Friday, 23 March 2007

Bilkin Sambo ta Mamman Shata!


Ana yi wa Dr Mamman Shata kirari da
"Sarkin wakar Kanawa,
Duna na Bilkin Sambo.
Warga-wargan namiji
Mai daci kamar guna..."

Wai shin Bilkin Sambo, matar sa ce, ko kuma k'anwar sa ce? Kuma meye tsakanin su da Yalwa? Wannan ita ce tambayar da Fatuhu ya yi a Majalisar Marubuta kwanan nan. Ni kuma na ba shi amsa kamar haka:


Malam Fatuhu,
Lallai ka yi tambaya ga d'an gida.
Tambayoyin ka su ne:
1. Wai shin Bilkin Sambo, matar Shata ce, ko kuma k'anwar sa ce?
2. Kuma meye tsakanin su da Yalwa?

BILKIN SAMBO
Wata mata ce a garin Funtuwa, Jihar Katsina, wato garin da Shata ya yi rayuwar sa, inda iyalin sa su ke. A farkon zuwan Shata Funtuwa, bayan ya taso daga Bakori (wanda shi ma gari ne kusa da Funtuwa) sai su ka shak'u da Alhaji Nagoya, wani d'an kasuwa mai cinikin auduga. Nagoya ya d'auki Shata kamar d'an sa. Don haka ne ya had'a shi da wasu 'ya'yan sa biyu mata, Indon Dutsen Reme da k'anwar ta Bilki.

Akwai kuma Sambo, wanda shi ne babban d'an Nagoya d'in. San da duk aka yi haihuwa a gidan Alhaji Nagoya, ya kan kirawo Shata ya ce, "Ga uwargida!" ko "ga ubangida na yi maka!" Da aka haifi Bilki, Shata ya na makad'in gidan, sai maigidan ya ce masa, "To ga sabuwar uwargida na yi maka." Daga nan ne ita Bilki, wadda akan kira Bilkin Sambo, ta zama Bilkin Shata, sa'annan shi ma Shata ana ce masa Na-Bilkin Sambo (har marokan sa su kan yi masa kirari da "Mai tambura Na-Bilkin Sambo!").

Abin mamaki, Shata bai yi Bilki waka ba (a iya sani na), amma kuma ya wak'e Indo da wakar "Indon Dutsen Reme Lambawan." A yanzu ita Indo ta na auren Magajin Garin Musawa, Alhaji Abdullahi Inde. Ita kuma Hajiya Bilki, ta nan da ran ta a Funtuwa, inda ta yi aure har ta hayayyafa. Ga hoton ta nan tare da d'an ta (amma tsohon hoto ne, domin na ke jin kila ma wannan yaron ya girme ka!)

2. YALWA
Akwai Yalwa guda biyu a rayuwar Shata. Ta farkon ita ce kanwar sa mai bi masa, wadda ta rasu tun tuni. A garin su Musawa ta yi aure, har ta haifi d'a wanda ake kira Umbaje (ka san ana yi wa Shata kirari ana cewa "Uban Umbaje").

Yalwa ta biyu kuma ita ce Hajiya Yalwa Bature, wadda matar sa ce da ya fi so a rayuwar sa. Sun dad'e da rabuwa, har ta auri marok'in sa Alhaji Bature Sarkin Magana (wanda shi ma ya dad'e da rasuwa, tun kafin Shata ya rasu). Hajiya Yalwa ta na nan zaune a Kaduna tare da 'ya'yan ta, cikin su har da 'ya'yan da su ka haifa da Shata (Umma, matar Kanar Bala Mande wanda ya tab'a yin gwamna a zamanin Abacha, kuma ya yi ministan Obasanjo), da Bilkisu Shata wadda d'aliba ce a fagen Political Science a Jami'ar Abuja, da kuma Nura).

Da ka ji ana kiran Shata, "Shata na Yalwa", to k'anwar sa din nan ake nufi, ba matar ba, domin tun kafin ya auri Yalwa ake ce masa hakan.

Da fatan ka gamsu.

8 comments:

Talatu-Carmen said...

Malam Ibrahim,

Tun, tun ada, ina ta tunani yadda nake so in rubuta ka (sorry for the bad grammar). Sai, lokaci ya guduna. Ka yi hakuri. Amma, na karanta 'Yar Tsana shekara da ta wuce, kuma ina son littafin din kwarai da gaske. Ina so in sake karanta shi kafin na rubuta a kansa, amma wallahi tallahi littafin mai ban sha'awa ne.

To, bari in cigaba da aikina, sai ina so in gaishe ka. (Prof. Abdalla ya gaya mini a kan blog d'inka.) Ka huta lafiya,

Talatu

Anonymous said...

Salam,
Ranka ya dade, na karanta amsar da ka baiwa Fatuhu a kan Bilkin Samo, kuma ni ma na karu da abubuwa da dama a ciki. Allah Ya taimake ka, amin.
Bissalam
Al-Amin Ciroma

joffe said...

Salam, Ibrahim
mun gode da blog naka. Allah ya taimaka, amin.
Jaafaru Malik

DAN'UMMA said...

ML. Ibrahim salamu alaikum. kanar Bala Mande yayi gwamnan nasarawa state a lokacin mulkin Gen. Abdussalam Abubakar ne ba lokacin Gen. Abacha ba. Mun gode.

Unknown said...

yallabe, thank you for the information. what of Barira diyar Mallam?

Unknown said...

GYARA
Alhaji Sambo Yellow ba shine babban D’an Malam Nagoya ba, akwai Adamu wanda akafi sani da Baban Dabo shine babban D’an malam Nagoya.
Haka kuma Indon Dutsen-reme ba ita ce ke aure a Musawa ba, ita a Kano take aure tama haifi wani d'a da ake cema Alhaji B.B wanda ya taba yima Gali Na Abba S.A.
Kada ka manta malam Nagoya yana da Indo biyu wato Hajiya Indo wadda ta auri magajin garin Musawa da Hajiya Indon Dutsen Reme mai aure a Kano. Sannan kuma yana da Bilki biyu wato Bilkin Sambo da Bilkin Gali.
Da fatan ka gamsu.

Bahaushe Mai Ban Haushi said...

Na gode kwarai da gyararrin da ku ka yi mani. Ni ma na k'aru matuka. Sheme

AREWA CASSIQ TUNES said...

Na code da samun mor information akan shata