Wednesday, 22 August 2007

HIRA DA BOBO* Gyaran waya ya ba abokin sa, shi
Kuma ya kwafi majigin daga ciki

* Bobo ya rantse sau 16 cikin guntuwar tattaunawa

* Ya na neman afuwar dukkan Musulmi


ALHAJI Usman Bobo, dan canjin nan da ya dauki majigin batsa tare da Maryam Usman Hiyana (ga hoton ta nan a sama), ya b'ace b'at tun daga lokacin da sirrin su ya tonu. A farkon faruwar lamarin, shugabannin ’yan fim na Kano sun kira shi sun nuna masa bacin ran su kan wannan abu. Majiyar mujallar Fim ta ce mutumin ya yi nadama a gare su, har ya na cewa wallahi shi ba kan sa ya ke ji ba, yarinyar ya ke ji. An ba mujallar lambobin wayar Usman, amma ya ki samuwa.

Kwatsam, a ranar Lahadi, 19 ga Agusta, sai ga labarin Bobo ya ~ullo a sashen Hausa na BBC, a shirin su na rana. Duk da yake akwai abubuwa da yawa da ba a tambayi mutumin ba, amma hirar ta kara haske kan wannan rikirkitaccen lamari. A hirar, Bobo ya bayyana cewa ya na zaman boyo ne a yanzu, kuma ya nuna tsantsar nadama, sa’annan ya yi kira ga jama’a da su yafe masa wannan ta~argaza da ya tafka. Ga yadda hirar ta kasance:

BBC: Ko me ya sa ka aikata wannan abin kunya?
BOBO: Wallahi tallahi ba na yi da gayya ba ne.

BBC: To kamar ya abin ya taso daga gare ka, kai?
BOBO: Wallahi abin nan sirri ne. Wani aboki na ne ya saci wayar nan... wani aboki na, wallahi tallahi, wayar nan na ba shi ya yi min gyaran ta. Ka na ji na ko? Kuma abin nan an yi shi sama da shekara daya, wajen shekara daya da wata tara kenan. Kuma wallahi tallahi na yi nadama. Kuma ina fatan don Allah don Annabi duniya ta yafe min abin da ya faru. Wallahi, domin duniya... saboda Allah da Annabi su yafe min. Abin nan ba wai na yi shi ba ne ko da gayya ko da wani abu, ka fahimta... ko da fariya. Wallahi sace wayar nan aka yi, wallahi tallahi, abin ya fita.

BBC: Kai ne dai ka yi abin a waya aka dauka. Me ya sa tun asali din, misali, ka dau abin a cikin waya ka yi shi, duk da ka san ba abu ne da ya dace ka dauka a waya ba, misali.
BOBO: Ai lokacin na ke gaya maka, tun a lokacin na riga na goge, wani ne ya sace abin.

BBC: To yanzu yaya ka ke ji game da wannan abu da ya taso haka?
BOBO: Bakin ciki, wallahi! Abin ya na damu na sosai, wallahi tallahi! Wallahi ba na iya shiga jama’a, ba na iya yin komai wallahi.

BBC: Yanzu ka na sane da cewa akwai wadanda ma su ke cewa lallai da kai da ita wannan yarinyar da ku ka yi wannan abu, kamata ya yi sai an hukunta ku saboda ba kan ku kawai ku ka yi wa ba, kun yi wa mutane, kun janyo wa al’umar Musulman arewacin Nijeriya da ma duk inda su ke wani abu na kaskanci.
BOBO: E, shi ne na ke rokon Musulman duniya. Ina nuna damuwa ta a kan laifin da na yi wa Musulunci da Musulmai. Shi ya sa na ke neman gafara ga Musulman duniya su yafe min saboda Allah da Annabi. Kuma ina fatan Allah Ubangiji ya yafe min, kuma ya shirye mu gaba daya.

BBC: Kamar zuwa yanzu ka san halin da ita yarinyar da ku ka dauki hoton ta ke ciki? Ka yi magana da ita zuwa yanzu?
BOBO: Wallahi tallahi ba mu yi magana ba, amma na san ta na cikin damuwa wallahi.

BBC: Daga lokacin da abin ya bazu zuwa yanzu, ka na ci gaba da harkokin sana’ar ka ko kuwa me ya ke faruwa?
BOBO: Wallahi tallahi ba ma wanda ya san inda na ke a halin yanzu, don na gudu, na bar ma garin gaba daya, wallahi.

BBC: Ka na nufin ba ma a cikin Legas din ka ke ba a yanzu?
BOBO: Wallahi ba a cikin Legas na ke ba.

12 comments:

Zahratique said...

Wanna al mari na kulle min kai wallahi. Allah dai ya kyauta, kuma Allah ya gyara. amin

Anonymous said...

To Innalilahi wa ina Ilaihir raji'un. God has bring us to the world and we've just to apologise to the almighty allah for a forgiveness and also Blessings: Because we all do know that he's an Acquainted allah that wants a Polite admitting and he will be surely there for us. We should remember it has already happen and there is no way to clean it out from the Hausa Fulani whatever you call it. But as most people all said we all have our sins which is even more greater than this one that has ocured but everyone leave it to them selfs and God has a reason for expossing this out. So Jamatul Islam remember Him who exposse them knows the best than you and have his own good reason for that. I hope he knows the best and he will grantly cleqn our sins for us insha Allah. More blessing to islam!!

Aliyu Bun Mohammed Fulani.

Anonymous said...

To Innalilahi wa ina Ilaihir raji'un. God has bring us to the world and we've just to apologise to the almighty allah for a forgiveness and also Blessings: Because we all do know that he's an Acquainted allah that wants a Polite admitting and he will be surely there for us. We should remember it has already happen and there is no way to clean it out from the Hausa Fulani whatever you call it. But as most people all said we all have our sins which is even more greater than this one that has ocured but everyone leave it to them selfs and God has a reason for expossing this out. So Jamatul Islam remember Him who exposse them knows the best than you and have his own good reason for that. I hope he knows the best and he will grantly cleqn our sins for us insha Allah. More blessing for islam!!

Aliyu Bun Mohammed Fulani.

Anonymous said...

gaskiya bobo ka cuci yarinyar kanemi gafarar ta don kasan allah zai saka mata. suleiman ibrahim

محمد مصطفى الشيخ محمد برنوما said...

wannan mutum ya nunu cewa shi yahayi kololowar rashin daa da cin amana
saboda yarinya miskina ya yaudareta yazo kuma ya hada surarta ya kharraba sum arta har yauma takuon,
subhamallah bansan akwai irin wadannan bunsurayen a nigeria ba ,
babu shakka allah zai sakawa diyannan ,
ko ba komai ka nunawa duniya cewa kai ba dan mutanenebe

Anonymous said...

Sadi Abdulrahman Kofar mata Kano.

To Maryam Hiyana wannan abin da kikayi kin tabbatar wa da duniya cewa abin da a ke zargin yan wasan hausa na aikata alfasha gaskiyane,ALLAH ya shirye ku ya sa kudawo hanya madaideciya.
saboda haka sai kiyi tayin istingifari ko Allah yayafe . mukuma Allah ya shiryar damu amin.

Anonymous said...

cheap wow power leveling buy wow gold cheapest wow power leveling CHEAP wow gold BUY power leveling CHEAPEST wow powerleveling
wow goldwow goldwow goldwow goldweiwei

Anonymous said...

We are in this world juts to learn new experiences, for us to evolve in a love environment, too bad that we as a society are not doing it, more and more we are heading to destruction.


------------------------------------------
generic viagra

mustapha said...

toh video din yana wane website

You will be seen as said...

Ni naji dd da aka goge video a cikin kowane website na internet kuma munasa ran Allah ya karbi tuban su

muhsin said...

allah kare alummar musulmi

Unknown said...

Allah ya shirya,