'a lahira,
Kun san ku ka zuwa lahira,
Narambad'a ba ya zuwa lahira,
Ko ya je dawowa ya kai,
Gama kun san d'auke mai akai.”


Maganar sa ta tabbata: fadawa ke mutuwa; da bafade ya mutu, a fada an manta da shi. Da Sarki ya mutu, a fada an manta da shi, an yi wani. Amma idan zakaran mawak'a ya mutu, ba mutuwa ya yi ba. Har yanzu ga Narambad'a ba shi duniya, ana maganar sa, ana jin maganar sa. Ina fadawa su ke? Saboda haka duk wani mawak'i da ya san kan sa, ya yi luguden wak'ar, to bai mutu ba, ya na nan a raye!

BBC: To, Farfesa Aliyu Bunza, mun gode k'warai.

Musulmi ne abokin gabar Musulmi

A cikin wannan makon, labari ya bazu a Kano cewa wai an samu wani sabon bulufim kuma na wata 'yar fim din, wato bayan na Maryam Hiyana da ya bazu a gari. Wai wata wadda sunan ta ya fara da suna "M" ce ita ma ta yi majigin batsa.

To a gaskiya na yi cikakken bincike, na gano cewa sam, labarin ba gaskiya ba ne.

Abin da ya faru shi ne, wasu shakiyyai (ko wani shakiyyi) ne suka dauki wani bulufim na Amerika, suka saka a cikin wayar GSM, suka ba shi sunan ita wannan "M" din, suka kuma yad'a a garin Kano cewa wai ita ma ta yi bulufim. Inda za ka san cewa ana bin 'yan fim da sharri da gangan shi ne yadda su kan su Turawan da ke cikin wannan fim, ba ma bakar fata ba ne, a'a, jajaye ne suke yin lalatar, to amma don sharri sai aka ba fim din sunan "M" din.

Don haka don Allah mu daina saurin yad'a ji-ta-ji-ta. Sai ka ga mutum bai yi wani bincike ba, amma da jin cewa an yi kaza sai ya shiga yad'awa, wani har a intanet (watakila don kada a riga shi!). Don Allah mu daina yad'a ji-ta-ji-ta. Mu tuna, a yau Musulmi shi ne babban abokin gabar Musulmi; Musulmi ne ke daukar wuka ya dab`a wa cikin sa. Mun ga haka a al'amarin Hiyana.

Sunday, 26 August 2007

GYARAN GANGAR ABZINAWA!

Na saurari jama'a a cikin 'yan kwanakin nan tun lokacin da hayaniyar Hiyana ta taso, kuma na karanta wasu ra'ayoyi a kan lamarin. Akwai mutane da na ga suna cewa wai ya kamata a dakatar da harkar shirya fim baki daya a kasar Hausa. A yanzu haka ma akwai masu cewa harkar finafinan ta mutu har abada!

Ni ra'ayi na ya bambanta. Ba na tsammanin za a daina yin fim saboda Hiyana. Ga dalilai na:

1. Fim al'amari ne na ci-gaban fasaha (technological development) da ya shigo kasar Hausa. Kamar ka ce a daina amfani da wayar GSM ne. Fim ya riga ya zo, ko mu ce ya ci gaba (domin kuwa tun tale-tale akwai shi). Ba zai dainu ba.

2. Fim sana'a ce. Ko tana da kyau ko ba ta da kyau, sai an yi shi. Ni a gani na, sana'a ce mai kyau idan za a gyara ta, ta yadda za ta tafi daidai da addinin mu da al'adun mu. To mu dauka ma ba ta da kyau din kamar yadda wasu ke cewa; shin an hana sata? An hana karuwanci? An hana zamba? An hana shan wiwi? Me ka hana?

3. Idan aka hana yin fim (wai wa ma zai hana? Gwamnati ko malamai ko mutanen gari?), to za a samu 'yan sunkuru su rika shirya "finafinai" wadanda suka fi wannan da ake yi yanzu muni. Wato za su yi ramuwa kan hana su harkar da aka yi. Su rika sayarwa ta bayan gida (underground).

4. Idan an hana yin fim a Kano, za a hana yi ne a Filato ko Bauchi da Kaduna da duk sauran jihohi? Za a hana a Legas da sauran jihohin Kudu? Ko kuwa idan an je Legas an yi fim din Hausa, sai a hana sayar da shi a ko'ina a Nijeriya? A lura, Gwamnatin Tarayya ba za ta hana yin fim din wani yare ba.

5. A gani na, Gwamnatin Jihar Kano din ma ba za ta hana yin fim ba domin 1. harkar fim ta rage wa gwamnatin matasa marasa aikin yi. Na biyu, sana'ar fim ta kasance hanyar samun dimbin kudaden shiga ga gwamnatin Jihar Kano ta hanyar kudaden harajin tace fim da sauran su. Na uku, sana'ar fim ta taimaka wa harkar kasuwanci a Kano. Akwai manyan 'yan kasuwa da aka samu ta hanyar sana'ar fim. Shin gwamnatin Kano za ta kashe harkar fim a daidai lokacin da sauran harkokin kasuwanci na Kano (misali, masana'antu) suke durkushewa?

Ga mafita.

Na sha gaya wa wasu mutane cewa shirin fim kamar d'aki ne -- idan ka zuba shara ciki, za ka tarar da shara a ciki; idan ka zuba tabarmi masu kyau a ciki, su za ka tarar. Don haka kamata ya yi a gyara sana'ar don ta tafi daidai da tarbiyya tagari. Dakatar da harkar zai kasance gyaran gangar Abzinawa.

Duk masu cewa a dakatar da fim -- daga 'yan boko zuwa malamai da sauran masu surutu -- suna yi ne saboda wani dalili na son rai nasu. Wasu don a ce sun ce. Wasu don su nuna su malamai ne. Wasu don su nuna cewa su 'yan gurguzu ne (radicals). Wasu don son a sani. Kai, wasu ma don sun jahilci abin ne. A tuna, tun kafin al'amarin Hiyana, akwai masu sukar harkar fim. Gyaran ne aka ki yi. Amma yanzu dama ta samu ta yin gyara, don haka sai a gyara. Akwai sana'o'i da ayyuka da suka fi fim muni, amma ba a dakatar da su ba, sai wannan?

Kuma su masu sukar 'yan fim da sana'ar fim, da me suka fi 'yan fim tarbiyya? Akwai manema mata da 'yan luwadi da mazambata da magulmata da matsafa da sauran mugga a cikin al'umma a cikin su da ske cewa wai a hana yin fim saboda "laifin" Hiyana. Wanzami ba ya son jarfa, ko?

Kai, gaskiyar masu iya magana da suka ce laifi tudu ne - ka taka naka, ka hango na wani.

Wednesday, 22 August 2007

JARABA 1

JARABA wani sabon littafi ne da na ke rubutawa, ana bugawa a jaridar Leadership Hausa kowace Juma'a. Wannan shi ne kashi na farko, wanda zai fito jibi Juma'a a jaridar idan Allah ya kai mu. A sha karatu lafiya.

BABI NA DAYA

Tara ta gota. Lokacin da Tanimu ke karyawa, ya ji lokacin da tamburan gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna su ka buga, kuma ya ji mai gabatarwa na cewa, “Yanzu }arfe tara. Ku na tare da Sashen Hausa na Rediyon Tarayya na Kaduna.” Daga nan sai aka sako ki]a a filin ‘Za~en Mai Gabatarwa.’ Kassu Zurmi ne aka sako ya na rera wa}ar Shayi [an Gidan Labbo. A duk lokacin da Tanimu ya ji wannan wa}a, ba abin da ya ke tunani sai dalilin da ya sa Shayi ya zama talasuru haka.
Bara ya yi jidalin bi]ar aure sai da yas samu,
Kai ta gidan maigidan su yah hwa]i,
Tsoho ya hwa]i ba abin ]iba
Kuma ba abin gado,
Su ko masu gari, dan}o ba ka hwa]uwa }asa banza.
To amma kuma daga baya sai ga shi Shayi ya nuna mana cewa ya san abin da yake yi. Ba wawa ba ne. Ba gaula ba ne. In ba haka ba, ya aka yi har ya “hwara sassaben gonas su”? Kuma ya aka yi bayan masu gari sun sayar da gonar, ya yi tawaye har aka mayar masa da gonar ala tilas? Anya Shayi talasuru ne? Tanimu ya tambayi kan sa a yayin da amon gangunan Kassu ya cika masa falo, ya na fitowa daga cikin wata ]ibgegiyar rikoda da ke kan dibaida.
Can sai ga Tsahare ta shigo. Ta na sanye da ba}ar abaya mai ratsin kore tare da wata }awanya a }asan ta mai ruwan gwal.
“Yanzu za ka tafi ne?” ta tambaye shi.
Tanimu ya tsotse yatsun sa, ya ture kwanon ]umamen nan gefe, sa’annan ya amsa, “{warai kuwa. Ban son Alhaji ya riga ni zuwa shago, ko da yake dai ya ce zai je ]aurin aure da safen nan. In ya riga ni, zai yi min fa]a. Kin dai san shi da fa]a – kamar sabon kuturu.”
Tsahare ta yi ‘yar dariya, ta ce, “Uh hm! Kada dai ka ciji yatsan da ke }osar da kai.” Ta je ta nemi wuri a kan kushin ta zauna da }yar. Ta na da tsohon ciki, wanda ya maida ita ta na harkokin yau da kullum a takure kamar mai ta~arya a cikin ciki. “In ka na ruwa, kada ka zagi kada.”
“Tsaharatu kenan! Wallahi shi ya sa na ke son hira da ke. Ba ki ganin laifin kowa,” inji shi.
“Ba haka ba ne, Tanimu. Kai da Alhaji dai ai ba a cewa komai. Duk wanda ya san ka, tare ya gan ku. Kuma wane abu na alheri ne bai yi maka ba? Kar ka manta, shi ne fa ya biya maka sadaki; kai, shi ne ma ya yi ma wannan auren.”
“Oho! Gori kuma za a yi mana? To, ko za a maida amaryar gidan shi ne, ni a bar ni haka nan?”
“Allah ya huci zuciyar ka. Ba nufi na kenan ba.”
Tanimu ya mi}e daga kan tabarma inda ya zauna ya yi kalaci. Sai ya tuna bai sha ruwa ba, don haka ya du}a ya ]auki goran roba, ya kwankwa]i ruwa.
Tsahare, hannayen ta a kan cinyoyin ta, ta na kallon ma}ogwaron sa, kamar ta na kallon ruwan ya na wucewa a kwararon sa tamkar wani }aton kogi.
“Wannan irin shan ruwa haka – sai ka ce wanda ya cinye giwa?” ta tsokane shi.
Ya aje goran, ya dube ta, ya ce, “Tsahare ai wannan malmalar da na cinye, ]aya ta ke da giwa. Zakaran ka, ra}umin ka. Kuma ga shi kin yi mani irin miyar da na ke so – kuka da man shanu da ]an yajin tattasai.”
“Miyar kuka Baha]ejiya! An gaishe ki mai sa maigida santi!” Tsahare ta yi dariya, ta mi}e.
Tanimu ya ]auki hular sa da ke kan kujera, ya sa. Shi da matar sa su ka fita daga ]akin, su ka doshi babur ]in sa da ya aje kusa da }ofar shiga gidan. Da ma a duk lokacin da zai tafi aiki, sai Tsahare ta raka shi inda mashin ]in sa ya ke.
Gidan nasu ya na }unshe da gidaje uku, kowannen su flat ne mai ]aki biyu da falo da ban]aki da madafa. A tsakar gidan akwai bedi inda matan gidan su kan taru su na yin hirar su da ‘yan aikace-aikace. Domin fa a gidan matan aure uku ne. [aya sunan ta Lami, matar wani ma’aikacin reluwe mai suna Abdullahi; ]ayar kuma Magajiya, matar Ustaz.
Da su ka isa, Tanimu ya dudduba mashin ]in, sannan ya buga shi ya tayar. Gidan ya cika da rugugin sa. Da ya hau mashin ]in, sai ya dubi Tsahare, ya ce, “Allah gama fuskokin mu da alheri!”
Ta kara hannu a jikin kunnen ta, ta ce, “Me ka ce? Wallahi ban ji ba!”
Ya ce, “Cewa na yi gamon katar!”
Sai ta sa hannu ta kama makullin mashin ]in, ta juya shi. Mashin ya mutu.
Ta ce, “Ai da sai ka bari sai mun gama magana sannan ka tafi. Ba na jin ka, saboda }arar mashin. Me ka ce?”
“Cewa na yi sai mun ha]u. Anya lafiya wannan kunnen naki? Ko ~ur~ushin kurunta ya soma shigowa ne?”
“Wallahi lafiya ta lau. Haba Tanimu, mashin ]in naka ne ya cika rugugi, abu kamar jirgin sama! Shi ya sa na ran nan na ce ka sayi Besfa, ta fi da]in sha’ani. Ka san ni abin da ke shero ni Besfa shi ne ‘yar gu]ar nan tata mai da]i idan an murza ta. Ni in da namiji ce, ba yadda za a yi in sayi mashin bayan ga Besfa. Da za ka sayi Besfa, zai dace. Ka ga idan ma mutane sun gan ka, sun san ba ]an aca~a ba ne.”
“Kin fara ko? Ke dai Tsahare ba ki rabuwa da tsokana.” Ya dubi rigar sa, wadda shu]iya ce mai kyakkwan aiki a wuyan ta. “Ya za a gan ni a haka a ce min ]an aca~a? Ai su ‘yan aca~a da ka gan su ka san su ne; abu za ki ga wani ma kamar ]an sama jannati! Wasu za su saka irin hular nan hana-salla da burgujejen wando irin wanda ake kira buhun mahaukata, da tsohuwar rigar sanyi ‘yar Rasha wadda kila ma mai ita ya da]e da she}awa barzahu. Wani ma sai ki ga har da ba}in gilashi ya }wamo, wai shi niga. Abin babu ko kyan gani.”
“Ni fa wannan shigar tasu ta na ]aya daga cikin abubuwan da ya sa ba na hawan express lokacin ina budurwa. Wani ]an express ]in ma sai ka ji ya na wari.”
“To me zai hana su yi wari tunda dai kullum su na cikin gumi, sun ]ibga kaya kamar gawa a makara? To yanzu da irin wa]annan ne za ki kwatanta ni, ni da ke cikin shigar mutunci? Ai yaro ko da ganin birni ya san ya fi garin su.”
“A cikin ‘yan express akwai masu shigar mutunci. Irin magidanta ]in nan masu shekaru da ]an kauri-kauri. Su ba sa yin irin shigar nigogin nan. Ni na fi son hawa mashin ]in su. Ga shi kuma ba su gudun fitar hankali irin na sauran ‘yan mutuwar. To wasu za su iya ]auka kai irin su ne.”
“Ke dai ki na tsokana ta kawai. Na san manufar ki – ke dai in canja zuwa Besfa. To ba komai Tsahare ta. In da rai da rabo, ko? Wata rana sai ki ga mutum a mota ma.”
“Haka ne. Allah ya ba mu sa’a.”
Su ka kalli juna. Tsahare ta yi masa murmushi, shi kuma ya ci gaba da kallon ta babu }iftawa har abin ya so ya ba ta kunya.
“Lafiya ka ke kallo na haka kamar maye? To, kurwa ta kur!”
Tanimu ya yi murmushi, ya ce, “Ai ni da maye ne, ke zan fara cinyewa – don kada in ta~a rabuwa da ke. Kin ga idan kin shiga cikin jinni na, ai shikenan kullum mu na tare kenan.”
“To ai kuma za ka daina gani na kenan.”
Tanimu ya ce, “Wai yau me za ki dafa mana ne – abincin dare?”
Ta ce, “Me ka ke so? Na san dai kai sarkin cin tuwo ne.”
“E, haka ne. Kin san Shata ya ce sai wawa sai mahaukaci ke raina mafari. Tuwo da hura kuwa su ne mafarin Bahaushe.”
“Ka na nufin dai a yi tuwon, ko?”
Ya girgiza kai, ya ce, “Rai dangin goro ne, ban iska ya ke so. Gara mu sauya abinci. Me zai hana ki yi mana faten tsaki, ki toya mashi man ja, kuma ki dama mana kunun tsamiya mai ]auke da kanumfari?”
Tsahare ta ce, “An gama! Ni ma ina marmarin kunu wallahi. Amma kuma kai ma ka taho mana da gasasshiyar kaza don mu kwantar da yawun marmari.”
“Da kyau, uwar ‘yan biyu! Ai da ma na san a rina, an saci zanin mahaukaciya! Na san sai kin ce a zo maki da nama.”
“{warai, ai ba laifi ba ne. Ka san mai ciki da kwa]ayi… Ka dai bi a hankali, kada wata rana in cinye ka kamar mayya!”
“Wa ma ya sani ko mayyar ce na auro? Wannan cin nama haka?”
“Ai mayu ba sa cin nama, malam, sai dai kurwa.”
“Way a gaya maki? Kul, kada mayen gaske ya ji ki! To, zan zo da kazar, ke kuma ki yi naki aikin. Kin ji ko, uwar ‘yan biyu?”
“To. Amma ka san na ce ka daina kira na haka, ko? Wa ke son ya haifi ‘yan biyu yanzu? [ayan ma ya ishe ni.”
“Ai Allah ke bayarwa. Kuma dai wannan ciki naki, in ba ‘yan biyu ba ne a cikin shi to menene? Abu kamar kin ha]iyi duro!”
Tsahare ta tum~una fuska, ta ce, “A’a, ba duro na ha]iya ba, mota ce tanka mai taya sha takwas!”
Fa]in haka ke da wuya sai duk suka bushe da dariya.
Da su ka gama, Tsahare ta dube shi, ta ce, “Tanimu, don Allah ka yi min wani al}awari.”
Ya gyara zama a kan mashin, ya tambaye ta cikin damuwa, “Al}awarin me?”
Ta ce, “Al}awarin za ka dawo da wuri domin mu ci abincin dare tare.”
Dariya ta kama shi, har ya na }walla. Ya na sharewa, ya ce, “Haba Tsaharatu! Ke ni fa har na ]auka wata babbar magana ce? Wannan ma har wani abin yi ma al}awari ne?”
Ta ce, “Ni dai ka yi min. Domin na san ka, kullum sai ka ce za ka dawo da wuri, amma ba na ganin ka sai tsakar dare. Abincin ma ba ka ci, said a safe a yi maka ]umame. Har ina tunanin ko wata ta sace maka zuciya ne.”
Ya ce, “Sam, ba haka ba ne. Ai na ce maki ba za ki ta~a samun kishiya daga gare ni ba. Haba, ni da na samu mace ]aya tangan da goma! To, in dai batun al}awari ne, na yi maki. Zan dawo da magariba. Ki shirya komai. Ai ba ki sani ba ma, sabon amarci za mu bu]e!”
Cikin farin ciki, ta ce, “Alhamdu lillahi. Ni kuma zan jira ka. Zan shirya komai kafin ka zo. Kuma wallahi ba zan ci abinci na ba sai ka zo mu ci tare, ka ji ko?”
Tanimu ya amsa, “Kalas! Na ji, na yarda.”
Ta ka]a kai, ta ce, “Sai ka yi }o}ari ka tafi, kada Alhaji ya ritsa da kai ka ce mashi ni ce na ri}e ka a gida!”
Daga nan su ka yi sallama. Tsahare ta je get ]in gidan, ta bu]e masa. Ya tada babur ]in sa, ya fice daga gidan tare da ]aga mata hannu. Bayan ya tafi, ta rufe get ]in, ta koma falon ta.

Za mu ci gaba a makon gobe insha Allah

Birnin Kano a zamanin iyayen kakannin mu

'Yartsana za ta sake shiga gari!


Littafi na, "'Yartsana," ya sake fitowa. Tun lokacin da ya fito a cikin 2003, ya ci kasuwa a 2004, ba a k'ara ganin shi ba. Ya k'are! Mutane sun sha tambaya ta cewa don Allah a sake buga shi, amma ina! na kasa saboda yanayin rayuwar kasar mu. To amma yanzu an buga shi, aka gama a makon jiya. Zai fito a ranar 1 ga watan Satumba. Ko yaya mutane za su kalle a yanzu bayan hayaniyar Hiyana? Oho! Ban damu ba.