Saturday 19 May 2007

Bikin kona littattafai - Amsar Abdalla

Professor Abdalla Uba Adamu
Sashen Horon Malaman Kimiyya da Fasaha
Jami’ar Bayero, Kano

Hira da Maje el-Hajeej na Hausa Leadership wacce za ta fito a wannan satin (19 Mayu 2007).

1. Shin a matsayin ka na Furofesa ko bikin kona littafan Hausa da gwamnati ta yi ya dace?

Ba a matsayina na furofesa zan yi magana ba – domin za ka samu furofesoshi da dama wadanda wanna abin ya zauna mu su daidai. Zan yi magana ne a matsayina na almajiri mai neman ilimi. Gaskiya a nawa ra’ayin wannan bai dace ba, domin babu cikakken bayani game da laifin da littattafan da a ka kona a ka ce sun yi. Da zai yi kyau, kafin a kona, a yi wani sharhi a kan kowanne littafi domin nuni ga ire-iren abubuwan da hukuma ta haramta kuma wadanda suka fito a cikin wadannan littattafan. Ta haka za a tabbatar da cewa sun aikata wani laifi. Yin haka shi ne adalci.

Amma ko da sun aikata laifi, konawar ba shi ne mafita ba – domin konawar zai jawowa gwamnati wata matsala inda za a funskance ta a kan maras son ci gaban al’uma. Sannan kuma za a iya kwatanta wanna da ire-iren abubuwan da gwamnatin Taliban ta yi a Maris 2001 na dandake gumakan Buddha, wadanda sun fi shekaru dubu a kasar, har ma duniya ta dauke su a matsayin jarin al’adun al’ummatn duniya. Manazarta sun yi kuka da lamarin da nuni da cewa duk da wadannan gumakan na kafirci ne, wanda kuma ya sabawa gwamnatin Taliban ta wancan lokacin, amma adanasu na da humimmanci wajen tattara tarihin dan Adam da nuni da yadda rayuwarsa ta gabata, wannan ma kadai zai hana a sake yunkurin bauta musu domin da ganinsu ka ga sakakkun abubuwa wadanda ba su cancanti a bauta musu ba.

Amma duk da cewa ban goyi bayan konawar littattafan kagaggun da aka yi ba, dole mu yi la’akari da cewa gwamnati na da hakkin kula da rayuwar jama’a ta yadda ya dace da jama’ar. Saboda haka in bera na da sata, daddawa na da wari.

2. A matsayin ka manazarci ko irin wannan bikin kona littattafai ya na faruwa a wasu sassan duniya?

Bikin kona littattafai ba abu ne sabo a duniya ba. Tarihi ya nuna cewa hukumomi da dama a lokuta dabam-dabam sun shugabanci bikin kona littattafai saboda dalilai guda uku. Na farko tunanin cewa abin da aka rubuta ya sabawa akidar al’ummar da aka rubuta a cikinta. Na biyu sabawa addinin da hukuma ta yarda da shi – ko da marubucin ba ya cikin addinin hukumar. Na uku siyasa tana sa hukuma ta jagoranci kona littattafai domin ganin an karya alkadarin ‘yan adawa da gwamnatin da ke kan gado.

Abin da ya sa ake kare fasihai (marubuta, mawaka, da kuma masu zane ko fim) daga bikin kona ayyukan fasaha shi ne wata rana ba rubutun za a kona ba – fasihan za a kona. An taba yin haka a China a karkashin masarautar Qin (shekaru 212 kafin bayyanar Annabi Isa (AS) wacce Qin Shi Huang ke shugabanta, inda shugaban lokacin ya ga kona littattafan bai isa ba, sai ya hada da kona masu rubutun littattafan; har ma da masu karatun – duk sai da ya sa a ka kona su, kimanin mutane 450.

Haka ma sojojin Rumawa suka bi wannan salon kona littattafan da ke Laburaren Alexandari a jihar Alexandria da ke Masar (Egypt) shekaru 300 kafin bayyanar Annabi Isa (AS). A wannan lokacin a duk fadin duniya babu wata laburaren da ta fi wannan girma, yawan littattafai da kuma manazarta. Kar fa a manta duk tarin littattaan da hannu aka rubuta su, domin lokacin babu injin buga littafi.

Da Hitilar ya zama shugaban Jamus kuma ya kafa akidar Nazism, shi ma ya shugabanci kona littattan da Yahudawa suka rubuta, a rukunayen shekarun 1930 da 1940. Misali, ranar 10 ga Mayu 1933 kusan littattafai 20,000 a ka saka daliban suka kona a Berlin.

Babu inda ba a kona littattafai ba – daga kasar Amurka, inda ake ganin sun fi kowa walawa, zuwa kasashen da dama ana ganin kamar a takure su ke. A Ingila a shekar 1525 an kona littafin Injila wanda William Tyndale ya rubuta. Sannan a 1633 an kona Histiro-Mastix, littafin Willian Prynne wanda ya kalubalanci sarauniyar Ingila. Shi kansa marubucin, an kama shi, a ka yi masa dukan tsiya, aka yanke kunnuwansa, sannan a ka kulle shi a gidan yari. A Amurka a 1650 an kona littafin Willianm Pynchon, mai suna The Meritorious Price of Our Redemption saboda ana ganin ya yi sabo. Jaridar farko a Amurka, Public Occurences, haramta fitowarta a ka yi a 1650.

Kada kuma a dauka wai jahiliyyar ilimi ce ta kawo wannan. A dai Amurka din, a jihar New Mexico, a 2001 an kona kagaggun labaran Harry Potter, labarin wani yaro mai yin shihiri.

A Masar, a Janairu na 1991 hukumar kasar ta jagoranci kona duk littattafan Abu-Nuwas al-Hasan ben Hani al-Hakami ( wanda ya rayu daga 750 zuwa 810 miladiyya), wadanda ake ganin kamar sun shafi batsar luwadi da kuma sharholiyar shan giya.

Saboda haka akwai misalai ratata inda a ka kona littattafai saboda rashin yarda da marubuci – daga kasashen da ake ganin sun ci gaba, zuwa kasashen da ke tasowa. Ba abu ne sabo ba; ba kuma abu ne da za a ce wai gwamnatin Shari’a ce ta kawo shi ba – da ma yana can.

3. Shin a irin karatun wadannan littattafai da ka ke yi, ko kana ganin sun cancanci gwamnatin ta kona su?

Kamar yadda na ce, ba mu san sunayen littattafan da a ka kona ba, da kuma hujjar da a kabi domin tantance wadanda za a kona. Tabbas a kwai littattafan da suke dauke da abubuwan batsa marassa kyau. Wadannan sun hada da, misali, Shu’uma (Maje el-Hajeej), Maza Sai Sannu (Binta A. Wali), Guguwar So (Mukhtar Isa Adamu), Halacci (Sadiya Baba Yusuf), Maza Sai Sannu (Binta A. Wali), Mugun aboki (Dan Barno), Shan Koko (Jamila Abdulkadir) da sauransu. Kona su ba shi zai sa a daina irin wannan rubutun ba, domin konawar ba ta shiga zuciyar mutane ta inda za a fahimci dalilin konarwar saboda dalilai uku.

Na farko dai wanda ya sayi littafin shi ya yi asara – ba marubuci ba, ba kuma dan kasuwa mai sayar da littafin ba. In da gaske a ke so a yi, da sai a je wajen dillalan littattafan a kasuwa, domin su ne suke bugawa, a tattara a kona a can. Amma ka ga ai ba haka a ka yi ba – makaranta aka je, aka sami dalibai wadanda suka sayi littattafan da kudinsu, ba da kudin hukuma ba, aka ce su fito a kona su. Ba ayi komai ba a nan, domin dama sun gama karanta littattafan – watakila ma sun rasa yadda za su yi da su; wadansu ma ba dole ne a ce littattafan da ake bukata a kona suka fito da su ba, sa iya fitar da littafin karatun da ba sa so (misali, Lissafi), su kawo a kona. A nan waye ya yi asara? Kuma wacce nasara a ka ci?

Na biyu, in da so a ke a yi konar ta yadda za a isar da sako, da sai a tattara marubuta waje daya – misali laburaren Murtala Muhammad – sannan a ce kowa ya kawo littafin da ya rubuta, sannan a tara a banka musu wuta. Idan an yi haka, sai a ga mai zai faru? To amma ba a bi wadannan hanyoyin ba.

Na uku, dole a tambayi marubuta ire-iren wadannan littattafan – menene manufar rubuta su? Kada a manta, kamar yadda wani marubuci ya taba fada, ‘yancin ka na ka yi kutufo da hannunka a iska ya tsaya daidai inda hanci na ya fara. Saboda haka idan marubuci na da ‘yancin rubuta abin da ya ga dama, dole ya nauyaya da sakamakon abin ya rubuta da kuma abin da zai haifar.

4. Kowacce hanya ce mafi dacewa da gwamnati ya kamata ta yi amfani da ita, domin daidaita sahun marubuta?

Nunawa su kansu marubutan muhimmancin jagorancin jama’a wajen rubutu. Idan marubuci zai dauki cewa yana da ‘yancin ya yi duk irin rubutun da ya ga dama, to dole ya auna sakamakon rubutun da zai yi. Yi wa fasihi takunkumi ko katanga ba shi ne mafita ba – domin da takunkumin da katangar duk ba sa aiki. Hasali ma dai dada lalata lamarin su ke yi, domin da zarar an ce an haramta wani abu, to tabbas za ka ga dangin shaidan na rububin abin. Kungiyar Marubuta ta Kasa, reshen Kano, ANA ta taba haramta wani littafi wai shi [ufana kusan shekaru shida da suka wuce. Kafin ka ce kwabo, kudin littafin ya tashi daga naira talatin zuwa naira dari, kuma aka dinga tururuwa neman sa. Dan-da-nan ya bace a kasuwa saboda rububi. To haka ma wadannan littafan da aka kona. Tabbas da mutane sun san sunayensu, to da marubutan sun zama miliniyoyi saboda rububin littattafan za a dinga yi. Abin la’akari a nan shi ne, inda duniya na raye, to [an Adam na tare da Iblis. In kuwa haka ne, to ire-iren wadannan abubuwa za ci gaba da addabar jama’ar har busa kaho.

Saboda haka dole marubuta su yi la’akari da hakkin jama’a a kansu – wannan shi ne katangar da su za su iya yi da kansu, amma ba katangar hukuma ba. Sanin hanyar da za a yi wannan shi ne yadda hukumar A Daidaita Sahu za ta bi domin maganta lamarin. Af, ji nake ita dai wannan hukumar mai kona littattafai, ita ce ta gayyaci marubutan a 2005, ta ba su kwangilar rubutu irin wanda hukumar ke so? Sai yanzu ne kuma za su ce wadannan mutanen lalatattu ne? Ashe ka ga da sake kenan.

4 comments:

Cheetarah said...

hmm dogo labari, wana jerida a hausa nei duka? ba turenchi? wanda bai jin hausa fa?

Kiibaati said...

I enjoy your blog but I don't speak no hausa. How far now? How can I get a translation?

? said...

Greetings!
This is only to reserve a seat here and I will be back to comment properly after exploring this excellent blog.
Ill be back. However, just in case I am taking too long, please give me a shout.
See you shortly.

Anonymous said...

Malam Ibrahim, Great work! More grease to your elbows.