Tuesday 24 July 2007

Joe McIntyre (Malam Gambo) a Kano





A ranar 28 ga Yuni 2007 ne wani sanannen Baturen Ingila mazaunin Jamus mai suna Dakta Joe McIntyre ya ziyarci Kano. Da ma ya taba zama a birnin na Dabo, kuma manazarcin harshen Hausa ne. Yana jin Hausa kamar jakin Kano!

Kungiyar ANA ta Kano, tare da hadin gwiwar Cibiyar Nazarin Al'adun Hausawa (inda ni darakta ne) sun shirya wani taro a dakin karatu na Murtala Muhammed, inda aka yi jawabai. Dakta McIntyre, wanda sunan sa na Hausa Malam Gambo, ya yi jawabi kan Hausawa 'yan ci-rani a Hamburg, inda ya nuna taskun da Hausawa (da 'yan Afrika masu kiran kan su Hausawa) suke sha a kasar Jamus - duk wajen bidar kudi. Da Hausa radau ya yi jawabin. Duk da yake akwai karin harshe kadan, kai idan ba a fada maka ba, ba za ka rantse cewa ba Bahaushe ba ne yake magana. Ya burge kowa!

Na halarci taron. Ga hotunan wasu sassa nan na taron, masu nuna mahalarta (cikin su kuwa har da ni! Dubi hoto na biyu, ina sanye da koriyar hula). Farfesa Abdalla Uba Adamu ne ya aiko mani da hotunan, kuma shi ya dauke su. A hoton farko, inda Malam Gambo ke jawabi, ana iya ganin Farfesa Abdalla sanye da tabarau.

A hoto na uku, inda mata suke, akwai mata ta Binta a ciki.

No comments: