Thursday, 24 February 2011

Ma’anar }arfin ikon jama’a

DA }arfe 6:43 na yamma a birnin Al}ahira a ranar Juma’a ta makon jiya, wani jagoran masu zanga-zangar }in amincewa da mulkin Shugaba Hosni Mubarak mai suna Wael Ghonim ya tura sa}o a dandalin Twitter da ke intanet, ya na fa]in: “Mu na taya ki murna, Masar, babban mai laifin nan ya arce daga fadar sa.” Ya na nufin Mubarak wani babban ~arawo ne ko mai kisan kai da sauran manyan laifuffuka wanda mulkin sa ya zo }arshe har ya gudu daga fadar shugaban }asa. Hakan ya biyo bayan tumbu]in da al’ummar }asar su ka shafe kwana 18 su na yi, inda a }arshe, ran Juma’a da ta wuce, zamanin Muhammad Hosni Mubarak a karagar Jamhuriyar Larabawa ta Masar ya kawo }arshe. {arfin jama’a ya tabbata. Idan kun tuna, a rubutun da na yi a wannan shafin a makon jiya mai taken, “Fir'auna Na {arshe Ya Fa]i!” na bayyana cewa, “Tuni muguwar gwamnatin sa ta shiga garari, ta fara tarwatsewa, domin kuwa iyalan sa da manyan jami’an gwamnatin sa tuni su ka fara arar takalmin kare su na arcewa.”

Tarin jama’ar da ta taru a Dandalin Tahrir ta wuce maridan gwamnati su maida ita abar wasa ko su yi mata ri}on sakainar kashi, domin jama’a ce wadda ta san ciwon kan ta kuma ta ke da zummar lallai sai an biya mata bu}atar ta. Yawancin mutanen da ke cikin taron matasa ne wa]anda ba su gama ko ta-ta-ta ba lokacin da Mubarak ya ]are karagar mulki a 1981. To amma mutane ne masu ilimi, wayayyu a lamurran duniyar mu ta yau, masana intanet, masu fushi da gur~acewar mulki, wa]anda su ka gaji da salon tafiyar hawainiyar mulki, kuma sun gaji da salon mulkin mutum ]aya, sannan su na son canji ko ta halin }a}a. Matasa ne ’yan Facebook wa]anda su ka san yadda za su yi amfani da intanet da kuma tashoshin talabijin na satalayit don cimma bu}atun su. Duk wani mai ba}in mulki da ya yi kunnen uwar shegu da irin wa]annan ’yan taratsin, to jiki magayi.

Mubarak ya yi duk wasu kame-kame don ya li}e a jikin she}ar sa. Saboda lallai ya san tsiyar wa]annan nau’urorin ya]a labarai da Turawa su ka }ir}ira, ya dakatar da Facebook da gidan talabijin na Aljazeera na wani ]an lokaci, amma duk a banza. Babu abin da ya yi masa amfani; misali barazanar da kwamandojin sa na soja su ka yi wa masu zanga-zangar, da soki-burutsun da Mataimakin Shugaban {asa Omar Suleiman (mutumin da shugaban ’yan zanga-zanga Mohammed El-Baradei ya kira da “abokin tagwaicin” Mubarak) ya yi masu, da hare-haren da magoya bayan Mubarak su ka kai wa ’yan zanga-zangar ko kuma jawaban yaudara da shi Mubarak ]in ya yi wa jama’ar }asar a ran 1 da ran 10 ga Fabrairu, inda ya sha alwashin wai zai ci gaba da mulki har na tsawon watanni bakwai masu zuwa. Da alama, bai gane zurfin tsanar da mutane su ka yi wa azzalumar gwamnatin sa ba. Tunda dai duk }asar ta na kuka da shi, sannan dubban mutane sun shiga yajin aiki, inda su ka ja wa }asar birki, don haka bai fi awoyi ka]an - ba ma kwanaki ba - kafin }arshen sa ya zo.

Aje aikin da ya yi ran Juma’a wata shaida ce da ke }ara gabbata da }arfin ikon jama’a. Irin haka ta ta~a faruwa a }asar Filifins a 1986, wanda ya sa aka dinga yin juyin juya hali a }asashe da dama a Gabashin Turai a 1989, ana rusa gwamnatocin gurguzu. Amma an jima irin hakan ba ta faru a nahiyar Larabawa ko ta Afrika ba ma, inda masu mulki ke kallon kan su a matsayin wani abin bauta. To amma yanzu ta fara sauya zani. A yau, Larabawa su na yin tambaya kan halin da rayuwar su ta ke ciki, kuma su na yun}urin kifar da azzaluman shugabannin su. A watan jiya, hakan ta faru a }asar Tunisiya inda jama’a su ka yi zanga-zanga su ka ham~arar da shugaban }asar, har sai da ya tsere zuwa gudun hijira. To amma fa ba wanda ya ta~a tunanin cewa irin wannan za ta iya faruwa a Masar, }asar da ke kan gaba wajen yin ala}a da Yammacin Turai a }asashen Labarawa duka, musamman ma da yake Mubarak ne shugaban }asar, mutumin da ake ganin ya na da }arfin mulki tamkar Fir’auna, wanda sai dai a kwatanta shi da shugaban Ira}i na da, wato marigayi Saddam Hussein. To, duk da haka sai da ta faru ta }are, wai an yi wa mai zani ]aya sata! Jama’a sun fa]i abin da su ke so, kuma sun samu.

To amma fa tsugune ba ta }are ba, an saida kare an sayi biri. An dai fidda Mubarak, amma kuma ginshi}in gwamnatin sa - wato sojojin da su ka ]aure masa gindi - har yanzu su na nan daram damdam, sun maida }asar maras dimokira]iyya. Har yanzu za a iya ci gaba da cin mutuncin jama’a. Za a iya mur}ushe duk wani ]an adawa.

Na biyu, tsoron da gwamnatocin Yammaci su ke yi na cewa wai babbar jam’iyyar adawar }asar, wato Muslim Brotherhood, za ta hau kujerar mulkin }asar wata babbar barazana ce ga abin muradin jama’ar Masar. Turawa da Yahudawa su na so Masar ta ci gaba da kasancewa a tafin hannun su saboda kawai ta na dakushe abin da su ke kira da tsattsauran ra’ayin addini. A ranar da Mubarak ya fa]i, Firayim Ministar }asar Jamus, wato Angela Markel, ta yi garga]in cewa tilas ne Masar ta ci gaba da yin abokantaka da Isra’ila. Sannan wani fitaccen ]an jaridar Amurka wai shi Glenn Beck, wanda tsattsauran ra’ayin sa bai da bambanci da na ’yan Al}a’ida wajen tada hankalin jama’a, ya bayyana cewa yun}urin fidda Mubarak wani babban gangamin ha~aka addinin Islama ne na duniya wanda ya taso tun daga nahiyar Asiya har zuwa Ingila. Beck, wanda ke da ]imbin mabiya shirin sa na talabijin a Amurka, ya ce, “Wannan ba zancen Masar ba ne. Wannan magana ce ta dukkan wani mutum da ya ta~a yin shiri, ko ya ke so, ya canza ainihin rayuwar Turawa da Yahudawa baki ]ayan ta.” Manyan masu fa]a a ji a Amurka da dama su na da wannan ra’ayi, ciki kuwa har da babban ]an jam’iyyar Republican ]in nan mai suna Newt Gingrich, wanda ya furta cewa, “’Yan Muslim Brotherhood su ne manyan ma}iyan rayuwar mu da jinsin mu.”

Shin wai ba abin mamaki ba ne kuwa a ce ’yan ra’ayin ri}au na Yammacin Turai ba su son ganin mulkin dimokira]iyya ya wanzu a yankin Gabas ta Tsakiya don kawai irin shugabanin da talakawan Larabawa ke so ba su ba ne Turawa da Yahudawa ke so, sun ]auke su masu tsattsauran ra’ayi? ’Yan ri}au ]in Yammaci sun fi son shugabannin Larabawa masu }aryar son jama’ar su sun ci gaba da mulki, a yayin da su ke kau da kai daga matsalolin rayuwa da su ka addabi jama’ar su saboda kawai shugabannin duk ’yan koren su ne.

Sa’annan sai maganar tattalin arziki, wanda Mubarak ya kasa gyarawa domin ya fi maida hankali ga harkar tsaro. Shi kullum abin da ya fi damun sa shi ne dangantakar }asashe, wadda ta ha]a da shiri da Isra’ila da kuma ya}ar ’yan kishin Islama. Saboda haka, duk wanda ya zama sabon shugaban }asar Masar ya na da babban aikin gyaran koma]ar tattalin arziki a }asar sa. Bayan haka, wani abu mai muhimmanci kuma shi ne batun yadda za a gina ingantaccen tsarin mulkin dimokira]iyya bisa ginshi}in addinin jama’ar }asa. Hujjoji da dama sun nuna cewa tsarin mulkin dimokira]iyya ya na iya ginuwa a }asashen Musulmi. Shugaban Amurka, Barack Obama, ya fara amincewa da bin hanyar da gwamnatocin Amurka da dama su ka }i aminta da ita, wato bu}atar gina tsarin mulkin dimokira]iyya a }asashen Larabawa.

Idan an bi wannan hanyar bil ha}}i da gaskiya, to za a ga ci-gaba sosai. Domin fa rashin samun za~i, da kuma cusa wa jama’a shugabannin da ba su so ta hangar ci da addini ko batun tsaro ya na taimakawa wajen sa wasu su ]auki tsattsauran mataki, wanda ya ha]a da tada bam a cikin jirgin sama ko kuma fasa motar safa da gurnati. Don a cimma nasara, tilas ne Turawa da Yahudawa su }yale Larabawa su za~a wa kan su shugabannin kan su ta hanyar za~e na fisabilillahi. Juyin juya hali da aka yi a Masar ya nuna cewa zamanin da Turawa su ke cusa wa Larabawa shugabanni don biyan bu}atar su ta son rai ya shu]e. A yau, matasa za su ri}a bin bahasi da babbar murya.

Mu ma a nan Afrika ya kamata mu farka daga barci. Don me? Dalili shi ne mu na da masu mulkin mur]iya amma masu kiran kan su da sunan masoya dimokira]iyya. Wasu ma su na ta }ara ~ullowa a fagen. Ya kamata matasan Afrika, Ba}ar Fata, su yi koyi da takwarorin su da ke arewacin nahiyar mu; kada a manta, su ma ’yan Tunisiya da ’yan Masar duk ’yan Afrika ne. Yackamata su farka daga gyangya]i, su yi bin bahasi ga shugabannin su, su bu}aci sauyi a duk inda hakan ya dace.

Ku kuma ’yan Masar mu na taya ku murna. Fir’auna ya fa]i.

---

An buga a LEADERSHIP HAUSA ta ranar Juma'a da ta gabata

No comments: