Friday 23 March 2007

MAMMAN SHATA - BA RABO DA GWANI BA...!

A yau ga wata 'yar waka da na yi wa marigayi Alhaji Mamman Shata. Rasuwar Sarkin Daura Bashar kwanan nan ce ta tuno mani da wakar, wadda an buga ta a littafin tarihin Shata da muka yi ni da wasu abokai na. Bismilla:

GA MU NAN ZUWA!
(Wak'ar Ta'aziyyar Mamman Shata)


Ya Rabbi k'aran da ilmi na shirya
'Yar wagga wak'a da yau zan karanta.

Na shirya wak'ar yabon nawa gwarzo,
Dakta Muhammadu Alhaji Shata.

Kun san shi ko da fa ban bayyana ba:
Sarkin Mawak'a na dukkan k'asa ta.

Shi yai wafati gabanin na shiryo
'Yan wanga baiti da yau zan tak'aita.

Rok'o nake Jallah bud'an k'wak'walwa,
Da za ni wak'ar fasihin mu Shata.

Mannanu, K'uddusi, ar-Rahamanu,
Shi bai da farko da k'arshen sarauta.

Sarkin da ba d'a garai ko aboki,
Shi ba iyaye garai ko ko mata.

Shi yay yi kowa da komai ku gane,
Shi yah halitto fasihin mu Shata.

Na shaida Manzon Sa Mamman na Dija
Ya zo da sak'o da duk mun karanta.

Ya ce ga Allah mu zam sujjadawa,
Ko wak' k'i lallai ku san ya yi wauta.

Shata a farko na wannan bayani,
Musawa kakan sa shi yak kafa ta.

Sannan a nan ne garin haihuwa tai,
Iroro Yaro uba ne ga Shata.

Nan yay yi wargi da kiwo da noma,
Kakan sa Idi, uwa Lariya ta.

Shi ba ya doko a layi ga tsara,
Hatta a jeji ciki yai bajinta.

Shanu, awakai, tumakan sa kwata,
Su yai ta kiwo da sandar sa Shata.

Yai kasuwanci na goro a baka,
Hatta alewa ya na, "Zo ku sha ta!"

Baban sa bai so ya zam rera wak'a,
Shi ya fi son sui ta noma da Shata.

Hangen sa d'an Fillo irlin sa noma,
Ko yai ta kiwon bissai har farauta.

Amma a ce yai rawar dandali kam,
Kai, ya yi hauka, a nan bai da gata!

Balle a ce d'an taro har da sisi
An ba shi, kunya a nan ya ko sha ta.

Amma bisani ya ce, "Kai, su Shata,
Iko na Allah a nan an k'adarta!"

Ya k'yale Mamman ganin ya yi nisa
Can gun rawar duniya shi ya taka.

Muryar sa zak'i ta ke yi Mahamman,
Tamkar zuma in ka saurari Shata.

Sam ba fasihi kama tai a wak'a,
In dai kid'a za a sanya shi kwata.

Na gode Allah Ta'ala da yay yo
Wannan fasihi cikin nan k'asa ta.

Domin raha ne ya ke shirya baitin
'Yan dambe hatta giya wai ku sha ta.

Ya nuna illar mashayi ku gane
Don gargad'i, ya fi k'aunar ku bar ta.

Ai ya yi wak'ar b'arai don a dara,
Can ya tab'o masu lale ta karta.

Dukkan sarakan k'asar nan ta Hausa
Yai musu wak'a Muhammadu Shata.

Shi yai yi wak'ar fatake da tela,
Bai bar manoma had'a har masunta.

Mai sanya khaki da mai d'aura k'irgi,
Mai kama biro da mai tuk'a mota.

Ya k'era wak'a ta Malam da gardi,
Hatta kadoji a domin bajinta.

D'an kasuwa mai saye don ya saida,
Ko karuwai masu aikin k'azanta.

Bai k'yale gurgu, makaho da kurma
In ya yi wak'ar su zo don su ji ta.

Hatta su Manzo, Sahabbai, waliyyai,
Ya rera wak'ar su mun ji ta Shata.

Ya burge kowa a birni da k'auye,
Yaro da babba maza har da mata.

Sun ji shi sun so shi sun so ganin shi,
Sun bai Muhammadu dubbai na kyauta.

Sun ba shi kurd'i, gidaje, dawakai,
Gona, tufafi, da mata da mota.

Arna, Musulmi, had'a majusawan
Kurmi gani nai su ke sun k'agauta.

Jarman Kano D'ankabo ya rik'e shi,
Yai mai dubun arzuka duk na gata.

Sarki na Daura Bashar kar ku manta,
Tamkar uba ne a gu nasa Shata.

K'auna da yarda tsakanin dukkan su,
Mamman da Mamman a rayin su kwata,

Ai ta yi kauri da k'arfin dad'ewa,
Har ma ya koma ga Allan sa Shata.

Sarki Bashar ne ya sanya shi hanya,
Mai kyau da dad'i a domin ya bi ta.

Jarma ya d'auke shi ya sa shi jirgi
Sun je Amurka da London su Shata.

Can ya yi kallon Baturai tsanake,
Ya k'ara wayon zaman ran sa Shata.

Har ya yi wak'a a birni na L.A.,
Hausar sa Modibbo ne ya fasarta.

Sai ga Baturai a tsuke da wando,
Sun sanya naktaye rigar su kwat ta.

Amma kalangan Muhamman amon su
Ya sa su zarya da juyi ga Shata.

Mamman hali nai ya na nan da kyawu,
Don ba ya sharri ga me mai mugunta.

Ya tsaida sunna ta aure hak'ik'an,
Ya haifi 'ya'ya na sunna da mata.

Mata ta farko da am ba shi aure,
Auren budurwar sa sunan ta Binta.

Bakori nan ne akai wanga aure,
Dangin sa sun je su shaida ga Shata.

Shi gaskiya ce ya ke so Mahamman,
K'arya garai ta fi d'aci na gauta.

Ni na fa zauna da Mamman a zaure,
A Funtuwa k'wag gida nai da kwalta.

A kan kushin nan sarakin ka hard'e,
Nan ko gaba nai mutane ka kwanta.

Ga shimfid'u an baje mun ko zauna,
Mun bud'e kunne, idanu ga Shata.

Zance ake yi kawai kan siyasa,
Ko kan mutane da ke rafka wauta.

Ko ko a zanta a kan masu himma,
Ko masu k'arfin hali 'yan bajinta.

Shi ma garai mun ji dad'in ruwaya,
K'walwar sa kullum batu ya cika ta.

In an ka zauna da Shata a zauren,
Shi ba ya ~oyon batu mai bajinta.

In ya yi arba da insu da jinnu,
Take a nan gun ya na ko baje ta.

Zai ma ruwayar ka san ba ya tsoro:
Ko da wuta ce katsam zai shige ta.

In tsamiya ce da jinnu a kan ta,
Bai waiwaye take ne zai haye ta.

Ko ko ruwa wanda manya ka shakka,
Mamman ciki za ya afka da mota.

In ya ga ramin kumurci da zurfi,
Hannu ya kan sa ya shak'o wuyan ta.

Ran nan Aliyu na K'ank'ara ya ce
Bai yarda Shata mutum an halitta.

"Kai shi fa Mamman a kai nai da motsi,
In an gaya ma ka zan gaskata ta.

"Shi ga shi tsaf d'an'adam ne a fuska,
To aljani ne a zuci da hanta.

"Ai an yi sa'a da bai ba da tsoro,
Sai dai a so shi Muhammadu Shata."

An so shi Najeriya kewayen ta,
Hatta k'asashen da ak kewayen ta.

Don ya yi yawon k'asashe ku duba,
Har Ghana, Burkina ma ya shige ta.

Har Saliyo, Kamaru da Chadi,
Ya san su sun san shi Alhaji Shata.

Ai ma Nijar san da Mamman ya lek'a,
Babban gida sun ka baishe shi mata.

Lallai Hurera uwa mai biyayya,
'Yar malamai Inna mata ga Shata.

Tun ran da Allah ya sa ta k'asan sa,
Ta bi shi rayin sa duk ta wadata.

Uwargida ce gidan nan na Baba,
Su su uku kun ga sun mai wadata.

Domin akwai 'yar sarauta gidan sa,
Ta-Falgore wadda an ba shi kyauta.

Lallai Khadija fara kin yi kirki,
Allah ya zan sa ki Firdausi kyauta.

Ke ma Ta-Dukke fara kin biyayya
Gun Baba Alhaji Mamuda Shata.

Ba haihuwa gun ki Yaya Amina,
Ke cimma Mamman a Aljanna kyauta.

Ran nan fa tsufa ya karyo wa Mamman
Ga ciwuka rayuwar sun rufe ta.

Don ya yi ciwo na k'oda da zafi,
Har Jidda an kai shi baban mu Shata.

An samu sauk'i sa'annan fa ciwon
Yay yo kwana ya ko banke shi Shata.

Duk d'an'adam ajizi ne ku gane,
Shi rayuwar tasa an rurrubuta.

Farkonka k'arshen ka komai a tsare,
Ai ba tsimi ko dabarar gudun ta.

Domin hakan kun ga tilas Muhamman
Ya kai gaci babu sauran bajinta.

Birnin Kano inda Mamman ya haska,
Can ne a k'arshe a dama ya kwanta.

An mai kushewa a Daura a ranar,
Sarki Bashar ne ya sallaci Shata.

Na gode Allah da naz zan sanin shi,
Ya san mu sosai da baban mu, Shata.

Ai sun yi huld'a uba na da Shata,
Ni ma na zo na ci duk moriyar ta.

Taro mu zauna mu na mai du'a'i,
Mannanu gafarci Alhaji Shata.

Allah jik'an wanga babban fasihi,
Yafe kure nai da shi d'in ya lafta.

Sanya shi Lambu na Firdausi, Jallah,
Kafin mu cim mai a can baba Shata.

Mu ma ka yafe mu laifin mu, amin,
Domin amincin Muhamman na Binta.

Zan sanya aya a nan kar na zarce,
Ai alk'awar nay yi kan zan tak'aita.

Baiti d'ari ne cikin wanga wak'e,
Alhamdu lillahi don na gama ta.

Malam ka k'irga da kyau don ka gane,
In nai kure sai ka yafe ni wauta.

Ya Rabbi rok'o na ke yi da k'ari,
Saka wa Shata da Lambun Ka kyauta.

Amin da amin da amin da amin,
Nai fatiha 'yan'uwa na dire ta!

3 comments:

Anonymous said...

Hey, Im a Nigerian in UK, Im interesting in listening to Mamman Shata Songs, I search on the youtube, non is there. Can u guys help upload it? U know it is free, and it will help seperate our culture. It will be nice if u will assist Nigerians abroad

Thanks

Anonymous said...

I think Mamman Shata Songs are full of his essense. I would love to listen to new songs from him. I heard he wants to launch an album in English under the title generic viagra

get rich said...

join illuminati today to be rich and famus.Are you a business Man or Woman,Artist, power. Political,Musician,Student,do you want to be rich,famous,powerful in life,here is your chance.Here is my life story my name is Dan Jerry I am here to share my testimony on how I join the great brotherhood Illuminati and my life story was change immediately i become member. I was very poor no job and I has no money to even feed and take care of my family I was confuse in life I don’t know what to do I try all my possible best to get money but no one work out for me each day I share tears, I was just looking out my family no money to take care of them until one day I decided to join the great Illuminati , I come across them in the internet I never believe I said let me try I email them.all what they said we happen in my life just started it was like a dream to me they really change my story totally . They give me the sum of $1,200,000 and many thing. through the Illuminati I was able to become rich, and have many industry on my own and become famous and popular in my country , today me and my family is living happily and I am the most happiest man here is the opportunity for you to join the Illuminati and become rich and famous in life and be like other people and you life we be change totally.If you are interested in joining the great brotherhood Illuminati.then contact him whatsspa +2347051758952 or you need my assistance   morganilluminatirich@gmail.com