Tuesday 5 October 2010

Malam Turi: Ba rabo da gwani ba...


A ranar 17 ga Satumba, 2010, Allah Ya ]auki ran Malam Turi Muhammadu, a Kaduna. Shekarun sa 70 a duniya. Kafin rasuwar tasa, ya ta~a ri}e mu}amin editan jaridar New Nigerian sannan daga bisani ya zama manajan daraktan kamfanin da ke buga jaridar. Malam Turi fitaccen ]an jarida ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawa ga ci-gaban aikin jarida a }asar nan. Sai dai kash! yawancin mutane, ciki kuwa har da wa]anda su ka san shi, farin sani, ba su kula sosai da nasarorin da malamin ya samu a wannan fagen ba har sai da ya koma ga Mahaliccin sa. Da ma akwai irin wa]annan mutanen jingim a garuruwan mu – wa]anda su ka yi abin a zo a gani amma ba a damu ba har sai wani abu ya faru gare su, musamman ma mutuwa.

Kamar yadda mu ka gani a makon jiya, ’yan jarida da dama a Nijeriya sun ci moriyar tarayyar su da Malam Turi. Da yawa, ya kasance uba a gare su a lokacin da ya ke aikin jarida da kuma bayan ya bar aikin. Daga rubuce-rubucen ta’aziyya da ’yan jarida irin su Sam Nda-Isaiah da Mohammed Haruna da Clem Baiye da Adamu Adamu da wasu su ka yi a jaridu, za mu iya fahimtar cewa Malam Turi babban masani ne a wannan fage, wanda ya yi amfani da }warewar sa don ciyar da aikin jarida gaba, sannan mutum ne mai son ganin cewa an ci gaba da ya]a }udirorin dalilan kafa jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, ba kawai ga kamfanin ba a yau, a’a har ma ga maza da matan da su ka ta~a yin aiki a kamfanin amma yanzu su na rubutu ko gudanar da wasu kafafen ya]a labaran na Arewa. Don haka ne ma ya ke sa ido kan mutanen da ke aiki a wasu jaridu ko ko gudanar da jaridun da ke da ala}a ta asali da kamfanin New Nigerian, wato jaridu irin su Daily Trust, Leadership da Peoples Daily. Na tabbatar da cewa ’yan jarida da dama da ke aiki a wa]annan jaridun – da kuma wa]anda har yanzu su ke a New Nigerian a yau – za su shaida cewa Malam Turi ya na daga cikin dattawa }alilan da su ka damu da yin mu’amala da su, su na tuntu~ar su, ba don komai ba sai don ganin cewa sun ci gaba da yin aiki a bisa turbar kyakkyawar tarbiyya da bin }a’idojin aikin jarida. Wasu daga cikin su, ya ]auke su kamar ’ya’yan sa a aikin, yayin da wasu kuma ya ]auke su jikokin sa.

Ni ]in nan ina daga cikin irin wa]annan mutanen. Na fara ha]uwa da Malam Turi shekaru 13 daidai da su ka wuce, lokacin da ya aiko mani da wata wasi}a da ya rubuta da hannun sa ya ce ya na so ya gan ni. Na yi mamaki }warai, tare da jin da]e, a ce babban mutum kamar sa ne ya ke so ya gan ni. A takardar, ya ce ya samu labarin cewa ina }o}arin rubuta tarihin sarkin mawa}an Hausa, Alhaji Mamman Shata, kuma ya na so mu sadu don ya fa]a mani wasu abubuwa wa]anda }ila su taimaka mani a aikin. A lokacin, ban ta~a ganin Malam Turi ba, illa iyaka dai na kan ji labarin sa a matsayin fitaccen ]an jarida da ake girmamawa. To amma dai na san cewa ’yan jarida su kan yi sha’awar abubuwa da dama a rayuwa, wato ban da aikin su, ciki kuwa har da son ka]e-ka]e da wa}e-wa}e. Da ma tun kafin lokacin, wani tsohon manajan daraktan kamfanin buga jaridun New Nigerian ]in, wato Alhaji Tukur Othman, ya ta~a kira na ya yi doguwar hira da ni kan dangantakar Shata da wasu manyan ’yan bokon Arewa da ke zaune a Kaduna a lokacin da Shatan ya ke kan }ololuwar tashe, irin su Alhaji Sani Zangon Daura.

Na samu Malam Turi a gidan sa da ke unguwar Malali, Kaduna, a ran 22 ga Yuli, 1997, kamar yadda mu ka aje. Ba zan ta~a mantawa da wannan ha]uwar ba. Na farko, na yi sha’awar rashin girman kan sa da }o}arin sa na faranta mani rai. Malamin ya ce lallai in tashi daga }asa inda na zauna na har]e don girmamawa, in koma kan kujera kusa da shi. Sa’annan ya sa aka kawo mana abinci. Da }yar na samu na ]an ci abincin domin gwarzantakar sa a fagen da na ke fafutikar yin nawa sunan duk ta miskile ni.
A tattaunawar mu, Malam ya nuna mani cewa ya na biye da abubuwan da na ke yi a fagen aikin jarida. Ya san cewa na ta~a ri}e mu}amin mujallar Rana da mujallar Hotline shekaru biyar da su ka gabata, bayan na yi wasu shekarun a kamfanin jaridar The Reporter, na kuma samo digiri na biyu a aikin jarida a }asar Birtaniya, sannan yanzu kuma ina aiki a New Nigerian a matsayin ]aya daga cikin }usoshin gidan. Ita ma tattaunawar da mu ka yi a kan Mamman Shata, ta karantar da ni abubuwa da dama. Ni a da na ]auka na san duk wani abu game da Shata ta yadda ba wani sabon abu da wani zai iya fa]a mani kuma, ballantana kuma wani Banufe. To amma Malam ne ya fa]a mani wani abu da ban sani ba: wato yawan wa}o}in zambo da Shata ya yi bai kai ko cikin cokalin wa]anda ya yi na yabo ba, wanda hakan ya taimaka masa wajen samun }arin farin jini da kuma ]aukaka. Da na dubi wannan magana da kyau, sai na ga gaskiya haka ]in ne. Wa]annan bayanai da Malam Turi ya yi mani su na cikin littafin da mu ka yi mai taken Shata Ikon Allah! mai shafi 604, wanda aka wallafa a cikin 2006, kuma mun nuna cewa shi ne ya fa]a.

Mu’amalar mu da Malam ta ci gaba ne kwan-gaba-kwan baya; sai a jima ba mu ha]u ba, wanda laifi na ne. Ya kan so mu ha]u a kai a kai, to amma sai in kasa kamar yadda na ke so. Na kan la~e da cewa saboda ina da gida biyu ne, ]aya a Kaduna ]aya a Kano. Amma yanzu idan na tuna baya sai in ga cewa wannan ba }wa}}warar hujja ba ce, kuma na yi nadamar rashin kusantar Malam kamar yadda ya ke so. Na yi nadamar rashin yin kiwo sosai a cikin faffa]ar gonar ilimin sa don in }aru da basirar sa, wanda a shirye ya ke ya }osar da ni daga gare ta. Na kan ]an yi }o}arin ganin sa jefi-jefi. Kuma a koyaushe ya kan kar~e ni hannu biyu-biyu, tare da tambaya ta, “Shin wane ya fa]a maka cewa ya gaida mani da kai lokacin da ya zo nan gidan?”

Ba shakka, idan abokai na sun je gidan sa su kan ce mani, “Na je gidan Malam Turi kwanan nan, ya ce in gaida kai.” Da zarar na ji haka, sai in ji kunya ta rufe ni. Nan da nan na kan yi al}awarin cewa lallai zan ziyarce shi don mu ci gaba da wata tattaunawa da wata}ila mu ka fara a zuwan da na yi gidan sa can a baya.

A koyaushe Malam ya na so in ci gaba da zama ]an jarida, ya kan ce Arewa ta na bu}atar mutane iri na a aikin. Amma bayan na yi aikin shekara hu]u a New Nigerian, inda na ri}e mu}amai daban-daban kamar su editan ma}aloli, editan labaran }asashen waje, editan adabi, sakataren kwamitin editoci, har zuwa mataimakin edita, sai na aje aikin. Dalili shi ne an yi wata shida ba a biya albashi ba, wanda ya sa na fara tunanin irin makoma ta idan na zauna a aikin da ba zai iya ba ni damar ci da iyali na ba. A }arshe dai, na dawo aikin jaridar, kuma na ji da]in hakan.

Malam Turi mutumin }warai ne wanda ke son ganin ci-gaban Arewa. Abin ba}in ciki shi ne bai yi tasiri a siyasa da ya shiga ba, bai samu cin za~en zama sanata ba bayan ya bar aiki a New Nigerian a cikin 1980. Ya yi la’akari da cewa siyasa mugun wargi ne, wanda bai kamaci mutane irin sa ba. Na san dai cewa ]aya daga cikin abubuwan da bai ji da]in su ba shi ne koma-bayan da jaridar New Nigerian ta samu a matsayin babbar jarida daga Arewa. A rubutun ta’aziyya da Malam Mohammed Haruna ya yi a Daily Trust ta ran Larabar makon jiya, ya yi nuni da cewa rugujewar }imar jaridar da koma-bayan ta ya fara ne daga lokacin da Malam Turi ya bar aiki a kamfanin, domin shugabannin kamfanin da su ka zo bayan sa sun sauya turbar da wa]anda su ka kafa kamfanin su ka ]ora kamfanin a kai. Ni ma na yarda haka ne. Manufar littafin da Malam Turi ya rubuta na tarihin jaridar, mai suna Courage and Conviction, ita ce a isar da wannan sa}on ta hanyar bayar da cikakken tarihin jaridar a cikin shekarun ta ashirin na farko inda ta cimma gagarumar nasara. Ka dubi dai jaridar da ke buga kwafe 250,000 a kullum lokacin da ta ke tashe, sai da ta koma ta na buga kwafe 2,000 a wani lokaci. Duk da yake an sha yin ho~~asan dawo da martabar jaridar a baya, abin ya }azanta a cikin shekaru kamar goma da su ka gabata. A gaskiya, babbar karramawar da za a yi wa Malam Turi (Allah Ya ji}an sa) har ma da mutane irin sa da su ka yi aiki tu}uru don gina New Nigerian, ita ce a yi dukkan abin da ya dace a yi don dawo da }arfin jaridar kamar yadda ya ke a da.

-----
An buga wannan makalar a LEADERSHIP HAUSA ta ran 1 ga Oktoba, 2010

No comments: