Friday 21 January 2011

Hattara da ramuka a gaba!

A jiya Alhamis ne ]imbin ’ya’yan jam’iyyar PDP, musamman dalaget, su ka yi kwamba a Abuja domin gudanar da za~en fitar da gwani wanda zai yi takarar zama shugaban }asa a }ar}ashin inuwar jam’iyyar su. Tun kafin ranar, dalaget da sauran membobin PDP ]in su ka dinga antayowa zuwa cikin babban birnin na tarayya, ta yadda ko ya zuwa ran Talata da wuya mutum ya samu ]aki a dukkan otal-otal na garin. Su ma wuraren cin abinci sun cika ma}il da ba}in.

In ba domin batun ya shafi PDP ba ne, to da wata}ila sai mu zuba na mujiya kurum, mu yi kallon bada}alar da ake yi. To amma PDP ta na kurarin cewa ita ce jam’iyyar siyasa da ta fi kowace girma a nahiyar Afrika. Haka kuma ita ce jam’iyyar da ke mulki a Nijeriya. Ta haifar da shugabannin }asar har guda uku daga lokacin da aka fara Jamhuriya ta Hu]u, domin kuwa ita ce aka ce ta lashe za~u~~ukan shugaban }asa da aka yi a cikin 1999 da 2003 da kuma 2007. Sannan ita ce ke da rinjaye a yawancin jihohin tarayyar }asar nan, da kuma Majalisar Tarayya. {ungiyar Gwamnonin Nijeriya yawanci membobin PDP ne su ka cika ta, kuma ta na daga cikin }ungiyoyi masu fa]a a ji a }asar nan. Bugu da }ari, duk wasu tsare-tsare na mulkin }asa wa]anda PDP ta fito da su kuma ta ke aiwatarwa, wa]anda aka ]ibiya a kan ]imbin ku]a]en shiga da ke zuwa daga safarar man fetur, su na shafar rayuwar jama’ar }asar nan. Saboda haka, ko an }i ko an so, za~en wanda zai tsaya takarar zama shugaban }asa na jam’iyyar ya na da matu}ar tasiri a rayuwar ’yan Nijeriya, ya Allah tasirin nan mai kyau ne ko akasin haka. Don haka, tilas ne mu damu kan wannan lamari, domin duk shukar da za a yi a wannan gangami zai iya shafar rayuwar mu kusan ta kowane ~angare.

Kamar yadda kowa ya sani ne, wannan ne karo na farko da shugaba mai ci yanzu, wato Dakta Goodluck Jonathan, ya ke takarar wani mu}ami da sunan sa. A da, shi sifiya-taya ne kurum - inda a Jihar Bayelsa ya yi mataimakin gwamna, sannan a 2007 ya zama mataimakin shugaban }asa. A yanzu ne ya ke gwajin farin jinin sa a karo na farko. Idan har ya na so ya zama za~a~~en shugaban }asa, to, na farko sai ya tsallake sira]in za~en da aka taru a yi a jiya, 13 ga Janairu. Idan ya ci, sai kuma shallake sira]i na biyu: wato kada abokan hamayyar sa wa]anda sauran jam’iyyu za su tsayar. Duk wa]annan sira]an, ba wasan yara ba ne. Aiki ne wurjanjan. Ko a kogin farko da ya ke }o}arin hayewa yanzu, akwai maridan kadoji a ciki; Jonathan ya na bugawa ne a za~en fidda gwani mafi tsauri a takarar zama shugaban }asa da aka ta~a yi a tarihin siyasar Nijeriya.

Hakan na faruwa ne saboda abin da masu nazarin al’amuran yau da kullum su ke kallo a matsayin da~a wa ciki wu}a da PDP ta yi: wato yarjejeniyar kar~a-kar~ar shugabancin }asa tsakanin arewa da kudu da ta rattaba hannu a kai. Jonathan ya ]are kujerar shugaban }asa ne ta hanyar sa’a kurum lokacin da maigidan sa, Shugaba Umaru Musa Yar’Adua, ya kwanta dama. A yarjejeniyar da aka yi, kamata ya yi shugaban }asa da zai maye gurbin Yar’Adua ya fito daga arewa domin kuwa shi Yar’Adua bai kammala wa’adin da ya kamata yankin ya yi ba. To amma shi Jonathan da magoya bayan sa, sun za~i su yi fatali da wannan yarjejeniyar. Su kuwa manyan ’yan takarar PDP daga arewa, sai su ka janye, su ka goyi bayan tsohon mataimakin shugaban }asa, Alhaji Atiku Abubakar (Turakin Adamawa), sakamakon yarjejeniyar fidda ]an takara }waya ]aya na arewa a jam’iyyar da aka yi, kuma akwai yiwuwar shi za su ci gaba da goyon baya a wannan za~en fidda gwanin da kuma bayan za~en.

A yayin da ake cikin haka, sai ~angarorin biyu su ka shiga ya}in watsa wa juna }asa a ido. A kullum sai ka ga wanin su ya na yi wa ]an’uwan sa ~atanci a jarida, da zargi iri-iri na cin hanci da rashawa da kuma ambaton wasu kalamai maras da]i da wani daga cikin su ya ta~a yi a baya. Manufa ita ce a nuna cewa wane bai dace da zama shugaba ba. [aya daga cikin wannan zargin na kwana kwanan nan shi ne inda aka ruwaito Atiku ya na ragargazar jam’iyyar ta PDP, aka ce wai ya yi kalamin ne a cikin watan Nuwamba na shekarar 2006.

Shin Atiku bai da hurumin yin irin wannan maganar a WANCAN lokacin, wanda kowa ya san cewa da gaske ne PDP jam’iyya ce inda ba a bin doka da oda? Kalamin da aka ce Atikun ya yi, wai ya yi shi ne a sashen Hausa na Muryar Amurka inda ya ce PDP “ba ta da }a’ida; ba ta bin doka da oda da kuma shugabannin ta.” Amma idan mun duba da kyau, za mu ga cewa duk abin nan da Atiku ya fa]a game da PDP a wancan lokacin, gaskiya ne. Akwai ma mutanen da su ka fa]i abin da ya fi haka. Shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka, ya bayyana jam’iyyar PDP da cewa she}ar ba}a}en macizai ce kawai.

An shafe shekaru PDP ta na cikin rigingimu, ba don kurum ’ya’yan ta sun ]auke ta a matsayin hanya mafi gajarta wajen ku]ancewa a dare ]aya ba, a’a har ma da yadda babu tsarin dimokira]iyya a cikin ta. A PDP, ana cusa wa masu za~e ]an takara, a ce shi ake so a za~a ko da kuwa jama’a ba su son shi, kuma lallai ne duk wanda aka tsayar sai ka ji shi ne ya lashe za~en. Sakamakon haka, a yayin da ake ta kiraye-kirayen cewa ya kamata a kimtsa jam’iyyar, sai ’ya’yan ta da yawa su ka dinga sauya she}a. Kuma jam’iyyar ta fa]i a sababbin za~u~~uka da aka yi a wasu jihohin. A yau ma da hukumar za~e ta ke ta yayata cewa za ta gudanar da za~e fisabilillahi, ai ga shi nan ’yan PDP da dama sun yi hijira zuwa wasu jam’iyyun, inda su ka tsaya takara. Alamun cewa an fara dawowa daga rakiyar jam’iyyar ta bayyana }arara a za~u~~ukan fidda gwani na takarar zuwa Majalisar Tarayya da aka gudanar a }arshen makon jiya, inda sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da dama su ka sha kaye a hannun abokan adawar su. To, kallo ma bai }are ba har sai an zo za~e tsakanin jam’iyya da jam’iyya; a nan ne idon wasu ’yan takara - ciki kuwa har da gwamnoni - zai raina fata. Sai ga shi a yau PDP ta shiga gargada, duk da cika-bakin da shugaban ta na }asa na lokacin, wato Prince Vincent Ogbulafor, ya ta~a na cewa sai sun yi mulki har na tsawon shekara 60 ba tsinkewa; yanzu akwai alamun za ta fa]i ba nauyi.

Wannan za~en fidda gwanin da ’yan PDP ke yi a Abuja zai iya haifar da alheri ko sharri ga jam’iyyar, har abin ya shafi }asa baki ]aya. Akwai ]ar ]ar ]in da ake yi na abin da zai iya wakana idan har Jonathan ya fa]i a za~en ko idan Atiku ne ya fa]i. Tambayar da ake yi ita ce, shin idan shugaban }asar ya sha }asa, zai koma koyarwar sa a makaranta ne ko kuwa zai samu wata mafaka ne inda zai ri}a cin duniyar sa da tsinke? Ma’ana, zai yarda ya sauka daga karagar mulki kuwa kamar yadda ya ta~a al}awartawa? Ko kuwa zai yi irin na Shugaba Laurent Gbagbo na }asar Cote d’Ivoire ne, ya ce atafau ba zai sauka ba? Sa’annan ko kuwa shi Atiku, angulu za ta koma gidan ta na tsamiya ne ko kuma zai sake dabarar da ake ra]e-ra]in zai bi, idan har aka tandara shi da }asa? Ku sani cewa ita wannan sabuwar dabarar, ba fa wadda ’yan ~angaren Jonathan ke ya]awa ba ce, cewa wai Atiku ya ce zai janyo fitina idan ba a za~e shi ba. Dabarar dai ita ce wata}ila shi da magoya bayan sa su fice daga PDP su koma wata jam’iyyar su mara wa ]an takarar ta baya, misali jam’iyyar CPC ta su Janar Muhammadu Buhari, ba don komai ba sai don a tabbatar da cewa an ta]iye Jonathan.

Shahararren marubucin nan ]an }asar Ingila wanda ya rasu ]aruruwan shekaru da su ka gabata, wato William Shakespeare, ya rubuta a littafin sa na wasan kwaikwayo mai suna Julius Caesar cewa a tabbatar an yi kaffa-kaffa da ranar 13 ga Maris ko ranar 13 ga Janairu, domin kuwa wani mugun abu na iya faruwa a ranar ko a sakamakon ta. Sai ga shi ’yan PDP sun taru domin yin za~e a ran 13 ga Janairu. To, mu dai addu’ar mu ita ce ko ma wace irin waina aka toya a jiya Alhamis, Allah Ya sa ta alheri ce ga Nijeriya. Manyan kurayen da ke mulki a kan dokin PDP sun da]e su na yi wa ’yan Nijeriya hawan }awara, bayan kuwa a baki su na i}irarin wai sun zo ne su ceci talaka daga fatara da yunwa. Sai ga shi fatara da yunwar ba su ragu ba. Ci-gaban mai ginar rijiya kawai ake yi. Nijeriya ta ci gaba da kasancewa }asa mai koma-baya ta fuskar tattalin arziki, sannan ta na daga cikin jerin }asashe wa]anda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu. Ya Allah, mu na ro}on Ka sa kada mu fa]a cikin ramukan da mu ke hangowa a gaban mu. Amin summa amin.

----
An buga a LEADERSHIP WEEKEND ta makon jiya

No comments: